← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 128

Sashe 46

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~~~Cinyarta ta kaiwa duka a razane tana mikewa d sauri sbd Jin mugun cizon da sauro yyi Mata, waige2 ta fara Yi Nan taji gidan ya sake Yi Mata shiru tsitt, hankalin tane yadan Fara tashi "Kai Anya lpy kuwa? Har yanzu be iso ba" ta Furta hakan a fili tana mikewa tsaye sbd Jin har Wai Isha tayi, dake akwai Alwala a jikinta kawai ta tada sallar ta. Bayan ta idar ne taji wata irin Hamma ta Kama ta tuni ta hangame baki tana shafa cikinta sbd Jin yadda yake Kara kamar me ulcer, Cije lips dinta tayi tana rintse ido tabbas idan zata iya tunawa yau ko kyakkyawan breakfast Bata samu ba Dan cewa akai ya Kare sai wani guntun tea na dad daya rage data gani lkcn datazo yin wanke2 ta dauka ta kurbe sbd Daren jiya bataci komai ba shiyasa Tasha sbd yunwa, dukda ranar bikinta ne yau din ba'a daga Mata kafa ba Saida tayi aikin gida, Dan numfasawa tayi data tuna tun lkcn Bata samu wani abun takai bakinta ba, Dafe kanta tayi tana nazarin Wai meke Shirin faruwa da ita ne? Tashi tayi tsaye ta fara tattaki tana Dan yawo a gidan ita kadai sai kace Aljana anan fa yunwar ta fara cin karfin ta hakan yasa ta dawo wajen zamanta tana me bude kunnen ta sosai Koda zataji Alamun zuwan Dr. Omar din, juyi ta farayi a wajen data kwanta sbd yadda taji cikin nata shima Yana juyawa yunwace taci karfinta sosai Kai kace zata sheka, a garin juyin nata ta tabo wani Abu me Dan dumi a gefen ta, abinka Dame Jin yunwa zumbur ta Mike tana karewa inda ta taba kallo, "Oh! Ya Salam" Meera ta Furta tana dafe goshi Ledar da Dr. Sadeeq ya Bata ne dazu Akan Omar Idan yazo ta bashi, jawota tayi tace "Bari dai Naga meye a ciki" tana budewa kuwa taga gasassar kaza da fresh milk a ciki sai tashin kamshi take Tasha Hadi, wani irin tsinkewa yawunta yyi Habawa batare da tunanin komai ba hannun ta na rawa ta fisgo Naman tana Bismillah ta afka bakinta, cin Naman take bana Wasa ba tare da kurbar fresh milk, Saida ta kusa cinye fiye da Rabin tsagin kazar kafin ta hakura daci Dan ta koshi, rufe murfin fresh milk din tayi shima kafin taja gefe tana gyatsa hade da hamdala, Wata irin nutsuwa ce ta saukar Mata, sai yanzu tunanin ta ya dawo daidai yyinda gumi ya jike Mata jiki jalab, kallon Naman tayi sai take taji tsoro ya Kama ta, yanzu idan Omar yazo me zatace Masa? Gashi da alama shi kadai zaici tunda komai guda daya ne a gurin, lumshe ido tayi a fili tace, "nayi Masa bayani nasan zai fahimta" da hakan ta sake gyara zamanta tana Dan kishingida sbd yadda taji iskar wajen tana kadawa a hankali, Wasa2 shirun Dr. Omar ya zarta tunanin Meera, kallon Nokia dinta tayi taga 12am Dan har Dan bcci ne ya sureta ta farka a firgice dalilin cizon da wani sauro yyi Mata, koda taga 12am hankalin ta ba karamin sake tashi yyi ba, ba Abinda takeji sai kukan tsuntsaye da haushin karnukan unguwar, Tsoro ne ya Kama ta ainun ta waiga jikin kofar parlon still tana Nan a garkame, "Na Shiga uku kodai Sadeeq mistake yyi banan bane gidan?" Ta Furta hakan a tsorace tana Dan waige2 duk jikinta rawa yake sbd haushin karnukan da suka cika Mata kunnuwa, gaba1 Meera ta rude ba Mafita Dan Haka kawai ta bude akwatin ta Nan ta dauko mayafin ta na kwanciya shima tun na mamanta ne Bata rabuwa dashi Dan Yana tuna Mata mamanta, zama tayi ta fara karanto Addu'ar bcci Dan ta sare da zuwan Omar tana tunanin dole Asubar fari tabar gidan Dan d alama anyi mistake wajen kawota, Saida ta Gama Addu'o'in ta kafin ta tofa gabas da yamma kudu da arewa sanna ta shafe jikinta, duk Wannan abubuna tanayi ne a tsorace yafa mayafin tayi har kanta kafin ta rintse idonta sosai Dan har yanzu jikinta rawa yake sbd tsoro, kafin wani lkci dake dama ba ishashe bcci take samu ba kwanakin Nan tuni bccin yyi awon gaba da ita. Acan bangaren Dr. Omar kuwa, tunda ya sanarwa Saratu shi bikinsa Babu bidi'a ba wani taro ya dinga Shan Gori da miyagun maganganu, Shidai Abba besan dalilin dayasa Omar yace bayason taro ba sai kace bikin dole dukda Abba baya mgn harda shi akaje daurin auren besan meyasa ba Amma tabbas yyi farinciki da Wannan auren na Omar sosai, a wajen Saratu kuwa cewa take dama tunda kayo gadon talauci yaushe zakaso ayi Taron biki? Da alama yarinyar da zaka aura ma duk kanwar ja ce Banda Haka wacce cikakkiyar budurwar ce zata yadda da biki ba taro kamar bikin mujiya? Shiru Dr. Omar yyi Mata be tanka ba sbd duk yadda Saratu take kushe auren nasa jinsa yake ko a kwalar rigar sa Dan shi kadai yasan wanne irin aure yyi, shirun da yake shi yake karawa Saratu kaimin ci gaba da surfa bala'in ta tace Arziki na binka kana tirjewa Ka mannewa auren da babu riba. Jefar da wayarsa Dr. Omar yyi lkcn da suka Gama Waya da Dr. Sadeeq Akan yakai Meera gidansa, Dan Jan tsaki yyi yana me fitowa a dakinsa Dan yin Alwala sbd Jin Kiran Sallah da yyi, be dawo gidan ba sai Bayan yyi sallar Isha, Koda yazo gidan ma zama yyi wajen Abba, Abba Babu bakin mgn bare ya tmbyeshi yaushe za'a Kai amaryar tasa? Dan ya sanarwa Abba ya Kama haya sbd har yanzu be sanarwa Abba dukkan halin da yake ciki ba daga korar sa a skul har zuwa company din Alhaji Abdullahi, Rike hannun sa Abba yyi Yana Dan jijjigawa hade dayi Masa mgnr kurame da hannu, Dr. Omar dake kallon sa ya gane me yake nufi Sarai, shi duk bayajin dadin Wannan zumudin auren da Abba yakeyi sbd ba auren So yyi ba, Kuma ba wani me lasting bane za'a rabu, Toh Amma ya ya 'iya? Haka dai kamar kullum ya danyi murmushi Yana duban Abba yace, "Sai zuwa gobe za'a kaita" yyi mgnr Yana kawar da idonsa da sauri sbd bayason Abba ya gano Gskyr, binsa da kallo Abba yyi kamar be gamsu da mgnr Omar din ba Dan Haka da mmki ya juyo d fuskar Omar din gareshi yyi Masa Alama da hannu Meya faru? Daidaita yanayin sa Dr. Omar yyi cikin dakiya sosai kamar gske yace, "Eh Abba sai gobe sukace zasu kawota I thought ma yau ne sbd ni dasu din duk ba wani bidi'a akai a bikin ba" girgiza Kai Abba yyi cikin gamsuwa Amma a ransa yanaso yyiwa Omar din mgn ne aure ko a kauye ai Ana shagali bare shi auren birni cikakken Dan boko gashi Dan gayu, saidai ya bar hakan a Matsayin kowa da ra'ayin sa kila shi Kuma nasa ra'ayin kenan, Omar ne ya katse shi da fadin, "Bari na Shiga ciki Abba" ya Furta hakan Yana mikewa tsaye, Saratu data fito daga bayi taja tsaki da karfi tace, "aikin kenan Haka za'a Kare dakai da dangin amarya kowa ba kwabo Tunda ka Musa zabina aurenka bazaiyi Albarka ba" ko kala Dr. Omar bece Mata ba ya wuce ciki abinsa a ransa Fadi yake Toh dama wanne Albarka za'a nema a auren daya zama na wucin gadi? Balle botir din rigar sa yyi ya zame ta kasa sannan ya cire dogon wandon sa, karowa fankar sa gudu yyi kafin ya zauna gefen katifar sa, Yana bude wayarsa yaga misscall din Sadeeq kusan 5, Dan tsaki yyi ya maida wayar gefe Dan yasan dalilin Kiran nasa yanzu zai fara Masa wa'azi be kamata ya zauna yabar 'yar mutane acan ba, dauko system dinsa yyi ya kunna yana me duba ayyukan dazai gabatar a company zuwa gobe Dan ko a company din ma ba'asan yyi aure ba, Shidai auren gashin Nan dai saikace na magulmata, Saida ya Gama nazarin Abinda yakeyi kafin ya tashi yayo wanka, Bayan ya Gama Shirin bccin sa ya dauko heater ya dumama ruwan zafi sharp2 ya hadawa kansa coffee ya kurbe, Bayan ya Gama yyi kwanciyar sa batare da tunanin komai ba, Yana rintse ido kuwa yaga fuskar ta ta bayyana a gareshi lkcn data zabga Masa Mari, cikin kunar zuciya Yaja wani irin mugun tsaki me yaji2 kafin ya sake juyawa dayan barin, Addu'a yyi ya shafa sannan ya rufe Ido ko takan tunanin halin da take ciki beyi ba Kawai bcci yyi awon gaba dashi. A bangaren Ameera kuwa bccin Nan nata rabi da rabi tayi sbd cizon sauron dake damunta, har kwallar takaici Saida tayi sbd cizon d suke Mata gashi haushin karnukan d ake kamar a cikin gidan suke sbd ihu, a daddafe dai taje Asuba a Haka, Wannan ruwan famfo shiya taimaka Mata tayi tsarki da Alwala, Bayan ta idar Bata Dade ba kuwa ta bingere da bcci sbd Rashin samun yinsa a Daren jiya. Shi kuwa Dr. Omar sai 9am ya Gama Shiri cikin Shigar kananan Kaya sunyi matukar Yi Masa kyau dama Shidin ma gwanin kyau ne, laptop dinsa ya dauka zai fito a daki kenan yaga Kiran Dr. Sadeeq, dauka yyi da sallama, Dr. Sadeeq yace, "ah lalle ango kasha kamshi ai tunda na Kira jiya naji shiru nasan cewa Ana tare da madam" ya Furta hakan cikin tsokana Yana dariya, tsaki Dr. Omar yyi yace, "zaka fara iskancin naka Koh?" Dr. Sadeeq Yana dariya yace, "oh Iskanci? Dani dakai waye Dan iskan?" Sake Jan tsaki sosai Dr. Omar yyi kamar zai tsinkewa Dr. Sadeeq kunne sbd ya fahimci inda ya dosa cikin kufula yace, "Amma ka cuceni banza" dariya sosai Dr. Sadeeq yyi yace, "so how far? Ya madam?" Dr. Omar be Amsa Masa ba shima yace, "so ya Shirin exam? Kasan yau zaku Fara" sassauta dariyar sa Dr. Sadeeq yyi yanajin wani irin tausayin Omar din a ransa sun taso tare, burinsu tun suna secondary su zama manyan Doctors yau gashi dalili yasa ya zama GM a company, Dr. Omar ne ya katse Masa Shirun da fadin, "Okay sai kun fito Allah ya bada sa'a" yyi mgnr Yana kashe wayar sbd yadda yakejin wani iri shima, kasa
Chapter 46 · 0% Book details