← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 128

Sashe 4

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"karki bada Mata Mana, Abu me sauki ki Tabbatar cikin dare yadda Babu kowa saiki zaro bindin nasa ki zura a gaban ki daganan ya rage naki kisan yadda abin xai shiga"

"Toh shikenan boka zanyi yadda kace"

"Dakyau"

Ya furta Yana dariya, Nan sukayi Masa sallama Bayan sun bashi kudi Wanda Nas ce tayi guzurin su.

A hanya Saratu da Nas sukaci gaba da tattauna yadda lamarin zai kasance, suna shiga gari kuwa Nas tace,

"Yanzu Ina zakije?"

Saratu tace,

"can gidan Alhaji Mana yaushe zanje gida tun yanzu"

Nas tayi dariya tace,

"haba Ashe kin gane, Nima wucewa zanyi"

"toh shikenan"

Nan suka raba hanya Nas ta wuce gida yyinda Saratu ta wuce gidan *ALHAJI ABDULLAHI OMAR MAI FATA*

••••••••°°°°°••••••••�

*ASALIN LABARIN*

*ALHAJI ABDULLAHI OMAR MAI FATA*

Rikakken me kudi ne Wanda duniya ta shaida hakan, kamar yadda nace a baya Tabbas Alhaji Abdullahi ya shahara a Nigeria domin kowa yasan shi mutum ne daya rike mukamai dayawa yyi aiki da gsky daga karshe ya fita daga harkar mulki ya koma kasuwanci, dama Shidin asalin Dan kasuwa ne sbd safarar fata da sukeyi kasashen waje inda ake gyara fata ta koma abun ado wato takalma, jaka dadai sauran su, Duk wannan Dunbin DUKIYA daya samu Allah be bashi haihuwa ba shi da matar sa Hajia Aisha, duk wani mgni sunyi amfani dashi abin yaci tura, Dole suka zubawa sarautar Allah ido domin sunsan ba'a yiwa Allah Dole sai lkcin dayaso zai baka, hakan kuwa ta kasance sun dukufa sosai wajen yin Addu'a dakai kukansu game duka, cikin ikon Allah Saiga Hajia Aisha da juna biyu murna a gurin wa'annan bayin Allah ba'ace komai, tun daga lkcn suka fara tattarowa Dan dawowa Nigeria dama akan Shirin hakan suke Dan tuni Alhaji Abdullahi ya tamfatsa musu kerarren gida anan unguwar Tarauni, kowa yaga gidan Tabbas Saiya kyasa Kai kace ba'a kasar Nan yake ba wajen kyau da tsaruwa, a haka suka hawo jirgi Dan zuwa kasarsu ta haihuwa,

saukar su keda wuya driver dinsu da aka sanar masa Yana jiransu a harabar wajen Dan haka suna zuwa suka wuce cikin mota Nan kuwa suka taho gida, Suna daga Bayan mota sai ji sukai driver yyi wani wawan birki kamar su hantsila cikin muguwar tsawa Alhaji Abdullahi ya dakawa driver yace,

"Kai Salmanu are you out of your sense?"

Jiki na rawa Salmanu yace,

"Ka gafarceni Alhaji Wlh wata Mata mukaso kadewa"

"Mtwsss"

Alhji Yaja tsaki cikin takaici yace,

"shiyasa nace kana duba hanya sbd irin haka...."

Be rufe bakinsa ba yaji Ana kwankwasa musu window, Zugewa Hajia Aisha tayi da tun dazu batayi mgn ba, matar da akaso kadewa ne ta fara mgn,

"Dan Allah bayin Allah ku taimaka min da Abinda zanci Wlh yunwa nakeji kamar Zan mutu."

Kallon ta sukayi cikin tausayi Hajia Aisha ta zaro kudi ta Bata tace,

"gashi"

da murna matar ta karba tace,

"Nagode, Nagode Hajia Allah yasa kufi haka Nagode"

Nan dai suka tafi tanata zabga godiya. Suna wucewa itama matar ta koma gefen hanya cikin murna tana jiran mijinta ya dawo, daga bayanta taji ance,

"gashi *SARATU* dakyar na samu kunun Ashirin ki karba Kidan kurba kinji"

Juyowa tayi da murnar ta tace,

*"MALAM SALE* Yaudai Allah ya hadani da mutanen arziki Ashe dama akwai na Allah?"

Mlm sale yace,

"meya faru?"

Nan ta Gaya masa Abinda ya faru tana nuna masa kudin da aka Basu, girgiza Kai mlm sale yyi yace,

"Tabbas akwai na Allah samun su ne yanada wuya Allah ya biyasu"

Ya karasa mgnr cikin jin tausayin kansu, Tabbas idan zai iya tunawa yau kusan kwana uku kenan suna yawon bara titi-titi gida2 Basu samu abincin da zasuci ba bare Inda zasu tsugunna sunje gidan sarki yafi a kirga Babu bayani, sun tsaya a sansanin 'yan gudun hijira Abin gwanin takaici sbd yadda sukaga Ana layi da ture2 wajen karbar sadakar rabon gishiri kamar Wani garin kwaki abin a zubda kwalla ne, ga matarsa na dauke da karamin ciki Dole ne su fito a samu Abinda za'a sawa bakin salati.

Tun daga Wannan ranar Suka samu rufin Asiri sbd kudin da Hajia Aisha ta bawa Saratu yanada tsoka Dan haka suka lallaba suka Kama haya daki daya sauran mlm sale ya fara jari dashi yanabin kasuwar kwari da wambai Yana Saro Kaya ya dinga yawo dashi akai Yana siyarwa, ita kuma Saratu Bata zauna ba taci gaba da neman Aikatau Sam ta kasa samu abin ya dameta gari ya kano ace ta rasa Aikatau,

Sai wata Rana a garin yawon nata Allah ya kaita wani katon gida me masifar kyau da sheki ga security tako Ina Ana safa da marwa, gidan ya birgeta matuka, Nan ta dinga zagayen gidan tana kallo har taji cewa inama zata samu shiga? Tana daga Dan nesa da gate din gidan kenan taga wata mota zata shiga gidan har an zarta ta sai kuma taga motar ta dawo baya, Daidai saitin ta aka tsaya sannan aka zuge glass din window wa zata gani....?

Hajia Aisha ce dake Bayan mota ta leko tana Kare Mata kallo, sosai suka gane juna da sauri Saratu ta matso tana Dan dukawa tace,

"Allahu Akbar Hajia kece? Allah sarki Ashe zamu sake gamuwa, Ina wuni? Ya gida ya iyali"

Hajia Aisha ta danyi murmushin ta na manyan Mata tace,

"Baiwar Allah lpy ko yaushe kike a titi?"

Dan sosa Kai Saratu tayi tace,

"Wlh Hajia neman Aikatau nake ranar Kuma da kika ganni Wlh..."

Daga Mata hannu Hajia Aisha tayi tace,

"Wuce mu shiga daga ciki I'm very tired yanzu sai muyi mgn a nutse"

"Toh, toh, toh Babu damuwa"

Saratu ta furta tana me ja baya hade da karewa falleliyar motar da hajian take ciki kallo ita kam ta samu shiga Wannan motar ai sai tayi sati a ciki Bata gaji ba, bin bayansu tayi Dan sukam tuni driver Yaja harma ya fara Sanya hancin motar cikin gidan, a nan bakin gate Hajia Aisha tayiwa security mgn subar matar dake bayansu ta shigo, Nan suka Amsa Mata cikin girmamawa, da saurinta kuwa taje gaban gate din ganin basuce Mata komai ba yasa ta saki ajiyar zuciya kafin ta nausa cikin gidan.

A falon baki Hajia Aisha tasa aka aje Saratu tare dakai Mata abin motsa baki,

Saratu na ganin haka ta zauna dirshan tana cin kayan itatuwa abinka Dame ciki duk sai ta fara hannu baka hannu kwarya gashi an kwana biyu ba'aci me nauyi ba.

Saida Hajia Aisha ta huta sannan tazo ta samu Saratu a falon baki, Saratu duk tayi daidai a tsakiyar falon tana Shan iska hade da zubawa TV kallo, Ganin Hajia Aisha yasa ta hade kafa tana sunkuyar da Kai, zama Hajia Aisha tayi tace,

"Kozan iya sanin sunan ki?"

Saratu ta gyara zamanta sosai tace,

"Sunana Saratu matar Sale"

Dan zaro ido Hajia Aisha tayi tace,

"kenan bakwa tare da mijin naki?"

Saratu ta girgiza Kai tace,

"Muna tare.."

"Amma ya barki kike yawo titi2 shi meye amfanin sa da bazai nema muku abinci ba?"

Hajia Aisha ta katse Mata mgnr. Saratu ta danyi kasa da kanta cikin muryar kuka tace,

"Wlh Hajia mu ba 'yan garin Nan bane, asalin mu daga kauyen borno muke a dalilin rikicin Nan yasa mukazo Nan garin, gaba1 Dangin mu sun watse wasu sun mutu wasu bamu San inda suke ba, muma lkcn da aka tada rikici a garin bama Nan ne Dan munje babban asibitin cikin garin Borno sbd jinya da nake ta fama da ita sai da mukaje aka Tabbatar Mana da Ashe ciki ne, toh Ashe tafiyar mu keda wuya 'yan boko Haram suka bulla cikin garin na takaice Miki lbri bamu tsira da komai ba sai kayan jikin mu domin lkcn da mukaje kamar anyiwa garin shara yyinda gefe guda garin ya koma kamar matattarar Makabarta, tun daga lkcn ni da mijina bamu sake awa daya ba a garin muka dawo Borno dadan kudin daya rage Mana muka taho kano sbd tunanin mu kano babbar jaha ce da ko bakaje ba zakaji Ana lbrn ta,

musamman yadda akace 'yan kasuwa ne sai muka ga hakan zaizo Mana da sauki tunda kowa zai iya kasa kasuwar sa ya watse idan munzo sai muyi kasuwanci har mu samu rufin Asiri, toh Wlh Hajia ranar da muka fara haduwa dake kwanan mu uku kenan muna garari a titi sai da taimakon Allah da kukazo wucewa kika bamu kudin Nan ni da mijina muka sarrafa shi wajen siyan abinci dayin jari, Dan Baku Dade da wucewa ba shima ya dawo sbd ya tafi ne ya nema min Abinda zanci sbd karamin cikina, ta karashe mgnr cikin Jan majina.

"Hmmmm....!"

Hajia Aisha taja gwauron numfashi ta ajiye Tausayin matar ya shiga ranta kwarai Nan ta zurfafa cikin tunani kafin ta dago kanta a hankali tace....
*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Na
*Nuceeyluv😘*

*Wannan page din naki ne Mrs Tajudden Tajra, Ina matukar Jin dadin yadda kikemin comments, hakika sai an nutsu an fahimci Asalin lbrn kafin a gane Ina littafin ya dosa, sai gashi kafin nayi nisa kin fara zaro bakin zaren💃🏻 Inayinki❤️❤️ Aci gaba da gashi🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀�*

4.....

"Zan amince ki zamo 'yar aikina saidai bansan wanne kala Zaki iya ba sbd mu Already munada ma'aikata a gidan Nan Zan taimakeki ne kawai badan mun rasa ba"

Cikin zumudi Saratu tace,

"Wlh kowanne iri ne Hajia Zan iya, daga kan share2 wanke2 da goge2 duk Zan iya Wlh, irin abincin ku ne dai bazan iya ba idan ba irin namu na gargajiya ba"

kallon ta Hajia Aisha tayi tace,

"naji kamar kince kina dauke da karamin ciki?"

Saratu ta girgiza kanta tace,

"sosai kuwa"

Hajia Aisha tace,

"Toh Taya Zan baki aiki Bayan kina da juna biyu? Ki Bari idan kika haife Abinda ke cikin ki saiki dawo muyi mgn"

da sauri Saratu tace,

"Dan Allah Hajia kimin Rai ni Wlh a hakan ma Zan iya inada dauriya sosai ko Dan goge2 Nan ki bani zanyi idan yaso na haife Abinda ke cikina saiki bani aiki me kwari"

Ta karasa mgnr cikin hade hannayen ta Alamar magiya, Shiru Hajia Aisha tayi tana Dan nazari can tace,
Chapter 4 · 0% Book details