← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 128

Sashe 26

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin dare Meera ta kasa bcci, Tabbas ta yadda da maganganun Sageer zai aikata Abinda yafi haka ma sbd taga alama baida digon Imani a ransa, A kashe Dr. Omar Abinda bazata lamunta ba kenan, Ta Dora Masa lefi Nan ma batayi Masa Adalci ba, shin Wai Toh yanzu Ina Mafita? Haka tayita dukan kanta da hannu sbd yadda kanta ya kulle ta rasa inda zata tsoma kanta taji Dadi gaba1 ta Shiga rikici, duk shawarar data yanke sai taga Babu mafuta, karshe dai Alwala tayi Dan samun sauki ga halin da take ciki.

~~~~
A bangaren Dr. Omar kuwa a Wannan Rana Koda suka Gama da wajen 'yan sanda direct gidansu Dr. Sadeeq suka wuce, lkcn Hajia(mahaifiyar Dr. Sadeeq) tana parlo tare da autan ta Saleem, Saleem na ganin su ya tafi da gudu Yana dariya ya rungume Dr. Omar, dukda Dr. Omar baya cikin walwala hakan be hanashi daga Saleem ba kamar yadda ya Saba idan ya shigo gidan, da fara'a suka karasa gaban Hajia tare da diban gaisuwa, Hajia tace,

"Likita bokon turai Har kun tashi kenan"

Nan suka Amsa Mata da murmushi, Hajia ta dubi Dr. Omar tace,

"ya jikin mlm?"

Dr. Omar yace,

"Alhamdulillah da sauki"

"Hajia tace,

"yauwa kaga inata so nayi maka mgn Kan ciwon Nan nasa Allah be nufa ba sai yanzu zancen ya sake dawo min"

Dr. Omar ya maida hankalin sa sosai gunta yace,

"Toh Hajia Inajin ki"

Hajia tace,

"munyi mgn da Abbansu(babansu Dr. Sadeeq) Mukace ya kamata gsky a duba ciwon Nan kodai Sihiri akai Masa?"

Shiru Dr. Omar yyi Yana nazari hakan yasa Hajia taci gaba da fadin,

"toh Nima dai tunda Naga yanayin ciwon abin ya daure min Kai sbd tun da cen da bakinsa Amma ace Rana guda baya mgn? Dukda dai akwai jarabawa ta ubangiji saidai yace tashi na taimake ka ba'a hanamu neman mgni ba, Dan haka nacewa Abbansu a nemi wani babban malamin da yake harka da irin Wannan ciwon wato Wanda suke bada Addu'o'i da mgni na Sihiri a gwada ko za'a dace"

Dr. Omar cikin gamsuwa da bayanin Hajia yace,

"Insha Allahu Zan Nemo mlmin sai a gwada"

Hajia tace,

"ai ta kwana gidan sauki akwai malam Haruna Dake Nan kurna Yana bada Wannan taimakon Insha Allahu duk sihirin da akayiwa mutum idan ya baka Addu'a da mgni za'a dace da izinin Allah matukar dai ba mutum shi yyiwa kansa ba wato yaje yima wani abin ya juye kansa, Toh Abbansu ya Samo number mutumin har anyi mgn dashi yace a hadaku sai kaje ka same shi kuyi mgn"

Cikin jin Dadi kwarai Dr. Omar yace,

"Nagode sosai Hajia Allah Yaja kwana ya Kara Arziki Allah yasa a Gama da duniya lfy"

"Ameen summa Ameen"

Hajia ta furta kafin taci gaba da fadin,

"Kai da Sadeeq ai duk dayane a wajena fatana Allah ya bawa Abban naka sauki"

"Ameen"

duka suka Amsa har Sadeeq din. Anan ta bashi number ya karba yyi Saving. Fitowar su daga bangaren Hajia kenan Sadeeq yace,

"inaga sai muje gun mutumin Nan da sassafe Koh?"

Dr. Omar yace,

"sai ya bamu lkci ai"

Sadeeq yace,

"Toh kirashi muji"

Nan ya latsa number malam Haruna, Bayan sun gaisa malam Haruna yace,

"yaje gunsa da yamma"

anan sukayi sallama da juna, Sadeeq yace,

"Alhamdulillah Allah ya bawa Abba sauki"

"Ameen"

Dr. Omar ya furta yanajin Dadi, kafin yace,

"gobe ka shirya da wuri karar karfe 8 za'ayi"

Dr Sadeeq yace,

"Sbd Allah bazaka janye ba?"

Dr. Omar yadan Bata Rai yace,

"sau nawa zance maka a'a?"

Dr. Sadeeq Yana zama kan kujerar parlon sa dake sunje part dinsa ne yace,

"gani nayi be kamata ka daga hankalin ka Kan Abinda be shafeka ba"

Dr. Omar yace,

"Dama Sai Abu ya shafeka zakayi taimako?"

Dr. Sadeeq yadan kalleshi kafin ya kawar da ido yace,

"Yama sunanta?"

Dr. Omar yace,

"ita wa?"

Dr. Sadeeq yace,

"yarinyar da zaka karbawa 'yanci"

Dan tsaki Dr. Omar yyi Yana shafa sumar kansa cikin halin ko in kula yace,

"I don't know"

Da mmki yace,

"Oh Really?"

Dr. Omar yadan tabe baki yace,

"Abinda na sani shine idan zakayi taimako kayi kawai Dan Allah bawai saika San mutum wanene ba That's All."

Girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi yace,

"uhumm Toh hakan za'ace"

ya fada Yana mikewa tare da kunna musu kallo, sai Bayan sallar Isha Dr. Omar yabar gidan duk murnar Mgnin da za'ayiwa mlm ta isheshi so yake ya sanarwa Umma Wannan good news din.

Aiko Yana zuwa gida lkcn Saratu ta Gama zazzagewa mlm masifa tana ikranin har Abada yyi sallama da mgn kenan saiga Omar yazo, besan wainar da ake toyawa ba Kawai daya gansu a tare ya dauka mgnr arziki ake Dan haka yaji ransa yyi fari sbd yanason umman su ta dinga Shiga cikinsu Amma sai ta dinga ware su kamar wasu bare, cikin zumudi Dr. Omar ya kalli Mlm sale ya rike hannayen sa kafin ya kalli Saratu da tayi tsaye tana jiran me zaice sbd itafa ko farinciki Taki jinin taga yanayi shiyasa takeso taga meya sashi Wannan farincikin? Aiko Yana kallon ta yace,

"Umma Abba ya kusa samun sauki"

"Kace me?"

Saratu ta furta a razane tana binsa da kallo, batare daya kula da yanayin ta ba ya dawo da kallon sa Kan mlm yace,

"Abba Da ikon Allah kaima zaka dawo kana mgn kamar da, Ana kyautata zaton Sihiri akai maka shiyasa aka bani number mlm Haruna zanje goben Nan nazo dashi Insha Allahu"

ya fada Yana juya bayansa gun Ummah, Saratu da hankalin ta yyi mugun tashi zani ne a hannun ta Amma sbd ba'a hayyacin ta take ba sai zanin yake kuncewa tana kamo shi, jikinta sai rawa yake tanason danne zuciyar ta Amma ta kasa, cikin tsantsar bacin Rai tace,

"Kai Maru Ashe baka da tawakkali ban sani ba?"

Dr. Omar ya dubeta da mmki, Saratu tace,

"eh na fada, sbd Allah idan cuta ta Kama mutum waye zai yaye Masa idan ba Allah ba? Ka kyaleshi man a haka wata Rana sai kaji ya bude baki yyi mgn, Amman Banda Rashin godiyar Allah Kai kullum hankalin ka shine ya za'ai yyi mgn? Toh da mutuwa yyi fah??"

Cikin danne zuciya da bawa ransa hakuri yace,

"haba Umma Yanzu duk meye abun bacin Rai Anan? Karki manta fa Allah da kansa yace tashi na taimake ka Kuma neman mgni ba haramun bane"

"Toh Dan Zamani saika nunamin bansan meye musulunci ba"

Saratu ta furta cikin tsananin takaici gaba daya lissafin ta nema yake ya dagule ba karamin firgici ta Shiga ba dajin Wannan bayanan, Dr. Omar cikin tausasa zuciya yace,

"Kiyi hakuri"

ya fada Yana dawo da kallon sa Kan mlm sale, Ga bisa mmkin sa sai yaga mlm sale Yana murmushi ganin haka sai shima yaji ransa yyi Sanyi, a bangaren mlm sale Kam tunda yaji batun Dr. Omar yake hamdala da fatan dacewa, Wannan murmushin da yake yanayi ne sbd yadda yaga Saratu ta firgice a ransa Fadi yake da sannu sannu dai wata Rana Abinda kike gudu Saiya sameki Saratu, Allah ba Azzalumin bawa bane saidai bawa ya zalunci kansa, haka yyita Wannan tunanin a ransa yyinda Dr. Omar ya zauna tare dashi har lkcn bcci kafin suka rabu.

bangaren Saratu kuwa yadda taga rana haka taga dare gaba1 ta kasa bcci gashi ta kasa Kiran Nas bare suyi mgnr sbd Dr. Omar Yana gida bataso ko kadan yaji Abinda zatace.

*Kuyi manage da Wannan please... sbd Alqawarin da nayi muku yasa nayi typing Badan haka ba Wlh Banda lokaci yau Afuwann...👏🏻*
8/15/20, 8:02 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

*Srry fans nasan kunata jira banajin Dadi ne shiyasa kuka jini shiru😌*

17....

Tun sassafe Saratu ta shirya da wuri ta riga ma Dr. Omar fita daga gidan mlm sale Yana lura da yanayin ta saidai kawai ya girgiza Kai Yana fatan Allah yasa ba wani mugun abin take Shirin Yi ba, direct wajen aikinta ta tafi wato gidansu Hajia Aisha, lkcn da taje Basu tashi ba shiyasa ta Kama aikinta da wuri Dan so take tayi ta Gama ta Isa gurin Nas bazata lamunci Abinda zai tona Asirin ta ba Sam, Aiko ta kusa Gama breakfast kenan Hajia Aisha ta sakko tun daga bakin Beni take tsaye tana lura da yanayin ta, Harta karaso cikin parlon batasan tazo ba, Hajia Aisha ce tayi mgn tace,

"Saratu har kinzo?"

Saratu ta juyo da sauri tana yake bakin Dole tace,

"eh Wlh Hajia barka da safiya"

Hajia Aisha na zama tace,

"Sannu ya aiki"

"Alhamdulillah"

Saratu ta furta tana Shirin wucewa kitchen, binta da kallo Hajia Aisha tayi batace komai ba, can saiga Safna ta Gama shirinta na zuwa skul dake tana level 1 ne a Nan Northwest, Lecture din safe garesu dining table ta wuce ta zauna tana fadin,

"Anty Sara kin kyauta Wlh kamar kinsan yau sauri nake"

tayi mgnr tana ajiye jakar hannun ta tare da zubawa kanta abinci yau ba jira, sauke ajiyar zuciya Saratu tayi lkcn da take karasa aje plate sosai taji dadi da Safna ta zuba da kanta bataso ta Bata lkci bata bar gidan ba, Ko kula mgnr Safna batayi ba ta wuce Dan dauko kular Hajjaju takai Mata, daidai zata fice Hajia Aisha tace,

"Saratu"

Saratu ta waigo tare da amsawa tana kallon ta, Alama tayi Mata da tazo, dawowa tayi tace,

"gani Hajia"

Hajia Aisha tace,

"yau Naga kamar bakya jin Dadi ko wani Abu na damun ki ne?"

Tayi mgnr tana tsareta da ido, cikin sauri Saratu ta fara washe bakin Dole tace,

"Ah Hajia ba komai Wlh kawai dai jikina naji Babu Dadi Dana tashi yau"

Hajia Aisha tace,

"Ayya sannu ai da kinyi waya kawai kin sanar basai kinzo ba"

take Saratu ta ayyana a ranta cewar Wannan dama ce da zatayi amfani da ita tabar gidan batare da an kawo komai akai ba Dan dama tana ta tunanin karyar da zata zabgawa Hajia Aisha sbd taje gidan Nas, a fili kuwa tayi kalar tausayi kamar ta arziki tace,

"Abinda nake tunani kenan dazu gaba1 banajin Dadi har wani jiri nakeji"

"Subhanallah"
Chapter 26 · 0% Book details