Sashe 54
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kusan hakan ne Dan yyiwa Anty Jamila Alqawarin turo nasa magabatan suzo ayi mgnr auren su, duk Dadi da murna ta Kama su sai Nan Nan suke da junan su, a kalla dai Saida akayi Dan tabe-taben da aka Saba kafin aka rabu da juna cikin shauki Bayan sunyi musu barin naira especially ma Sageer din, kudin d akaso zubewa Meera su aka zubewa Anty shafa, Bayan tafiyar su da gudun su suka Antaya cikin gida, a daki suka tarad d mom tana shirya wasu kaya, fadawa jikinta sukayi suna dariya, mom ta dubesu tana gyara zamanta sosai tace, "Kai lpy Naga kunata dariya kamar sabon kamu?" Anty shafa ce ta zube mata kudin wajenta bakinta yaki rufuwa tace, "Mom aikin mu ya Kama su" dariya Mom tayi tana kallon kudin da Anty Jamila itama ta zube tace, "Kai yau babbar ranace a gareni yarana kun Gama min komai Wlh" Suma cikin murna sukace, "ai mom mun yadda d bokan Nan naki aikinsa Kamar cin wuta Haka yake dandanan har Abu ya juye?" Mom na dariya tace, "an Gaya muku nidin ta wasa ce? Ai Dana nace kusha kurumin ku kamar anyi an gam" Anty Jamila tace, "gsky na jinjina Miki mom ai matukar munada ke bamuda wata matsala a gidan auren mu" mom tace, "yoh ba Dole ayi babban shiri ba? Ai aure ya wuce wasa, yanzu ma so nake ace sun turo manyan su sai musan Ina mukasa gaba" Anty shafa tace, "ai zance ya Kare Dan dukansu a gigice suka tafi zasu sanar da manya" ta karasa mgnr Yana dariya, dariyar itama mom tayi tace, "kaii Amma fa nagai da aikin boka" Nan suka sa dariya gaba dayansu. Kamar mahaukaciya Haka Saratu tahau dukan Sahabatu tana sambatu Fadi take, "Shegiya marar wayo Banda Rashin wayo yaushe Zaki Bari kazamin Dan Tasha ya turmushe ki?" Dakyar Sahabatu ta kwace daga rikon saratun tace, "ni Umma ki daina dukana Haka Nan ko ni nace a daura min tallar?" Saratu a tunzure tace, "au sai yanzu zakiyi korafin na Dora Miki tallah?" Zumburo baki Sahabatu tayi tace, "Toh koma dai meye ai a dalilin tallar ne Kuma Dan tsabar Rashin tausayi kihau Kaina kina duka kinsan Abinda nake dauke dashi ko so kike ki kasheni?" Ciza yatsa Saratu tayi tana huci ta gallara mata harara tace, "Shikenan Amma Wlh baki Isa ki fita Koda kofar gida bane bare ki jawomin zagi" tabe baki Sahabatu tayi tace, "ni fitar me zanyi? Idan na fita ma Ina zanje?" Saratu taja tsaki tace, "oho maki" tayi mgnr tana shigewa daki, Koda ta shiga dakin ma kasa nutsuwa tayi Dan Haka ta zaro wayarta ta Kira Nas, bugu biyu Nas ta dauka tace, "idan an jiki matsala ce" Saratu tace, "Dan Allah kibar Wannan mgnr akwai mgnr da nakeso muyi" Nas na dariya tace, "mgnr me?" Saratu tace, "so nake na kawo Miki Sahabatu ki rikemin ita harta haihu a wajenki" Nas Tace, "yaushe kikayi Aurenta da har ta samu cikin?" Saratu tace, "shiyasa na tunkare ki d mgnr sbd ke kadai ce Zaki rufamin Asiri" Nas tace, "Amma ke meyasa bazaki rike 'yarki ba?" Saratu cikin damuwa tace, "banason abin kunya ne tun kafin mutanen unguwar Nan Susan da zaman cikin Nan nakeso tayi kaura damu" dariya sosai Nas tayi tace, "Wai gudun abun kunya kike Saratu? Amma fa kinada abin mmki Wlh" ta karasa mgnr tana dariya, "nidai Dan Allah ki Amsa min bukata ta" Nas tace, "Shikenan Amma fa da sharadi" Saratu tace, "name?" Nas tace, "Zaki dinga biyana dubu goma duk wata" a razane Saratu tace, "haba Nas kin manta yadda muke dake ne?" Nas tace, "yadda muke kamar ya? Haduwar barikice fah? Atho Dan ba haduwar Alkhairi bace ta hadamu Dan Haka Koh gwamnati Bata aikin banza" Jan Numfashi Saratu tayi tace, "Shikenan naji Ina lefin na baki dubu biyar?" Nas tace, "Ashe ba so kike na rike Miki itan ba saiki nemi wata" tayi mgnr tana kokarin rufe wayar, da sauri Saratu tace, "Toh Shikenan naji zan biyaki" Nas na washe baki Kamar tana gabanta tace, "yauwa 'yar gari Ashe kin gane," nan suka yanke wayar Nas na dariya sosai a fili tace, "Haka kurum zanyi ta Miki wahala ba lada? Gashi bana sana'ar komai bare na samu Dan Haka a jikin ki zan tatsa Nima." Ita kuwa Saratu tashin hankalin tane ya karu yanzu kenan duk wata saita zare dubu goma cikin kudin Albashin ta? Wannan ai ta bada kusan duka kudin nata kenan Amma Yata iya? Haka ta fito da niyyar sanarwa Sahabatu yadda ta yanke. ~~~Tun yana office yaga labulayen office dinsa suka fara kadawa a hankali, wata sassanyar iskace take shigowa a hankali daga karshe ma iskar ce take kadawa sosai, tashi yyi zai kulle window dinsa ya hango gabas ta hadu sosai tayi baki Kamar za'a kece da ruwa, tsayawa yyi kawai ya zubawa gabas din Ido, knocking akayi be juya ba Amma ya bada damar shigowa, PA Dinsa ne ya shigo a gurguje yace, "Dr. Omar ni zan wuce gida kafin ruwan Nan ya kece tunda lkcn tashi yyi" kallon sa yyi yaga harya rungumi jakar aikinsa Dan Haka ya girgiza Masa Kai batare d yyi furucin komai ba, juyawa Habib yyi Yana tabe baki yace, "wata Rana dai dakai da kurma bakuda banbanci mutum Allah ya tsaga Masa baki Amma mgn ta gagare shi ba kurma ko bebe ba" da Wannan tunanin yabar office din gaba1, Shiko Dr. Omar maida hankalin sa gabas yyi Yana hango wasu fararen balbelu sunata gudu a jere gwanin sha'awa sbd yadda saman tayi baki sai farin nasu ya Kara kawata wajen, Dan murmushi yyi yanaji kamar ya Kama su, kafin yyi aune yaji an kece da ruwa kamar da bakin kwarya ruwa Kuma me irin feshin Nan, hakan yasa har cikin office dinsa ta window ruwan na shigowa, be rufe window dinba saima Jan Numfashi da yyi ya lumshe idonsa Yana shakar sanyin ruwa da Kuma feshin dake taba Masa jiki da fuska. 8/15/20, 8:05 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA*