← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 128

Sashe 52

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ya Gama dariyar muguntar sa kafin ya mike tsaye Yana duban Faisal yace, "Bari naje na watsa ruwa lkci ya gabato" "okay Nima Bari naje na shirya" Faisal ya furta hakan shima Yana tashi anan suka rabu. Acan wajen su Anty shafa kuwa har sun siyo duk wani snacks da suke bukata lkcn da suka dawo gida nan suka tarad da mom Ashe harta dawo, binsu da kallon mmki tayi tace, "tun dazu sai duba ko'ina nake a gidan Nan ban ganku ba Abinda ya dace ace kuna kitchen ko ya fasa zuwan ne?" Zama sukayi Kan kujera a gajiye kafin Anty Jamila tace, "fita mukayi" mom Tace, "kunsan da aiki a gaban ku kuka fita?" Anty shafa ce tace, "Mom Abinda zai amfane mu mukaje muka Nemo" tayi mgnr tana tura mata Ledar hannun ta, budawa mom tayi taji kamshin snacks ya bugi hancin ta, ta dago tana kallon su tace, "siyowa kukayi?" "Gashi Nan Kuma kin gani mom" Anty Jamila ta Furta hakan tana ci gaba da fadin, "kin sani Sarai dai Babu Abinda muka iya ta bangaren kitchen tun jiya muke fama mun gagara shiyasa muka yanke shawarar siya a waje" Girgiza Kai Mom tayi batare da wani damuwar Rashin iya girkin nasu ba tace, "dama ai bakuyi Kama da masu shiga kitchen ba idan aka samu nasarar janyo hankalin Sageer ma ai ku da kitchen saidai daga nesa" dariyar Jin Dadi sukayi kafin Anty shafa tace, "yauwa mom Ina mgnin?" Jawo jakar gefenta Mom tayi tana fadin, "tun safe da kuka ga na fice wajen bokan nawa naje dama yace yau na koma da sassafe sbd lakanin Yana jikin sanyin safiya Kuma an fiso a ranar da aka bada mgnin ayi amfani dashi shiyasa na koma" tayi mgnr tana dauko wasu kullin mgni kala biyu, bude dayar Ledar tayi tana shinshinawa kafin ta Mika musu, karba sukayi suna binta da kallo Dan Karin bayani, mom tayi murmushi tace, "Wannan shine turaren wanke tunani, a Haka zaku ganshi kamar turaren wutane Amma a zahiri akwai siddabarun da aka hada a ciki Dan Haka kunajin Sageer ya Kira yace gashi a gate daya daga cikin ku zata tafi ta turare parlon baki dashi sannan abar kaskon wutar da mgnin hayaki naci gaba da tashi Toh a daidai lkcn da Sageer ya shigo ya shaki Wannan kamshin turaren Ina me Tabbatar muku ya manta da asalin dalilin kawo shi gidan Nan, ya mance da duk wani zancen Meera dake kwanyar kansa, tunanin sa zai ta'allaka ne akan ki shafa" ta karasa mgnr tana kallon Anty shafa, murna ce ta Kamasu duka biyun Kamar su dira tsalle Dan Dadi, mom ta sake Miko musu dayar Ledar tace, "Wannan kuma shi ake Kira da cafke zuciyar Wanda kkeso, a cikin drink zaku barbada Masa bazai taba ganewa ba da zarar yasha mgnin Nan tofah aiki ya kammala domin kuwa zaiji soyayyar ki ta damqe Masa zuciya, zai koma yanzu kece a zuciyar shi ba wata can shegiya Meera ba, Ina Kara Tabbatar muku idan kukayi duk yadda nace batare da kuskure ba Toh kuwa kun Gama kame Sageer ya zama namu" ta karasa mgnr tana dariya, dariyar Suma sukayi cikin farinciki, kafin Jamila tace, "Toh Mom naji kinata Anty shafa ni Kuma Faisal din fa?" Mom tace, "ai gani nayi shi kedin yakeso ba wata a gaban shi" Jamila ta turbune fuska tace, "haba mom ko kanada kyau ai saika Kara da Wanka" dariya Mom tayi tace, "dawasa nake kema Zaki iya amfani dashi ai duk Wanda kayi nufi dashi Toh dashi mgnin zaiyi aiki Dan Haka Zaki iya Yi Masa kema" rungume mom sukayi cikin tsananin farinciki suna fadin, "Gsky mom keta dabance bamu da kamar ki" mom na dariya tace, "ai komai zan iya Yi akanku matukar Ina numfashi" Haka dai sukaci gaba da kulla tsiyarsu har suka Gama kafin suka Mike Dan zuwa yin wanka. *******Takowa yake tun daga can saman Beni cikin izza da Isa har izuwa kasa, Meera da tun dazu take mopping batasan da sakkowar tasa ba sai kamshin turaren sa daya mamaye wajen yasa ta dago da sauri, tsaye yake ya harde hannayen sa duka biyun Yana binta da wani irin kallon kaskanci yadda kasan cleaner Haka yake ganinta, wani tsohon dogon hijab dinta ne daya Gama jemewa sbd wahala tun acan gida dashi take aiki sbd Bata cika zama Haka ba musamman idan ta lura su Anty shafa da Mom suna yawan sa mata Ido a halittar ta da yadda take ganin hasadar su a fili yasa ta ware hijab din aikin gida, yawan aikin gidan da take dashi ne yasa ya jeme ya lalace domin ya kode sosai Bata hakura dashi ba ta taho da kayanta har gidan Omar sbd can gida sunce kada ta sake ta bar musu Koda Dan kwalinta ne basa bukata, ganin cewa Nan dinman sammakal ne da gida yasa ta dauko hijab din Dan ba wani hijabai ne da ita ba Dan Basu fi uku ba idan tana sake su duka tana aiki dasu Toh kuwa lalle zata Rasa na fita unguwa, gyara tsayuwarta tayi tana Dan since hijab dinta data daure ta baya sbd kada ya hanata aiki sosai murya na rawa Tace, "barka da safiya Ya Omar" "Mtwsssss.." Dr. Omar Yaja wani irin tsaki me sauti Yana matsawa gabanta, kallon gefen kumatun ta yyi take ya tuno da Marin data sharara Masa farkon haduwar su, Wannan tunani yasa zuciyar sa ta Kara tunzura da ita, ba tsammani Meera data kafe shi da ido taji ya kamo mata haba, kallon sa tayi da mmki zatayi mgn taji rikon bana Masa yyi mata ba, cikin kaushin murya yace, "Kece mace ta farko data taba breaking record a tarihin rayuwata" yyi mgnr Yana matse mata gefe da gefen habarta cikin mugunta Kamar Wanda za'ayiwa yaro durar mgni, jijjiga kanta Meera ta farayi taji kikam ta kasa kwacewa daga hannun sa, yyinda Kuma Dr. Omar yaci gaba da fadin, "bansan ke wacce irin mummunan kaddara bace a gareni dahar ace ranar farko da muka fara haduwa Kika samu zarrar wanka min mari a fuska" ya karasa mgnr Yana cije lips dinsa sbd zafin tuno da yadda ta marenshin, kwalla ce ta fara cika mata Ido tana kakarin mgn so take ta bashi hakuri Amma ya rike mata bakin, "da wayo na dai iyayena Basu taba marina ba saike kazama dake" yyi mgnr Yana bin jikinta da kallo na wulakanci kafin ya sakar mata bakin hade da dauketa da wani Marin bazata, dukawa Meera tayi kasa a gigice jikinta na rawa tana share hawayen dake sintiri Akan fuskar ta cikin Kuna da radadi, wani tsakin Dr. Omar ya sake ja yanajin Kamar ya dauketa yyita buga kwallo da ita har saita babbale zai huta yaji Dadi, ganin kamar Yana batawa kansa lkci ne ya saki wuci me zafi kafin yyi azamar barin gidan gaba1, Yana taku na daya Ana biyun yaji an kamo Masa kafa, juyowa yyi a tunzure yaga Meera ta hade hannayen ta biyu cikin roko tace, "Dan Allah ya Omar Dan Allah kayi hakuri Wlh duk Abinda nayi maka daga haduwar mu har kawo yanzu yanada dalili Kuma..." "Good point" Dr. Omar ya Furta hakan Yana Fisge kafarsa data rike San d tayi ransa a hade yace, "Tun kafin ki furta hakan na fahimta tun bayan da Kika Kara Tabbatar min da dalilin d kike ikrari yanzu, yeah na sani, da dalili Mana, ai duk Abinda kikayi shiri ne Right?" Hankali tashe tace, "no ya Omar ba Abinda kke nufi bane fa? Pls ka fahimceni" Dan murmushin takaici Omar yyi Yana me hade fuska Kamar farko duban cikin kwayar idonta yyi sosai yace, "ki godewa Allah Kinyi nasara akan Omar a cikin Shirin ku na takun farko, but yanzu aka fara wasan Ina me Tabbatar Miki bazaki sake cin nasara Akaina ba ke da munafikin naki Sageer a sannu a hankali saina koya muku hankali dukan ku" yyi mgnr yana me barin wajen cikin takunsa na Isa ko waiwayen ta be karayi ba, dukawa a wajen Meera tayi tana me fashewa da kuka Fadi take, "ka cuceni Sageer, Insha Allahu Nima bazan barka ba zanci gaba da Kai kukana wajen Allah ya bimin hakkina agun duk Wanda ya zalunce ni" ta karasa tana ci gaba da kukan ta. Dr. Omar kuwa Koda ya fito a gida direct ya wuce AKTH Dan yau yasan su Dr. Sadeeq basuda Exam, saida ya shiga ciki ma Dr. Omar ya Kira Dr. Sadeeq a waya, Bayan sun gaisa ne Dr. Omar yake sanar Masa ai gashi Nan yazo ciki, Dr. Sadeeq yace, "Toh ka karaso mana" Dr. Omar yace, "no akwai wani uzuri daya kawoni ne" "okay Bari na fito" Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana kokarin kashe wayar yaji yace, "pls inaso ku taho da Dr. Amina" Da mmki Sadeeq yace, "Me kace?" Dr. Omar na tabe baki Kamar Yana gabansa yace, "nasan kaji" yyi mgnr Yana katse wayar, bin wayar da kallo Dr. Sadeeq yyi Yana fatan ace ba wani tuggun Dr. Omar yake Shirin Yi ba, ganin tsayuwar bazata kaishi ko'ina ba yasa ya Mike Dan Nemo inda Dr. Aminan tayi, Yana bude kofa kuwa sai Gata ta taho itama zata shigo, matsawa gefe Dr. Sadeeq yyi yace, "yauwa shikenan ma" binsa da kallo tayi tace, "kamar ya?" Dr. Sadeeq yace, "Omar ke neman ki" "Da gske?" Ta Furta hakan da karfi bakinta yaki rufuwa, Tsayawa kallonta Dr. Sadeeq yyi cikin mmki yace, "look Amina me kike shiryawa abokina ne Haka?" Dan daidaita nutsuwar ta tayi tana kawar da Kai gefe tace, "me zanyi Masa kuwa?" Girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi Dan ya kasa yadda da ita fatansa dai Allah yasa ba wani mugun abin taje ta shirya Kan Omar ba har yake nemanta Haka, Katse Masa tunanin tayi da fadin, "Yana Ina?" "Biyoni" Dr. Sadeeq ya furta hakan a takaice, binsa tayi da sauri kamar ma zata wuce shi duk Dadi ya kamata daman yau take Shirin taje har gida ta ciwa Saratu mutunci sbd Taki gaya mata komai akan Abinda ta Sata sai gashi cikin ruwan sanyi yazo, tun kafin su Isa wajen take baza ido taga ta inda zata ganshi Amma wayam take gani
Chapter 52 · 0% Book details