← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 128

Sashe 95

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ba ita ta haifeshi ba gskyne, Ashe itadin ba mahaifiyar sa bace, Abba ne yace, "ai bama ita kadai ba harda Wannan Nas din da suka kulla abin tare za'a Kama su" kallon sa Hajjaju tayi Tace, "Dan Allah yi Mana bayani daya bayan daya yadda akai ta dauke Mana jinin mu tasa nata" Nan Abba ya fara sanar dasu tun daga farkon yadda yaji hirar su har kawo lkcn datayi Masa Asiri ya daina mgn kwata2, gaba1 wajen Ba Wanda be girgiza da lbrn Abinda Saratu tayi ba, take suka fara Allah wadai da halinta mikewa daddy yyi yace, "muje a dauko ta basai mun jira tazo ba" Nan Abba ya sanar musu shirinta na zuwa gun boka jiya, "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" suka sake sakin salati gaba1 hankalin su ya sake tashi ba Kamar ma Mummy da gani take duk silarta Abubuwan ke faruwa shiyasa duk ta kidime Kamar tayi hauka, ganin Haka yasa daddy yace, su wuce a fara Kai report kafin su dawo tunda ba'asan inda suka nufa ba sannan yace kowa ya rike Addu'a Insha Allahu Babu Abinda zai samu dayansu. a bangaren Sageer kuwa Ai tunda Abba ya Gama bada lbrn kullin da Saratu tayi a hankali ya sulale yabar parlon batare da an ankare dashi ba, Dukda Dr. Omar Yana cikin tashin hankalin Abinda Rayuwar sa take ciki hakan besa ya manta da batun Meera ba, Dan Haka Yana ganin daddy zai sake turashi suje wajen Kai report ya dafe kansa da sauri kamar Wanda ya Sara Masa, kasa yyi da sauri Yana dafa kujera, cikin azama daddy ya rikoshi Yana dubansa yace, "Omar kana lpy?" Dan yatsina fuska yyi Yanason pretending kawai sbd yaje gurin Meera yace, "my head" ya furta hakan Yana Dan cije lips dinsa, cikin damuwa yace, "muje cikin gidan kasha mgni" shiru Dr. Omar yyi yana Sunkuyar da kansa, Daddy yace, "idan kasha saika huta kaji?" Still Dr. Omar be dago ba Dan ba Haka yakeson ji ba, sai yanzu Mummy tayi murmushi tace, "Kasan be fara sakewa damu ba Inaga a barshi ya tafi gida Saiya dawo Anjima" wata irin boyayyar ajiyar zuciya ya saki har ma taso yasa a gane yyi saurin yin fuska, Safna ce Tace, "tho Bari na bishi tunda bayajin Dadi" a rude Dr. Omar ya kallota shikenan zata Bata Masa plan dinsa, Mummy Tace, "No Wannan surutun naki ma Kara Masa ciwon zaiyi" lumshe ido yyi yanajin kaunar Mummy na ratsa Masa zuciya, ba yadda suka iya Haka dai suka barshi ya tafi yyinda suka rike Abba a gidan hakan yasa sai shi kadai ne ya tafi. Tunda yahau titi yake sharara gudu burinsa ya Isa ga Meera gefe guda tunanin Rayuwar sa ne fal ransa, mmkin yadda akai yyi rayuwa batare da iyayensa na Asali ba yake, lbrn tamkar a film kk Novel? Wannan wacce irin matace Saratu? Yanajin Kamar yafi kowa shiga damuwa da tashin hankali akan Abinda yaji, Haka zalika yafi kowa son daukar mummunan mataki Kan Saratu datayi sanadin rabashi da Ahalin sa, saidai yanzu Meera ce a ransa shiyasa ya kasa maida hankali akan Abinda ke faruwa, tunanin yadda zai fuskanci Meera ne ya sake Fado Masa yanzu Kuma mezai ce mata?. Koda ya Isa gida ma ko parking beyi d kyau ba ya wuce can parlon sa, da Dan saurin sa ya bude kofar Yana shiga yaji Kara sosai ta saman sa anata buga kofar dafe kansa yyi domin ya manta da wanzuwar Salma a gidan, tsaki Yaja kawai ya wuce dakin Meera direct, kallon Kan gadon yyi yaga Alamar tudun bargo hakan sai yasashi tunanin Koh har yanzu bcci take? Dan guntun murmushi yyi Yana lumshe Ido Daren su na jiya yake tunawa Yana hango yadda take ta Masa rigima, kasa tsayuwar kofar dakin yyi yanajin wani Abu na taso Masa acan kasan ransa game da ita gefe daya Kuma cije lips dinsa yake Yana tuno gardi da dadin daya kwasa a gareta, cikin sanda ya lallaba Yanason Jin Koda duminta ne kadata farka harya fara Hawa gadon beji Alamar motsi ba, hakan yasashi Jin Dadi yasan Sarai zata wanke Masa duk wata damuwa da yake cikinta a yanzu, Saida ya daidaita Kan gadon ya fara janye katon bargon da yyi tudu a wajen, Yana fara ja bega Alamun ta ba be kawo komai a ransa ba yaci gaba da budewa, a mugun firgice yyi wurgi da bargon Yana kallon wajen da yake wayam ba Alamar Meera, cikin hanzari ya diro akan gadon Yana nufar toilet tunanin sa ko can tayi, Nan ma Yana budewa yaga wayam, Toh kardai kitchen ta nufa Nan ya fito daga dakin ya nufi kitchen Nan ma shiru, take hankalin sa ya fara tashi duk Inda yake tunanin zai ganta Bata wajen Nan ya haura saman sa Yana tunanin ko dakinsa taje, Yana shiga dakin nasa ma Babu Alamar mutum ya Shiga saima bugun kofar da Salma take tayi tun dazu ya cika Masa kunne cikin takaici ya fito yazo wucewa ya cire key din jikin kofar kafin yaci gaba da tafiya Yana son komawa dakinta duk hankalin sa ya fara tashi, Yana shiga dakin nata take hankalin sa yakai wajen data aje trolley jiya yaga wayam besan lkcn daya Furta "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" ba, a mugun firgice ya fito Yana bin hanyar waje direct wajen me gadi ya nufa bakinsa na rawa tun daga nesa ya fara kwalawa mlm habu kira, mlm habu dake daki ya fito da sauri daidai lkcn Dr. Omar ya iso yace, "Mlm habu ko kaga ficewar Ameera?" Mlm habu yace, "kwarai kuwa tun bayan tafiyar ka masallaci tabar gidan Nan Ina mata mgn ma Bata kulani ba" cikin karaji Dr. Omar yace, "Whyyyyy....???? Meyasa ka barta ta tafi....???" Ya karasa mgnr Yana dunkule hannun sa daya hade da kaiwa dayan hannun nasa naushi take mlm habu ya girgiza da yanayin reaction din Omar, jikinsa na rawa yace, "kayi hakuri yallabai nayi zaton da saninka ta tafi" wata irin doguwar tsuka Dr. Omar yyi yanajin badan darajar shekaru ba Babu Abinda zai Hanashi wankawa mlm habu Mari, tsayuwarsa a wajen Bata da Amfani Dan Haka a zuciye yyi hanyar fita Yana Ciro wayarsa Dan Kiran Dr. Sadeeq, saura kadan ya buge mlm habu ma Allah yaso yyi azamar matsawa gefe, kafin ya Shiga motar tasa yyi dialing number Dr. Sadeeq yanajin ta fara ringing ya bude motar ya shige, Yana driving yaji ringing din har ya katse Dr. Sadeeq be dauka ba, tsaki Dr. Omar yyi ya sake bin number still Dr. Sadeeq be dauka ba, cikin kunar Rai ya fara mgn shi kadai Yana sake dialing number Fadi yake, "ka dauki Kiran Mana Sadeeq" be Ida rufe bakinsa ba kuwa yaji alamun ya dauka, Dr. Omar najin Haka ya fara mgn da sauri2 Yana fadin, "haba Sadeeq Wai Ina ka shigane Ayita kiranka baka picking call" Cikin yanayin bcci Dr. Sadeeq yace, "haba Ango irin Wannan ihu Haka ai saika fadamin dodon kunne" tsaki Omar Yaja yace, "Dan Allah ka tashi ganin Nan zuwa inda kke I need your help" wata irin dariyace ta kwacewa Sadeeq har Yana rike ciki yace, "Kai Mijin Ameera Angon salamatu kace jiya kayi babban aiki harka manta da asalin waye Kai wato Doctor kana neman Dr. Sadeeq ya duba ku, ah lalle Salma tayi kokari" wani mugun tsaki Dr. Omar Yaja me daci-daci yace, "Wai meyasa Ana zancen serious kana sa wasa a ciki?" still Dr. Sadeeq na dariya yace, _Toh Angon salame saika iso" wani irin takaici ne ya sake makure Omar ji yake kamar ya fasa ta wayar ya naushi Sadeeq koya huce da takaicin hadashi da Salma dayake, Kai tsaye ya kashe wayar Yana karawa motar gudu Yana fatan daga can Sadeeq ya rakashi gidansu Meera Dan bazai iya jure rashinta a kusa dashi ba.
Chapter 95 · 0% Book details