← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 128

Sashe 104

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shirin maida kudin daya fito dasu ya hango farin Abu da sauri ya dakatar dashi yace, "caje Wannan kudin hannun naka" dawo da hannun sa Ayuba yyi Yana warawa kuwa saiga takardar a ninke salati ya dire cikin murna yace, "Alhamdulillah Wlh itace ai Wannan kudin ya bani da safe kafin su wuce tare dasu na ninke na aje...." Karbe takardar Omar yyi hannun sa na rawa ya warware ta wani irin farinciki ne ya Kama shi besan lkcn daya saki lallausan murmushi ba har hakwaran sa na bayyana, cikin Jin Dadi yace, "na gode mlm Allah ya saka" Mlm Ayuba yace, "ai kuwa Nima na gode Allah Wlh, Wannan Aba tun safe a kanta na kasa samun sukuni" hannu Omar yasa a Aljihun sa Nan ya zaro kudin da besan yawansu ba tsabar farinciki ya damkawa mlm Ayuba yace, "gashi Nan tukwici" Yana Gama fadin Haka ya juya da hanzarin sa, Kallon kudin mlm Ayuba yyi da murna Yana washe baki yace, "Allah sarki Ashe Alheri ke bibiyata tun safe ban sani ba." Dr. Omar kuwa daga Nan gidansa ya nufa ransa fari tas, Kiran Sadeeq yyi bugu daya ya dauka cikin Jin Dadi yace, "Sadeeq an samu" da murna Sadeeq yace, "dgske?" Omar yace, "yesso Dan Haka ka fara hada kaya zamu Adamawa" mikewa daga zaunen dayake Sadeeq yyi ya tashi tsaye d mmki yace, "Omar kana ganin lkci kuwa?" Omar yace, "Dan Allah ka daina duba lkci I just want to see my wife kawai" "dare fa ya kusa Omar har yaushe mukaje Adamawa bafa Nan da jigawa bane?" Omar yace, "an so? Son samu ma ace Daren yau tare mukayi shi..." "Dan iskaa..." Sadeeq ya katse sa d fadin Hakan Dan yaga kamar ya fara Saba lamba, 'yar dariya Omar yyi yace, "pls kazo Nima gida zan wuce na hada kayana daga Nan muje muyi masu sallama saimu tafi" Sadeeq yace, "Wai yaushe ka zama me naci ne Omar?" "Idan akan sugar babe ne u don't see anything..." "Sugar babe?" Sadeeq maimaita hakan Yana sakin baki kamar Yana kallon sa, "ehnn...watin?" Omar ya Fadi hakan shima, rufe bakin nasa Sadeeq yyi Dan yaga alama Rashin kunya Omar din yakeji Dan Haka yace, "saimun Hadu" "Alright." Omar ya Fadi hakan shima Yana katse wayar, Yana Isa gidansa kuwa da saurin sa ya wuce samansa kayansa ya zuba a traveling bag dinsa ya fito a gurguje, Mlm habu na ganin sa ya Mike da sauri Yana zare Ido yace, "yallabai lpy kuwa Naga kuke ta zari daidai?" Murmushin da be taba ganin ya Masa ba ya sakar Masa yace, "mlm habu abubuwa ne suka faru dayawa a safiyar yau ciki ma harda samun warakar Abba Yana mgn yanzu" cikin matukar murna mlm habu yace, "Allahu Akbar kaji Allah babban sarki, Alhamdulillah Allah sarki Koh can zakane Nima na bika nayi Masa murna?" Dr. Omar yace, "a'a ai baya gida zancen da tsayi gashi Kuma Ina Kan hanya" da mmki mlm habu yace, "wani wajen ka nufa yanzu?" Dr. Omar yace, "eh Insha Allahu Adamawa zan tafi" mlm habu yace, "dare fa ya kusa magriba ta gabato?" Dan murmushi Omar yyi Yana sa hannun sa a Aljihu ya debo kudi masu kauri ya Mika Masa yace, "bansani ba ko zanyi sati ko akasin haka sai yadda Abin dai ya kasance" karba mlm habu yyi da murna sosai yace, "Toh shikenan Allah ya tsare Hanya Allah ya kiyaye" "Ameen Insha Allah zan sanar da Abba sai yazo Koda d safe ne ku gaisa" "Toh madallah a sauka lpy" "Ameen" Omar ya furta hakan kafin ya fice a gidan dama be shigo da motar sa ba Dan Yanason Barinta a gidan daddy Dan Haka Yana fita ya Bata wuta. Suna tsaye a compound sbd Abba ya sanar musu inda omar din ya tafi Dan da farko da suka duba Basu ganshi ba zaton su an sace musu shi ne shiyasa hankalin su ya fara tashi, tun daga gate ya hango su a tsaye mmki ne ya Kama shi hakan yasa be karasa parking space ba ya fito, Hajjaju ce Tace, "Jikana ka samu tashin hankali" isowar sa kenan ya dubeta da 'yar dariyar sa yace, "me nayi d zaisa hankalin ku ya tashi?" Hajjaju Tace, "duk mun laluma lungu da sako na gidan Nan baka Nan sai muke tunanin ko sace min Dan kyakkyawan ango akai" dariyace ta Kama Omar hakan yasa duk suka zuba Masa ido da mugun mmki Dan tunda yazo gidan dazu Basu ganshi cikin fara'a ba sama da yanzu, hakan yasa Abba yace, "an dace?" Da fara'a yace, "eh Abba yanzu ma Shirin tafiya nayi zan jira Sadeeq yazo saimu wuce" kallon mmki suka Kara Yi Masa Daddy yace, "Adamawan Ayau?" Mummy Tace, "ai na dauka Shirin dawowa gida kayi" Sunkuyar da kansa yyi Yana murmushi, Safna tace, "ai kuwa zan bishi Nima inaso muje" Dagowa yyi Yana kallon ta, daddy yyi 'yar dariya yace, "lalle surukar tamu she's special" kunyace ta Kama Omar hakan yasa shi juya kansa Yana wani basarwa, daddy yace, "shikenan Amma sai zuwa gobe" da sauri Omar ya juyo Yana kallon daddy cikin damuwa, daddy yace, "yes yanzu dare yyi Omar gashi yau duk baka zauna ka nutsu ba tunda kaji good news ai yakamata ace kaje ka huta ne idan ta ganta Haka wujiga2 ai saita dauka Dan dambe ka koma" dariyace ta Kama mutanen wajen shikuwa Omar ya juya keya Yana tura baki shifa gsky ba Haka yaso ba Amma Kuma bazai iya yiwa daddy musu ba, Suna tsayen kuwa saiga Sadeeq ya shigo da tasa traveling bag din, Hajjaju tace, "hoo ashe duk kun Gama Shirin ku" Sadeeq Yana dariya yace, "Wlh nace ya Bari da safe Amma duk ya matsa Wai yanzu" daddy yace, "ai zancen ka Haka yake da safen zaku tafi Insha Allahu" "Toh Allah ya nuna Mana safiyar da Alkhairi ni Bari na koma" Sadeeq ya Fadi hakan, Omar ya riko shi Yana fadin, "ba inda zakaje" Mummy Tace, "Sadeeq ai Nan ma gida ne Safna rakasu inda aka Gama gyarawa Ameer dazu" Safna Tace, "Toh" Nan suka bi bayanta tana gabansu yyinda Sadeeq ke yiwa Omar dariya kasa2 so yake su kebe ya Masa Iskanci iya son ransa dama tun safe yake tarashi Akan Meera yadda ya gigicen Nan yasan dole da walakin goro a Miya bazai Bari yasha lami ba Saiya tsokane shi, shi Kuma Omar Banda turo baki ba Abinda Yake, Dan jinsa yake tamkar yyi tsuntsuwa ya ganshi gaban Meera.
Chapter 104 · 0% Book details