← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 128

Sashe 86

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ga bisa mmkin sa yaga kofar dakinsa dai ake Masa nuni cikin kaduwa ya kankame jikinsa yadda yaga bakin kofar ita kadai naci da wuta sosai tamkar gobara ba komai ya sake daga Masa hankali ba sai yadda yaga iya Wannan wajen ne kawai ke ci da wuta, ji yyi ta bayansa an kwashe da dariya Yana juyawa yaga Saratu ce ta fisgoshi cikin mugunta tana fadin bana fada maka ba? Nan zaka Kare ta karasa mgnr tana hankada shi cikin wutar..._ A firgice Mlm sale ya farka daga mummunan mafarkin dayake jikinsa sai rawa yake yyind zuciyar sa ke dauke da salati sbd b bakin mgn, ji yyi an kwalla Kiran Sallah hakan ya Tabbatar Masa da cewar lalle Asuba ce tayi take ya kalli inda yake yaga akan sallaya yyi bcci Wannan Abu ba karamin daure Masa Kai yyi ba shikuwa wanne irin nannauyan bcci ne ya kwashe shi Haka? Jin ana Shirin Kiran sallar shigane ya sashi mikewa da sauri, kallon bakin kofar sa yyi yaji gabansa ya buga da karfi hakan ya sashi yin Bismillah ya fito da kafar dama, Bayan ya dawo daga Sallah ne yana shigowa gidan yaga Saratu na saka hijab a tsakar gida, kallon sa tayi tana 'yar dariya Tace, "bama fada bamu cika ba Dan Haka nayi Nan" ta karasa mgnr tana ficewa a gidan, binta da kallo yyi gaba1 kansa a daure mafarkin jiya har yanzu be Gama fita a ransa ba, so yake ya Shiga dakin nasa ya kasa saima matsawa da yyi jikin kofar sa saitin inda yaga a mafarki ya tsura Masa ido, haka kawai yaji Yanason Buda inda ya hango kamar yadan Burma yyi Rami, fartanya ya dauko yanajin yakini da kwarin gwiwa a ransa Haka ya nufi wajen bakinsa dauke da Addu'a, Yana sa fartanyar kuwa yaji gun ya Burma Nan yaga Dan karamin kulli kamar tsumma a ciki, a rude Ya jawo kullun ya ganshi Dan karami, sosai ya danne ransa yyi ta maza ya zare wasu kananan Allurori da aka hade kullin dasu Yana cire Allurar karshe yaga wani irin bakin hayaki ya fita daga wata 'yar mitsitsiyar laya ta ciki, mlm sale besan lkcn daya wurgar da ita kasa ba a mugun firgice bakinsa ya fara Furta "Qalu innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" Fadar furucin Nan nasa keda wuya yaji kansa ya Sara sosai Nan yaji bakinsa ya Kara Furta "A'uzubikalimatil lahi tamma min sharri makalaq..." Take Wannan layar dake fitar da hayaki wacce ya wurgar ta Kama da wuta Nan mlm sale ya zube kasa Yana kwararar da wani irin amai baki-baki, Kore-kore yana Nan tsugunne Saida ya Gama amaye duk wani Abu marar kyau a cikinsa kafin yaji makogwaron sa wasai Babu alamun tokarewa, muryar sa ta dawo garassss yanzu Yana iya mgn, "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Mlm sale ya jera fadin Hakan yafi a kirga take yyi sujjar godiya ga Allah, dakinsa ya fada da hanzari ya dauko kudin da Dr. Omar yake bashi ya zura a Aljihu kafin yayo waje da sauri lkcn gari ya washe sosai be yiwa kowa mgn ba Dan ya fiso ya fara Furta kalamai a gaban Dr. Omar da Kuma Meera, shiyasa Saida yaje can bakin titi ya tsayar da me napep hade dayi Masa kwatancen unguwar dazai kaishi. Kusan Makara Dr. Omar yyi domin Saida aka fara Shiga Salla ma ya tashi, har lkcn Meera na bcci Bata farka ba tana kwance cikin faffadan kirjinsa tayi luff kamar mage, kallonta yake yanajin zuciyar sa cike da Nishadi, Dan kissing dinta yyi a goshi kafin ya cireta a jikinsa a hankali, Yana motsawa kuwa ta farka ganin a jikinsa take tayi azamar tashi da sauri ta matsa can gefe, kallon ta yyi cikin taushin murya yace, "I'm sorry" hararar sa tayi ta tashi da niyyar wucewa toilet kafarta taso gurdewa sbd kasan gado dayaso Fadar da ita, da sauri Dr. Omar ya taso gareta duk zaton sa zafin ciwon ne a rikece yace, "sannu" yyi mgnr Yana rikota, kwace hannun ta Meera tayi batari datayi Masa mgn ba ta dukar da kanta tana cije lips, gaba1 Dr. Omar ya rude a iya tunanin sa dai mgnin daya Bata zai rage mata zafi Amma ya akai har yanzu Bata samu sauki ba? Matsawa sosai jikinta yyi Yana rikota tana tirjewa, harya samu ta daina motsi sbd rikon da yyi mata a hankali yace, "Meeraa.... Pls ki sanar Dani har yanzu kinajin zafi ne?" Lumshe ido tayi a hankali tanajin takaici kamar ta doke shi, juyo da fuskar ta yyi Yana kallon ta har yanzu idonta a rufe yake yace, "pls kimin mgn Mana Meera tun jiya kike fushi Dani" bude idonta daya fara cikowa da ruwa tayi Tace, "na rokeka Ya Omar ka daina damuna idan son samu ne ma ka bani space" cije lips dinsa yyi kafin yace, "haba Meera Wai wanne irin laifi nayi d kike ta korana Haka?" Janye jikinta tayi daga nasa tana jifansa da kallo Tace, "wato ma bakasan me kayi ba Koh? Duk yadda nakeson tattali da mutuncina Saida ka rabani dashi, ya kkeson na sanar da Wanda zai so ni tsakani da Allah bawai Dan jikina ba?" Dafe kansa Dr. Omar yyi gaba1 ya Rasa yadda zaiyiwa Meera bayani ta fahimta, Mikewa yyi beyi Mata mgn ba ya fice a dakin dan zuwa masallaci gani yake Saiya Gama sallar kafin ya samu nutsuwar Yi mata bayanin yadda zata fahimta, saidai kashhh..., Wannan shirun da yyi Mata, da ficewar da yyi ya jawo wa Meera fadawa cikin tsananin takaici tunanin ta ya Bata toh dama ba sonki yake ba ai Kuma ya samu Abinda yakeso Toh zaman me zaiyi? Take taji zuciyar ta na tunzura, a zuciye ta wuce toilet Sharp2 ta fara Wanka, ranta na suya tana dawowa daki ko Mai Bata shafa ba ta Saba doguwar riga da Katon hijab hade da jawo trolley dinta da yake shirye tuntuni Tayo waje, tana zuwa bakin gate kuwa ta tarar da me gadi shi ya dawo ma daga masallaci, dubanta yyi da mmki ya Isa gareta Yana fadin, "Hajia lpy dai Koh?" Koh kallon inda yake beyi ba ta fice a gidan gaba1, Tana fita kuwa ta samu wata Adaidata ta sharo da gudu da sauri tasa hannu ta tare batare data fada Masa inda zataje ba ta shige ciki, Saida suka fita daga unguwar me Napep yace, "Hajia baki sanar Dani inda zamuje ba?" hankalin Meera ne ya Kara tashi yanzu Kuma Ina ta nufa? Take zuciyar ta Tace gidan mahaifin ki Mana ai dama hausawa sukace da Uba ake Ado, nan ta samu kwarin gwiwar sanar dashi unguwar su, sunyi tafiya me nisa kafin suka Kai ga zuwa bakin gate din su Meera, Meera da tun dazu kirjinta ke bugawa jikinta na rawa ta kasa fitowa a cikin napep din, sai me napep din ne ya sake fadin, "Hajia munzo fa" ya Fadi hakan a Karo na uku, cikin sanyin jiki Meera ta fito jikinta sai rawa yake ta Mika Masa kudinsa kafin ta fito, tana zuwa kuwa taga Ashe an canja me gadinsu, Karasawa tayi zata shige sabon me gadin ya taho da sauri yace, "ke baiwar Allah ba mgn sai kokarin Shiga gida?" Tsam Meera tayi ta kasa motsi kila umarnin Mom ne yasa yanzu Kuma Babu me Shiga, suna Haka sukaji an bude kofar wata irin faduwar gaba ce ta riski Meera lkcn data ga Dad dinta ne ya fito, Dad da be lura da Itan ba yaji me gadin Yana fadin, "yauwa Alhaji kaga Wannan yarinyar ce take Shirin Shiga na mata mgn tamin shiru" Juyowa dad yyi take yyi Arba da Yarinyar da ya Dade Yana nema ruwa a jallo be ganta ba, cikin tsananin farinciki ya Isa gareta yana fadin, "Ameeeraaaa..." Ware Ido sosai Meera tayi da mmki Anya kunnen ta ne yaji Abinda dad yace Kuma fuskar sa da walwala? "Allahu Akbar dama itace Ameerar da kke nema?" Sabon me gadin ya Furta hakan fuskar sa dauke da mmki, ware hannun sa dad yyi yace, "taho Nan Ameera your dad is missing you" wata irin kwallar farinciki ne ya tarar wa Meera saidai har yanzu ta kasa motsawa daga inda take tanajin Kamar mafarki take, dad ya sake matsawa inda take yace, "Meera kina fushi Dani Koh? I'm sorr..." Be karasa rufe bakinsa ba kuwa ta taho dadan gudunta ta fada jikinsa tana rungume shi Nan ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya.
Chapter 86 · 0% Book details