Sashe 112
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take hakan yasa Sadeeq yyi tunanin bcci yake Musamman da yyi lamo kamar me bccin, Sadeeq ma bccin ne ya sace Shi, shikuwa Omar kusan kwana yyi Yana sincewa da warwarewa. Acan gidansu Meera kuwa Suna parlon mamy Inna fure nata surfa fada Ahmad ya shigo, mmki ne kwarai ya Kama shi yanzu Nan fa yadan fita waje Toh meya faru Haka yaga kowa fuska kadaran kadahan? Gyaran murya yyi Dan ya lura sallamar da yyi ba'a jishi ba, Inna fure ce ta waigo tace, "yauwa gara da Allah ya kawo ka Ahmad muje yanzun Nan ka maida mu gida" Ahmad yace, "gida Kuma Inna?" Inna fure Tace, "eh Haka nace ko anan zan kwana?" Kallon Mamy data sunkuyar da kanta yyi ya waiga ya hango Asma'u a rakube fuskarta na nuna Alamar damuwa kafin ya dubi Inna fure yace, "wani Abu ne ya faru?" Cikin fada2 Inna fure Tace, "Toh Menene ma be faru ba Ahmad? Wai yaron Nan umara Dan jaraba har Adamawa ya biyo Ameera bayan duk wulakancin da yai mata" a firgice Ahmad yace, "Inna waye Kuma Umara? Meye hadinta dashi? Meyasa ya biyota?" Tsaki Inna fure taja Tace, "idan Ina tuna matsayin sa Yana bani takaici" kirjin Ahmad ne ya buga da karfi Yana duban Ameera da kanta ke bisa cinyar Inna fure tana goge hawayen da suka ki tafiya yace, "Dan Allah Inna ki sanar Dani kin sani a duhu" tabe baki Inna tayi Tace, "Wai shi Nan mijinta ya kwaso kafafun sa Wai zai tafi da ita Kai wasu mutanen ma basuda kunya Sam" ko kadan Ahmad be fahimci duk sauran maganganun da Inna take ba sai kalmar "Wai shi Nan mijinta" ita take ta Masa yawo akai hakan ya jefashi cikin matukar tashin hankali, dakyar ya iya furta, "Inna dama Tanada aure?" Inna fure Tace, "kwarai kuwa Amma dab muke damu since Wannan aure Dan bamu gaji wulakanci ba" ko kadan yanzun ma be sake fahimtar sauran bayanan nata ba sai amsar ke Masa shawagi a Kwakwalwa "kwarai kuwa" tsam ya Mike beyi mata mgn ba yyi hanyar fita, Inna fure Tace, "Kai da nace kazo ka maida mu gida?" Ko sake waiwayen ta beyi ba yyi gaba da sauri jikinsa na rawa. Zaton Inna wani uzuri ne ya Kama shi saidai har wajen 10pm ba Ahmad ba lbrinsa idan anje part dinsa a kulle wayarsa a kashe hakan yasa badan taso ba ta kwana a gidan nasu, Ameera na dakin Asma'u tayi lamo tunanin duniya duk ya isheta, Asma'u tuni tayi bcci hakan yasa take ta tunanin Abinda ya faru batasan meyasa takejin Rashin Dadi a ranta ba saidai wata zuciyar tana Bata kwarin gwiwar gwara data fada Masa hakan domin ta fitar Abinda ke ranta, cije lips dinta tayi tana tuno yadda Inna fure ta kora su a wannan lkcn bazata banbance me taji a ranta ba Sam saidai tana ganin hakan shi ya dace dasu Abinda ya shuka shi yake girba, da Wannan tunanin nata bcci yyi awon gaba da ita. Washe garin ranar ma da wuri Omar da Sadeeq suka shirya har sunyi waya dasu Mummy ma sun sanar mata Abinda ake ciki saidai Suna nuna musu kamar cewa komai normal ne shiyasa suka gamsu kwarai, Suna hanyar su ta zuwa gidan Alhji Kabir Sadeeq ya dubi Omar daya zurfafa a tunani yadan zungure shi hakan yasa shi Juyowa Yana kallon sa, Dan murmushi ya Masa yace, "kana ganin zata saurare mu yau?" Sauke nannauyan ajiyar zuciya Omar yyi kafin yace, "ko Bata saurare mu ba bazan Yi kasa a gwiwa ba Sadeeq, nasan nayi wasa da damata amma yanzu Kam bazan yadda Meera tayi nesa Dani ba duk rintsi Ina Nan Kuma Abinda matar Nan ta fada gskyne inada lefi matuka Dan ko kyalle ban taba siyawa Meera ba bare nasan meye damuwar ta" Dan Jan Numfashi Sadeeq yyi kafin yace, "matsalar shine ka dauki abin da zafi sosai, ka yanke hukunci cikin fushi shiyasa duk Abubuwan ya kwabe maka" shafa lallausan gashin sa da yaji gyara yyi Yana lumshe Ido kuskure Kam an riga an yishi saidai kawai a fuskanci gaba, me taxi dinsu ne yyi parking Nan Sadeeq ya biya shi suka fito, Suna zuwa bakin gate din aka bude musu domin Alhji Kabir ya shaida musu idan sun dawo kawai a barsu su shiga, shigarsu gidan kuwa yyi daidai da fitowar Alhji Kabir Yana Amsa waya, hango su da yyi ne ya musu alama su matso, matsawa sukayi shi Kuma Yana kokarin yanke wayar da yake, Bayan sun Isa wajensa ne suka duka har kasa Suna diban gaisuwa, Alhji Kabir yace, "yanzun Nan nake mgnr ku nace jiya bamuyi exchanging numbers ba" Sadeeq yace, "hakane shiyasa ma mukayi sauri kafin ku fita" Alhji Kabir yace, "Shikenan ku biyo mu muje" Nan sukabi bayansa Yana gaba. Ahmad dake leke ta window ne ya zame a hankali zuciyar sa na harbawa da sauri2, jiya kusan kwana yyi Yana juyi Sam ya kasa yadda da Wai Ameera Tanada aure, yarinyar data sace Masa zuciya tun a karon farko daya ganta gsky batayi Masa Kama dame aure ba Sam, ya Dade Yana wannan tunanin Yana sane ya kulle parlon sa hade da kashe wutar dakinsa jiya kawai Dan kada a dameshi, yanzun ma damuwar ce ta sashi tsayuwa gaban window Yana leke tunda ya hango su Omar kirjinsa ya buga da karfi especially daya gane Omar din lkcn dayake Kiran Meera jiya, rintse idonsa yyi ya koma bakin gado ya zauna hade da dafe kansa. Zamansu keda wuya aka fara kawo musu abin Kari, Alhji Kabir ya dubesu bayan an gama aje musu komai yace, "kuyi breakfast zanje na shirya kafin muzo ayi mgn" gyada Masa Kai sukayi shikuma ya fice waje, Yana fita kuwa Omar ya maida bayansa Yana lumshe Ido, zamowa Sadeeq yyi ya hada tea cup biyu ya dubi Omar da idonsa ke rufe yace, "ya kamata ka rage Wannan damuwar Omar kasan Abinda hakan ke haifarwa ga lpyr mutum" bude idonsa Omar yyi yace, "sadeeq kenan Kaima kasan a tsakankanin kwanakin Nan Ina haduwa da Abubuwane kala2 da farko Rashin sanin Asalina, ga Kuma bacewar Meera ya kke tunanin zan dau lamarin? Na tabbata da wani ne Wlh sai zuciyar sa ta buga sbd dawanne zaiji? Zafi bisa zafi lkci guda?" Sauke numfashi Sadeeq yyi sai yanzu ya lura Ashe har wata 'yar rama Omar din yyi lalle abun ba sauki danma omar din jarumi ne ya iya dauke duk wannan kaddarar data Fado Masa lokaci guda, cikin matukar tausayin sa yace, "Kayi hakuri komai zai zama normal Insha Allah" Dan guntun murmushi yyi kafin yace, "Haka nake fata" Mika Masa cup din yyi yace, "karbi ko kadan ne kasha tunda kaki Bari muyi breakfast acan" karba Omar din yyi ya fara Sha a hankali, ko Rabin cup din beyi ba yaji tea din ya gundure shi hakan yasa shi ajiyewa, shima Sadeeq din be wani Sha sosai ba ya aje Dan shimafa kusan acikin damuwar yake, Suna zaune Haka dad da Alhji Kabir suka shigo, gaishe da dad sukayi har kasa ya Amsa musu da sakin fuska hakan yasa Sukaji Dadi matuka, zaman su dad keda wuya Inna fure d Meera suka shigo, Dagowa Omar yyi da sauri Yana karewa Meera kallo yadda take ta dukar da kanta tana rabewa Bayan Inna fure, ita kuwa Inna fure fuskar Tace a hade dakyar ma su dad suka lallabata tazo akan kawai anaso aji ta bakin yaran kowa yasan Matsayin sa, zama tayi su Omar suka sake zamowa har kasa Suna kwasar gaisuwa kamar bazata Amsa musu ba sai Kuma ta juyo ta Amsa gaisuwar tasu, zamansu kawai sukai a kasa Basu koma kan kujerar ba, Alhji Kabir yace, "toh madallah, dama Abinda yasa nace kowa yazo Nan shine inaso naji dalilin dayasa shi Omar din ya nemi auren Ameera Alhalin baya sonta" shiru Omar yyi Yana dukar da kansa Sam bayason yaji ance baya sonta, Sadeeq ne yyi gyaran murya kafin yace, "idan ban Shiga tsakani ba ko za'a bani Wannan damar na Amsa tmbyr da aka Masa?" Alhji Kabir yace, "eh Babu damuwa ai Amsa mukeso" Sadeeq yace, "Nagode" Nan ya gyara zaman sa yace, "harga Allah a farkon auren da frnd Dina yyi da Ameera ba komai bane a ciki Banda daukar fansa" "fansa??" Duka suka Furta hakan da mmki, shi kuwa Omar kansa na kasa be dago ba, Sadeeq yace, "kwarai kuwa, dalilin Wannan fansar kuwa shine...." Tiryan-tiryan ya fara Basu lbrn yadda abubuwa suka faru tun daga lkcn da Omar yazo ceton Meera da Sageer yaso Yi mata fyade da Kuma son kwatar mata 'yan dayaso Yi a kotu....karshe ya karkare mgnr da fadin..."a maimakon Ameera ta bada shaidar gsky ta Fadi Wanda yaso rusa mata mutuncin ta shine ta maida mgnr akan Omar inda ya jawo Masa zubewar mutuncinsa a idon jama'a dama dukkan 'yan skul dinmu, Cikakken Likita ne shi me Jiran license dinsa a satin zamu Fara zana final exam dinmu Amma sanadiyar shaidar da Meera ta bayar hakan ya jawo Kora daga faculty dinmu shima duk a cikin plan din Sageer ne a takaice dai komai ya lalace game da Omar duk a sanadin furucin Meera shiyasa yyi auren fansa a kanta a ganinsa hakan shi zai rage Masa radadin Abinda tayi Masa....." shiru parlon ya dauka har Ahmad dake jikin window a labe Saida ya girgiza da Wannan lbrin, Inna fure kuwa Kamar wacce ruwa ya cinye ta Tama kasa Dagowa ta kalli Omar din, dad Kam kunyace ta Kama shi kwarai Haka zalika Alhji Kabir duk sunyi tsumu2, Meera kuwa a hankali ta rabe can gefen kujera jikinta na Bari duk Kuma Omar na kallon ta ta Wutsiyar Ido shima kansa a duke, gwauron Numfashi Alhji Kabir Yaja kafin ya dubi bangaren Ameera yace, "duk Abinda ya fada hakane?" A tsorace Meera Tace, "eh Abba" _Hasbunallahi wani'imal wakil_ Suka Furta hakan a ransu shikenan Kuma me zasu ce da Omar? Cikin fada dad yaso Yi mata mgn Alhji Kabir ya dakatar dashi, kafin a kunyace yace, "Omar shine dalilin aurenka da Meera?" Omar ya girgiza Kai be dago ba, Numfashi Alhji Kabir Yaja toh duk idea ta kwance Meera ai ta kunce musu zani