← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 128

Sashe 84

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

data kawo ta dinga kawomin ayoyi da hadisai na nuni da muhimmancin taimako, nidai nace mata banason su samu sabani a zaman su na tare Tace Wannan Babu matsala a takaice dai Abba da gudunmawar ta yakai har Saida tasa aka buga IV din bikin Nan a maimakon a dage bikin sai bikin ya juye Kaina yanzu ya rage befi 3days ayi ba, ta bukaci a sanar maka hakan a kurarren lkci domin bataso Kai ka Hana Dan tausayin yarinyar take sosai" Tunda Dr. Omar ya saki baki Yana sharara karya Meera ta saki kunnuwa da Ido, da hanci, da labba tana sauraron kalaman Dr. Omar da mugun mmki, yyinda shi Kuma Abba mmkin yarintar Meera yake karara, kallon su kawai Dr. Omar yyi Yana jiran yaga Abinda zai faru, dukar da kanta Meera tayi tana kokarin share zazzafar kwallar data gangaro mata taji Abba na kakarin mgn, Hakan yasa ta dago da kanta hawaye be daina taruwa a idonta ba taji Mgnr Dr. Omar ta katse su da fadin, "so yake ya tmbyeki Abinda nace ha....k..a..ne?" Ya karasa mgnr muryar sa na sarkewa sakamakon Juyowa da Meera tayi ta kafe shi da ido, kawar da kansa yyi da sauri Yana Dan yake fatansa ace Meera Bata Rusa Masa duk shirinsa ba, Juyowa Meera tayi tana kallon Abba hawaye na kwarara akan kumatun ta Kara gefen hijab dinta ta goge tana daga Kai muryar ta na rawa Tace, "ha..ha..Kane.. Abba" ta Ida mgnr hade da fashewa da kuka ta Mike tsaye da sauri tabar musu wajen, hakan yasa Abba ya kalli Dr. Omar da sauri yanajin a ransa kamar be yadda da maganganun Omar din ba, Ganin Haka yasa Dr. Omar ya nuna fuskar damuwa yace, "ka gani koh Abba? Itace Nan Tace nayi kullum idan zatamin mgnr sai ta zubar da hawaye na Rasa wanne irin tausayi gareta" ya karasa mgnr Yana yatsina fuska, Sam Abba ya kasa fahimtar su biyun yanaso ya gaskata wata zuciyar na karyatawa abun gaba1 ya daure Masa Kai hakan yasa be nuna wata Alamar komai ba ya Mike tare da wucewa dakinsa, dafa goshi Dr. Omar yyi hade da sauke ajiyar zuciya kafin shima ya tashi ya wuce parlo, tana Kan kujera sai sharar kwalla take taji alamun shigowar sa hakan yasa ta tashi a zuciye ta fara mgn Tace, "meye dalilin ka nayin karya Dani?" Kallon ta yyi ya watsar Yana Shirin hayewa sama ta bishi da sauri tana cakumo gaban rigar sa Tace, "sbd kanason Kara aure saika hada karya Dani? Dole sai Dani zakayi auren? Idan kanada ra'ayi hanaka zanyi??" Tallafo kumatun ta yyi yana kallon kwayar idonta yace, "Daman ke wacece da Zaki hanani yin aure? Matan da akayi auren soyayya dasu ma Ana musu kishiya bare ke da Babu digon sonki ko kadan a Raina" wani irin bacin rai ne ya sake Kama Meera Nan tasa hannayen ta biyu tana dukan faffadan kirjinsa Tace, "cewa nayi dama ka so ni? Kawai nace meyasa zakayi karya Dani?" Ta karasa mgnr kuka nacin karfin ta batasan dalilin da gaba1 ta Shiga tashin hankali ba, turar ta gefe yyi saura kadan ta Fadi yasa hannayen sa ya tallafo ta Nan idonsa ya sarke da juna suna yiwa junan su kallon-kallo, Saida suka kwashe kusan 3mins a hakan kafin Dr. Omar ya Kara jawota ta da nufin ta gyara tsayuwar ta sai ji yyi ta fada kirjinsa, besan lkcn da ya saki Numfashi ba dalilin Jin tudun kirjinta da yyi, d sauri kuwa ya matsa da ita gefe Yana Kama kafadar ta da duka hannu biyun sa ya kalleta up and down yace, "cikin dayan biyu, ki fara Shirin barin gidan Nan ko Kuma ki shirya zama 'yar aikin matata wacce ta kasance zabin Raina kin gane?" Bin hannayen nasa daya rike mata kafadu tayi take tasa nata hannun ta turar da nasa gefe tana kallon sa sosai tace, "basai ka sanar Dani hakan ba ni nasan Abinda ya dace Dani nayi" ta karasa mgnr hade da bar masa wajen tana Masa bye-bye da hips dinta, Dan bushashen yawu Dr. Omar ya hadiye Yana lumshe idonsa kafin yyi sama Yana Danna wayar sa, Kiran Sadeeq yyi Saida ta kusa tsinkewa kafin ya dauka, Dr. Omar yace, "Ina ka Shiga ne inata faman Kira" Dr. Sadeeq dake cike da haushin sa sbd Wannan auren daya rakitowa kansa yace, "yanzu fa ka Kira? Ko kayi wani ne Bayan shi?" Dan murmushi Dr. Omar yyi yace, "ya kamata mu hadu mutattauna duk Abubuwan da za'ayi a event" Dr. Sadeeq yace, "shi Kuma Wannan auren harda even za'ayi?" Dr. Omar na zama gefen gadonsa yace, "kanayin Abu kamar kana manta Abinda ya faru a baya, ka sani Sarai nace maka wancan auren da nayi ba aure so bane, a lkcn da zanyin auren zabin Raina lkcn za'a Tabbatar da biki nayi" shiru Dr. Sadeeq yyi tabbas ya tuna yadda sukayi a lkcn bikin Meera shi gaba1 tausayin yarinyar yake shiyasa baya goyon bayan Omar din ya Kara aure domin ya fuskanci matar dazai aura ma idonta a bude yake, "Hello kanajina kuwa?" Dr. Omar ya furta hakan, Dr. Sadeeq yace, "shikenan zuwa gobe zamu hadu" "okay Thanks" Dr. Omar ya Furta hakan kafin suka yanke wayar. matsawa jikin pillow dinsa yyi ya kishingida Yana me lumshe idonsa tunowa da duk Abubuwan daya faru yake yadda akai ya amince da tayin Salma, tun Daren ranar da Meera tayi Masa Wulakanci yasha Alwashin saiya Bata mmki, a washe garin ranar Yana zuwa office Salma ta shigo lkcn taci kwalliya sosai kayan jikinta sun kamata, tana zuwa ta durkusa Masa tana sanar Masa an takura Mata a gida ya taimaka ya Aureta kafin su aurar da ita ga Wanda bataso, a lkcn kallo yyi Mata na tsanaki ya fahimci tabbas ta kusa cika da irin matar da yakeso domin bazai yiwa kansa karya ba Meera ta fita kyau da kyakkyawan diri nesa ba kusa ba a takaice dai Meera itace irin zabin ransa da yake nema dare da Rana shiyasa ranar farko daya ganta naked ya birkice ya Kuma Susuce domin be taba zaton Haka halittar ta take ba Ashe kallon kitse yake yiwa rogo, duk yadda yaso ya lashi zumarta ita Kuma Taki Bari, Koda ya Gama kallon ita Salman sai yaji a ransa Wannan damace dazai fahimtar da Meera cewa ba ita kadai bace mace, shiyasa batare da Bata lkci ba ya amince da tayinta anan ta sanar Masa idan Babu damuwa bikin Nan da sati biyu, da taimakon Abban su Sadeeq dukda sunyi mmkin Karin auren nasa saidai Basu ce komai ba domin Basu San dalilin sa ba, yasa aka Kai kudin aure da kayan lefe akwati 12 Wannan Hajian su Sadeeq ta hada taso yin na Fadar kishiya wato Meera yace basai ta siyo ba Dan ya riga yakai mata a tashi karyar, a takaice dai kafin sati biyu har ankai komai na biki, biki aka shirya bana wasa ba, har kawo yau daya rage 3days a daura auren, Numfashi Dr. Omar Yaja Bayan ya Gama duk Wannan tunanin ya mike zaune Jin Kiran Sallah da ake yasa shi shigewa toilet Dan yin Alwala.
Chapter 84 · 0% Book details