← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 128

Sashe 74

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana mgn sama2 cikin fada Dan dakatawa yyi har zai matsa gefe yaji ance Sageer din banza Sageer din wofi? Jin Wannan ambaton yasa Dr. Omar din ya matsa jikin kofar Dan Jin Abinda ake fada, ji yyi wani na mgn yace prof Aliyu Abinda zaka duba anan shine yaron Nan Dan babban mutum ne Kuma kasan yadda kasar tamu ta lalace kada Wannan canjin department din da akayi Masa ya jawo Mana tashin hankali a kujerar mu, tsaki Wanda aka Kira da prof Aliyu yyi yace su sauran yaran da suke samun carryover su ba mutane bane? Saishi me shafaffe da Mai shine za'a tsallakar dashi sbd ubansa wani ne? Toh Bari kaji koma Shidin Dan uban waye bazan barshi a Wannan department din ba yaje can Sashen Hausa inda na maida shi ya karanta, shiru dayan yyi kafin a hankali yace kaga nine exam officer na Wannan department din ba Haka muke da wancan H.O.D dinba sbd muna tattalin kujerar mu, yyi mgnr cikin Jin haushi sbd su biyun Nan a department su suke cin kudin Sageer shiyasa yake tsula tsiyarsa sbd ya Kama saman, Tsaki Prof Aliyu yyi yace look kabiru Ina aiki ne tsakani da Allah badan wasu can ba Dan Haka sabon tsarin department yazo duk Abinda nace hakan za'ayi, mikewa kabiru yyi cikin danne Jin haushin sa yace shikenan yyi mgnr Yana kokarin bude kofar da hanzarin sa Dr. Omar ya matsa gefe hade da sunkuyar da kansa kasa Yana jiran ya wuce shima ya shiga, lkcn da mlm Kabir ya fito Sam be lura da Dr. Omar din dake gefe ba sbd munafurci da son zuciya sun rufe Masa ido ya zaro waya Yana Danna Kiran Sageer, shi Dr. Omar jira yake yabar wajen gaba1 sai gani yyi yadan tsaya Yana mgn kasa2 yaji yace hello Sageer, daga dayan Bangaren yaji ance Faisal ne ya ake ciki da maganar mu? Cikin takaici yace Wlh Wannan taurin Kaine dashi kamar mutanen farko inaga saidai kuyi Masa Abinda kukace zakuyi na hanaku Ashe bazaiji lallami ba, Tsaki Faisal yyi yace Toh basai Yana raye zaiyi Abinda yakeson yin ba? Mlm Kabir yace tabbas, Faisal ya sake Jan tsaki yace ka saurari ambaton mutuwar sa yyi mgnr Yana datse wayar, saukar da wayar mlm kabir yyi da sauri ya Kama hanyar fita Yana fadin sai muga inda gskyr taka zata kaika Banda Kai wawane ai yanzu duniya ta koma yaki halak yaki haram da Haka yabar Sashen H.O.D gaba1, Dr. Omar dayayi niyyar zuwa gun H.O.D fasawa yyi sbd Abinda kunnen sa ya jiyo game da Wannan wayar da Kabir yyi da hanzari ya fito a department din direct motar sa ya shige, Yana shiga ya cire facing cap dinsa da mask Dr. Sadeeq da yake binsa da kallo a tsorace yace lpy dai Koh? Dr. Omar na kallon sa Kai tsaye yace karfe nawa H.O.D dinsu zai tashi? Da mmki yace nikuwa yashe nasan zai tashi? Kasan koyaushe ma yana iya tafiya, cije lips Dr. Omar yyi Yana me tsurawa steering din gabansa kallo, Dr. Sadeeq ne yace wani Abu ne ya faru? Cikin damuwa Dr. Omar yace banason a dalilina Wannan mutumin ya Rasa Rayuwar sa, a razane Sadeeq yace me suke Shirin Yi Kuma? Lumshe ido Dr. Omar yyi a hankali ya fara tsarawa Dr. Sadeeq Abinda ake ciki, Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un Dr. Sadeeq ya furta hakan hankali tashe yace Anya Sageer Yana fatan Rahamar Allah a gareshi kuwa? Shiru Dr. Omar yyi bece komai ba, Dr. Sadeeq yace lalle ya kamata muyi wani Abu akai, kallon sa Dr. Omar yyi sai kuma ya tada motar sa suna barin wajen gaba1 dake su Sadeeq din sun Gama exam yasa yabar school din itama gaba1, hanyar company dinsa ya nufa dasu, Koda suka Isa office ma duk hankalin Dr. Sadeeq din ya kasa kwanciya, Dr. Omar ya dubeshi yace ya akai duk Naga ka birkice? Dr. Sadeeq yace ai dole na birkice sbd nasan illar sharrin mutanen can, Dan murmushin takaici Dr. Omar yyi a ransa yace baka kaini sanin illar su ba, Amma a fili kuwa yace kada ka wani damu I'm very sure Babu Abinda zasuyi Masa yau, Dr. Sadeeq yace meyasa kace Haka? Dr. Omar na gyara wasu takardu yace sbd nasan bazasuyi Abinda zai zama zargi a kansu ba, zasu Dan bada lkci yadda zasu batar da shaidar su Dan suci galaba a Kan mlmin, Tagumi Dr. Sadeeq yyi yace Ina fatan kada Allah ya Basu nasara a kansa, Ameen Dr. Omar ya furta hakan Yana duba system dinsa, Dr. Sadeeq ne yace ya lbrn madam? Share shi Dr. Omar yyi beyi mgn ba, Dr. Sadeeq yace oh abin ba mgn kenan, Dan hararar sa Dr. Omar yyi Yana yatsina fuska yace Kai kasan da wata madam ni mantawa nake da nayi ajiya a gidan Nan, da mmki Sadeeq yace Omar? Dagowa Omar yyi Yana kallonsa yace naji ka Kira sunana zunubi nayi? Rufe bakinsa Dr. Sadeeq yyi yace Al'amuran ka suna bani mmki ne Wlh, Dan murmushi Dr. Omar yyi yace Kai very soon zanyi aure, Au me??? Dr. Sadeeq ya Furta hakan da mugun mmki, Dan hade fuska Dr. Omar yyi Babu Alamar wasa yace Abinda kaji, daidai lkcn Salma ta turo kofar office din hade da sallama, Zuba mata Ido sukayi ita Kuma batasan da zaman Sadeeq din ba cikin karairaya Tace I'm sorry honey nayi late yau tayi mgnr tana fadada murmushin ta, Dan kawar da Kai Dr. Omar yyi daidai lkcn suka hada Ido d Dr. Sadeeq Ashe tuntuni ya maido da kallon sa kansa, fuskar sa a hade Dan be taba tunanin zancen da suke yanzu gsky bane, dage Masa gira Dr. Omar yyi hade da furta Sadeeq ga Salma Nan ku gaisa yyi mgnr Yana Dan dage Masa gira, sai a lkcn ta juya tana kallon Sadeeq din da fuskar sa take a hade tace hallo Sadeeq a tunzure Sadeeq ya Mike Yana hararar Dr. Omar din ya daga Mata hannu batare daya sake waiwayar su ba ya fice a office din, juyo da kallon ta gun Omar tayi lkcn shima kansa a kasa yake yana Yana latsa system taji yace ga waje Nan ki zauna yyi mgnr yana Dan Dagowa ya kalleta idonsa ne ya dire shi Kan manyan hips dinta dake Masa gizo da sauri yyi kokarin janye idon nasa ya hango cikinta daya matse cikin rigar data saka dake riga da skirt ne sai Dan gyale data yafa da hanzari ya kawar da kansa hade da fadawa duniyar tunani Yana hango Ramin cibiyar daya gani a shafaffen cikinta na jiya, lumshe ido yyi yaji Salma ta katse shi da fadin ya aiki, Bude idonsa yyi da sauri fuskar sa Gata Nan dai ba yabo ba fallasa yace Alhamdulillah, shiru Salma tayi tana jiran Abinda zaice, yyinda shi Kuma Dr. Omar yaci gaba da harkar gabansa Dan shi ba gwanin Hira bane besan ma ya ake hirar ba, Salma ce Tace am..nace ba? Dr. Omar na cike wasu takardu ya girgiza kansa batare daya dago ya kalleta ba, a hankali tace kanada aure ne? Tsayawa yyi tsak be ci gaba da rubutun ba ya dago Yana kallon ta cikin tsarewar gira yace meyasa kike tmby? Shan jinin jikinta Salma tayi bakinta na rawa Tace ah..ba komi dama na tmby ne, kawar da Kai Dr. Omar yyi yaci gaba da rubutun sa zuwa can Anjima taji yace inada shi ya furta hakan a takaice, kirjin Salma ne ya buga daramm wani irin zafin kishi na taso mata ta danne zuciyar ta kafin tace Allah sarki, tayi mgnr Kamar abin tausayi, bazaki auri me Mata bane? Yyi mgnr kansa na kasa har yanzu, da mmki Salma tace me kke nufi? Dr. Omar yace Abinda kike nufi, Dan matse hannun ta Salma tayi kafin tace ah.. why not? Ai ba haramun bane, Good Dr. Omar ya Furta hakan Yana duba agogon hannun sa lkcn sallar azahar ya taho yace zan wuce mosque, Kallon shi tayi tana hadiye yawunta musamman data zubawa pink lips dinsa Ido kamar taje ta Kama ta tsotse duk Bata gaji da zama dashi ba tace sai yaushe kenan? Dr. Omar yace sai Bayan wani lkci yyi mgnr Yana kokarin yin hanyar toilet dinsa, tashi Salma tayi Tace Toh Dan Allah ka bani number ka man, tayi mgnr Kamar zatayi kuka, Kamar bazai tsaya ba Kuma Saiya juyo yace okay Nan ya karanto mata number da hanzari take sawa har ta Gama kafin ta dubeshi da murmushi sosai tace Thank you tayi mgnr tana juyawa a hankali tabe baki yyi batare daya ci gaba da kallon mazaunan ta da take juyawa ba ya wuce toilet din. ~~~~Acan bangaren Meera kuwa tunda safe da take mopping mamakin ficewar Dr. Omar tayi da wuri mutumin da sai wajen goma yake tafiya Amma 8am yabar gidan koda yaje gurin Abba ma a gurguje yyi Masa sallama ya tafi, Ganin baya Nan tayi breakfast din su kadai har me gadi bayan ta kaiwa Abba sun gaisa ta koma ta dauko na me gadin ma takai Masa, dawowa parlo tayi ta zauna kan carpet tanaci tana kallon Sunnah TV data canja, a hankali take breakfast din tana sauraron wa'azin malamin da yakeyi, ba karamin Shigarta wa'azin yyi ba harya gangaro Kan kissar Sihirin da aka yiwa Manzon Allah S.A.W, kwarai ta shagaltu dajin Wannan wa'azin Kuma ta karu ainun Saida mlmin ya kusa tashi aka fara karanta tambayoyi, anan taji an fara karanto tmbyr data Kara Jan hankalin ta, take ta fara waige2 tana neman abin rubutu Dan dazu da zatayi gyaran parlon ta canja musu waje inda Dr. Omar ya Bari jiya da dare, da hanzarin ta ta Isa wajen sbd ta hango inda ta aje Masa su, daidai lkcn aka Kara maimaita Fadar tmbyr da fadin Allah ya gafarta malam yanzu idan mutum akayi Masa Sihiri ta wanne hanyoyi za'a bi domin a warware shi? Mlmin yyi gyaran murya kafin yace Toh Alhamdulillah ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta:117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya
Chapter 74 · 0% Book details