Sashe 44
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
nake parking zakaga wata sabuwar mota a wajen taka ce, a cikin motar daga kujerar gefen driver akwai takarda a ciki address din gida ne na baka halak malak" a firgice Dr. Omar yake dubansa ya bude baki zaiyi mgn kenan, Alhaji Abdullahi ya katse shi da fadin, "No ban sanka da saurin mantuwa ba ka dauki hakan kamar mahaifin ka ne yyi maka kyauta ba wani ba, so banson korafi ko godiya, yanzu ma kana iya zuwa kaje ka duba motar da gidan Dan Nima akwai inda zanje" ya karasa mgnr Yana mikewa tsaye yyi hakan ne duk Dan kada Dr. Omar din yace zaiyi musu ko yyi Masa godiya. Shi Dr. Omar gaba1 ya Rasa wanne irin tunani ma zaiyi, Abubuwan Al'ajabi da yake faruwa dashi tunda ya shigo company dinnan ya fara bashi tsoro gashi ba damar yyi mgn sbd katse Masa hanzarin da Alhaji Abdullahi yyi Masa tun farko, haka yaji a ransa bazai iya Masa musu ba, Toh Kuma maganganu suna Nan dankare a ransa yanaso ya Furta su Dan haka shima ya tashi da niyyar zuwa gun abokin sa Sadeeq Dan tayashi jimajin Abinda ke faruwa, anan sukayi wa juna sallama kowa yabar company din. ~~~~~~~ Kallon motar Dr. Sadeeq yake Yana shafata cikin tsananin farinciki, tun dazu ya kasa rufe bakinsa sbd murna, yyinda Dr. Omar yake binsa da kallon mmki, katse shi yyi da fadin, "Kai Dana fada maka Abinda ke damuna sai ka bige da murna?" Dr. Sadeeq na daidaita nutsuwar sa yace, "Kai Wlh na kasa boye murna ta ne, Kai Alhamdulillah Ala kulli halin Kai Wlh Allah babban sarki ne" Ya Furta hakan Yana duban Dr. Omar, Kafin yaci gaba da fadin, "Gsky ka godewa Allah Omar kada ka butulcewa ni'imar da Allah yake nufinka da ita, ka tuna Wannan Karin mgnr da ake cewa ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA KO Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi, Makiyan ka sunso su wulakanta ka a idon duniya, sunso suga bayanka, sunso suga ka tozarta, sai Allah ya nuna musu ikon sa, bakinda da Allah ya tsaga baya hanashi abinci, Idan Allah ya nufeka da samun Abu idan duk duniya zasu taru a kanka Dan kada ka samu Toh Wlh Basu Isa ba saika samu Dan hanyoyin Allah yawa garesu, haka zalika idan duk duniya zasu taru a kanka Dan ka samu Abu idan Allah beyi nufin ka samu ba duk buga-bugar ka bazaka samu ba, Allah yanaso ya nuna musu Basu Isa ba, wayon su ko dabarar su bazaisa ka tozarta ba domin ba haka Allah ya tsaro maka ba, Dan haka kayi hamdala Omar, ka sake yin hamdala Omar, kaci gaba dayin hamdala a Koda yaushe, Wlh you're special, baka da hakkin su, d sannu Allah zai saka maka." Jikin Dr. Omar ne yyi Sanyi da maganganun Abokin sa Sadeeq, tabbas duk Abinda ya Furta gskyne Dan haka yaji kwarin gwiwa sosai ya Kuma sa a ransa bazai taba butulcewa ni'imar da Allah yyi Masa ba, zai ci gaba da godiya ga Allah, Dan haka a fili ya dafa kafadar Dr. Sadeeq yace, "my frnd a Wannan lkcn abune me wuya a samu aboki irin ka duk wuya duk tsanani Ana tare Thanks you so very muchh..." Murmushi Dr. Sadeeq yyi yace, "Ai mun wuce abokai sai 'yan uwa" Dr. Omar na murmushi yace, "yeah." Nan suka hau motar Dan zuwa gidan da aka bawa Dr. Omar. ####### Fadar tsari dakyau na gidan da Alhaji Abdullahi ya mallakawa Omar ma Bata lkci ne, gidan ya hadu over daidai misali ga shuke2 na flowers gwanin ban sha'awa, tsaruwar parlon da dakunan sunyi matuka komai dai Masha Allah Saida suka Gama zagaye gidan suka fitowa dukkansu na Yaba kyawu da tsaruwar gidan. ••••••••� Yau saura kwana biyu bikin Ameera da Dr. Omar Amma haka kkeji lami Babu armashi sbd dad ya Hana ayi Masa duk wata bidi'a ta biki, yace a ranar da aka daura auren za'a raka Ameera ba wani zancen yinin biki ko sauran su, a bangaren Ameera Koda taji Babu lefe abin be wani dameta ba Dan ita gani take ko da Kaya kala daya zata zauna da Omar matukar zata kubuta daga kangin Rayuwar da take ciki na gidansu, zata huta da bala'in Mom da yaranta, a kalla zata samu 'yancin kanta tasan dai a gidan mijinta duk abinda tayi na aiki ladane sabanin gidansu ba lada ba zunubi saima zagi da ake binta dashi.