← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 128

Sashe 10

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta wuce dakinta itama.

~~~
Saratu Kam a darare ta wuce part din Sageer tasan a Wannan lkcn Yana makaranta dukda zuwa yanzu Bayan la'asar ne cikin sanda ta Shiga dakin tana waige a hankali ta tura kofar ta Shiga, sauke ajiyar zuciya tayi data ga Babu kowa a falon, tsayawa tayi tana karewa tsaruwar falon kallo ranta fari tas tanajin wani Nishadi a ranta duk fadin gidan Nan Babu inda takejin dadin zuwansa da kasancewa cikin farinciki sama da part din danta Sageer, shiyasa ko bazai Gaya Mata me Dadi ba zatazo taga yadda danta ke rayuwa cikin daula dajin Dadi, har hango kanta take sun mallaki dukiyar Alhaji Abdullahi yyinda ta zamo itace tamkar Hajia Aisha me mulkar gidan da nuna Isa akan komai, takanji takaici idan taga tana musu aiki saidai ta kudurta a ranta na lkci ne sbd d zarar ta shafeta a Bayan kasa ita da dukkan Ahalin gaba1 toh daga ranar ta zama me cikakken iko wani kayataccen murmushi ne ya kwace Mata data hangi hoton Sageer an mannashi jikin bango cikin Shiga ta Alfarma, a fili tace,

"yanzu da Wannan shegen miskilin yaron ne a Wannan daular Koh?"

Tana nufin Dr. Omar,

"Yadda yake da tsinannen isar Nan ace shine a wajen Nan ai da anga yadda ake mulki, Mtws"

tadan ja tsaki,

"haka naso yarona Sageer kayi Amma ka tsaya shiririta Babu me yabon ka sai Fadar aibinka musamman waccar tsohuwar"

wato Hajjaju, tunowa da Abinda ta aikata ga mlm sale yasa tayi saurin ajiye kayan abincin cikin sauri ta fito har tana hada hanya kafin wani lkci harta Isa dakin da take zama jawo Jakarta tayi ta duba mgnin da boka ya Basu Yana Nan a ajiye kamar yadda yake, zuge jakar tayi ta rayata Tabbas Dole ta binne layar Nan da wuri kafin a samu matsala, a gurguje taje tayiwa Hajia Aisha sallama sannan tabar gidan gaba1.

°°°°°°
Koda Saratu taje unguwar su lkcn yamma ce akwai masu zaman kofar gida, tana isowa zata Shiga gida mlm Shamsu ya taso Yana fadin,

"Saratu ya Abinda ya faru Kuma?"

Yyi mgnr cikin sigar jimami, Saratu ji tayi kirjinta ya buga sosai kodai mutuwar mlm sale yyi dgske? Amma sbd kada ta bada kofar a zargeta tayi fuska hade da zaro ido irin batasan meya faru ba dinnan tace,

"me kke cewa mlm Shamsu? Wani Abu ya faru ne?"

Tayi mgnr a jere, mlm Shamsu ya dafa Kai,

"Allahu Akbar Ashe bakya Nan koh, mlm sale ya zame jikin karfen gado jini ya dinga malala kamar an balle kogi abin ba dadin ji Dan suna asibiti tun safe har yanzu shiru"

sauke ajiyar zuciya Saratu tayi a boye Amma a fili kuwa cewa tayi,

"yau na Shiga uku ni Saratu"

ta fada tana Dora hannu akai, mlm Shamsu yace,

"sai hakuri tsautsayi ne"

da sauri Saratu tace,

"Bari na aje kayana na tafi asibitin"

Nan tabar shi tsaye ta wuce gida da sauri, tana Shiga gidan kuwa taja tsaki,

"aikin banza yoh ni daya mutu ma da zanfi kowa murna da hakan Dan har yanzu be tsira daga gareni ba saina toshe bakinsa tunda niyyar sa tana Nan Dole yana samun Dama Saiya tonamin Asiri nikuwa Abinda bazan lamunta ba kenan Sam"

a gurguje ta samo fatanya da mlm sale ya sakale jikin rumfar su, dake gidan dama be wani wadatu da siminti ba sbd farfashewa da yyi Saiya bawa Saratu damar cika burinta, cikin karfi ta dinga Sara kofar dakin nasa a gurguje tayi Rami Medan zurfi kafin ta fiddo layar jakar ta ta binne a ciki, tana maida fatanyar kenan aka shigo gidan a tsorace ta waiga ganin sahabatu ce yasa ta saki ranta, Saratu tace,

"yau kin dawo da wuri kice kasuwa tayi kyau"

Sahabatu na ajiye kula tace,

"ai umma na Gaya Miki Nima na waye zuwa yanzu na daina kwashen abinci"

Saratu ta washe baki batare da tayiwa kalmar fashin baki ba tace,

"shiyasa nakeji dake 'yata maza Shiga kiyi wanka ki huta ga abinci can na taho Miki dashi"

Sahabatu tace,

"yauwa umma me abincin 'yan gayu"

Saratu tace,

"ai nasha fada Miki wata Rana saidai ki bayar indai irin abincin Nan ne"

Sahabatu tace,

"toh umma kullum mgnr kenan yaushe wataran dinnan zatazo ne?"

Ummah tace,

"baki yadda Dani bane?"

Sahabatu tayi 'yar dariya tace,

"Toh ya na iya? na yadda zance"

tayi mgnr tana wucewa bandaki. Kwafa Saratu tayi ta bita da Harara, Wayarta data kunna taji tana Kara da sauri ta dauko ta cikin jaka, dagawa tayi tana fadin,

"Alo"

Shiru akayi ba'ace komai ba, can ta sake fadin,

"waye ke mgn?"

Daga dayan bangaren Omar ne daya zubawa Abba dake kwance ido cikin tausayawa bawai baida abin fada bane kawai Yana tunanin wacce amsar za'a bashi ne, can dai ya daure yace,

"Ummah..!"

Daidai lkcn Saratu na Shirin yanke layin kenan taji muryar sa ta daki dodon kunnen ta, wani kululin takaici ne ya mamaye ta itafa ba komai yake karawa saratun takaici ba sai yadda taga Omar din Yana Abu kamar na asalin mahaifin sa Alhaji Abdullahi muryar su iri daya, tafiyar su iri daya, cikar zarra da mazan taka iri daya banbancin su shine wancan ya manyanta shikuma Wannan matashi, yanzun ma ji tayi kamar Alhajin ke mgn, a harzuqe tace,

"sbd Debewar Albarka da Rashin ganin girman na gaba dama Kaine Dan wulakanci inata mgn kamin shiru?"

Tayi mgnr zuciyar ta na zafi har cikin ranta take jifansa da mugayen kalamai tana fata su tabbata a kansa danya daidaice ya lalace a ganin ta ko ba ita ta haifesa ba ai ta shayar dashi ko saboda Wannan bakinta zai Kama shi.

Rintse idonsa yyi cikin zafin Rai da radadin zuciya dukda bayau farau ba Amma ya rasa meyasa kullum yakejin dacin maganganun da mahaifiyar sa ke jifan sa dashi, Shidai ba yabon Kai ba Amma yasan Tabbas za'a iya jerashi cikin 'ya'yan da suke yiwa iyayen su biyayya bil hakki da gsky, toh shi besan mezai yiwa mahaifiyar sa ta so shi ba Koda na yini daya ne, Katse tunanin nasa yyi da sauri yace,

"Allah ya huci zuciyar ki Ummah, dama Zan Gaya Miki idan kin dawo gida ne Abba baida lpy tun safe Yana asibiti idan Babu takura nake rokon ko Zaki samu damar leko shi?"

Har zata jefeshi da wata kalmar ta tuna mgnin da boka ya Bata Tabbas Wannan ce damar ta da zatayi amfani da ita wajen sihirin da akayiwa mlm, a take tace,

"meya same shi? Kuma a Ina kuke?"

Tayi mgnr cikin kulawa, zaro wayarsa yyi ya duba Anya da ummah yake waya? Dan be zaci kalaman da zasu biyo baya ba kenan, da sauri ya mayar jikin kunnen sa yace,

"zamewa yyi ya bugi da karfen gado Amma yanzun Alhamdulillah muna asibitin Aminu kano"

ya fada da sauri, Dan tsaki kasa2 Saratu tayi can tace,

"toh gani Nan zuwa"

"Dr. Omar Yace,

"A iso lafiya"

yyi mgnr Yana katse layin da sauri kar yyi wani kuskuren ta fasa zuwa. A Rayuwar sa idan ka cire son Allah da Manzon Allah S.A.W toh Babu Wanda yakeso sama da iyayensa Yana matukar ji dasu dukda yadda suke ganin su yake tamkar sarakuna a idonsa shi mutum ne dayasan mutuncin Ahali, dagasu sai Abokin sa Sadeeq abotar su ta daban ce, a bangaren 'yan Mata kuwa be taba son wata 'ya mace ba har yau be ci karo da wacce ta dace da Rayuwar sa ba dukda Shidin Allah ya iyosa cikin Jerin mazajen da suke da karfin sha'awa Amma Yana dannewa kwarai dgske Yana Shan magani da yawaita azumin Nafila Dan samun sassauci, Kuma Alhamdulillah Yana ganin waraka tunda ba kasafai abin yake kaishi makura ba.

******
Koda Ameera ta nausa cikin school din sannu a hankali ta fara karanta department kala2 harta Kai ga department dinsu, Welcome to Biological Sciences Department taga an rubuta, sauke ajiyar zuciya tayi tana Kara kusanta jikin department din, Duba files dinta tayi Nan ta zaro nata ta nufi H.O.D office, ga mutane Nan dayawa a layi kowa jira yake ya Shiga, haka Ameera itama ta Shiga layin Dan jira, Bayan wasu mintuna ta samu damar Shiga office din Nan aka Bata wasu form ta cike sannan ya Bata wani form din daban wato course form Wanda zata cikeshi kowanne mlmi ya Mata signing, Barinta office yasa ta nufi department din gefen ta Dan Anan taga na 'yan education har office din H.O.D taje ta zube Masa files din su Anty shafa mutumin ya dago yace,

"which one is yours?"

Ameera ta nuna masa na hannun ta, da mmki yace,

"toh Wannan biyun nasu waye?"

Ameera tace,

"na Yayuna ne"

Rai a bace yace,

"Su yayun naki kutare ne da Zaki zo musu registration? ke kinada hankali ma kuwa? Kinsan me ake Kira da university? Bafa secondary bane fah?"

A tsorace tace,

"I'm sorry sir Zan Gaya musu"

"mtwss..."

Yaja tsaki hade da wurgi da files dinsu yace,

"idan Basu shirya yin karatun ba kada su Kara aiko ki Dan za'a soke sunan su cikin Wanda suka samu Admission"

ya fada cikin tsawa, jiki na rawa Ameera ta tattare files din tana bashi hakuri kafin cikin azama tabar office din da sauri.
Prof Adam kenan, H.O.D na department din E.DU Biology, mutumin ya tsani malalacin yaro, shiyasa daya fahimci turowa yaran sukai amusu yyi Mata barazana Dan idan karatun sukazo suyi da kansu bada gumin wani ba.

Ameera na fita ta sauke ajiyar zuciya hamdala take a ranta a fili tace,

"tab Allah ya taimakeni da yanzu Nima Ina ciki"
Chapter 10 · 0% Book details