← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 128

Sashe 76

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yace okay, Nan ya bawa wasu 'yan sanda umarnin su fito daga inda suka lafe, daidai lkcn Faisal ya rike Kan motar Yara biyun dake baya da suka shiga rudani Ada ganin motar ta tsaya yasa suka zaro guns dinsu a take suka fara harba wuta Kota Ina, Prof Aliyu daya ga hakan sai hankalin sa ya tashi Yana kokarin juyawa kenan yaga wani harbi ya wuce ta saitin kirjin sa kadan ya rage ya taba Masa jiki, kaucewa yyi cikin azama yaga sun Kara harbo Masa wani anan ya shige mota da sauri Yana kallon su ta mirror sai a lkcn ya fahimci ashe yaran Sageer ne, hankalin sa ne yyi mummunan tashi ya dauko wayarsa Yana kokarin Kira yaga motar 'yan sanda ta iso, a lkcn yaran Sageer din suka daina harbi, da hanzarin su 'yan sandan suka fito daga mota suna furta You're under arrest, Faisal ne ya fito a motar Yana nufar 'yan sandan yace Kunga bama bukatar ku Bata Mana lkci nawa kuke so mu Baku ki tafi? Da mmki 'yan sandan sukace Kai me kke nufi? Faisal yace kudi Mana nasan shine toshiyar ku, Wani daga cikinsu yace Amma kaikam baka da hankali wato so kke muci amanar kasar mu? Faisal yace Kai kunsan waye a cikin motar can kuwa? Sageer ne fa babban yaron me kudin Nan da kowa yasan dashi a fadin Nigeria gwara ku rufawa kanku Asiri ku Fadi Abinda kukeso ku bamu waje ko Kuma muje can gun manyan naku ai su sunsan harkar da alama kukam baku Dade da fitowa daga training ba, Dan Ayau dinnan mukeson kawo karshen wancan munafikin ya nuna prof Aliyu da yyi mutuwar zaune Yana kallon su da mmki, wani irin gigitaccen Mari Faisal yaji an dauke shi dashi besan daga Ina Marin yake ba Kawai dai ya bude idonsa ya ganshi tsaye gaban wani mutum da yyi Shigar bakaken kananan kaya da facing cap hade da mask, Cikin mugun takaici faisal ya bude baki zaiyi mgn yaji an sake wanke shi da Mari take yyi shiru Yana muzurai, Dr. Omar dake kallon su Sadeeq da shima ya badda Kama cikin kayan 'yan sanda yyi Masa Alama da ido akan a debe su, Nan kuwa aka kwashe su Bayan an gama Shaka musu hodar bcci aka nufi can wata unguwar dasu, Dr. Omar kuwa gaban prof Aliyu ya Isa, Lkcn dayaje prof Aliyu ya fito Yana fadin Gsky ban taba haduwa da babban Dan sanda Kuma Dan Nigeria dayasan Kan aikin sa ba sama dakai yallabai, dan murmushi Dr. Omar yyi har yanzu be cire mask dinsa ba yace Abinda nakeso dakai shine ka saki jikinka ka manta da komai kamar Babu Abinda ya faru dakai anan zanji da komai a hannun na, prof Aliyu yace Dan Allah ko zan iya sanin sunan ka? Girgiza Kai Dr. Omar yyi yace I'm sorry But na maka Alqawari wata rana zaka sani, girgiza Kai Prof yyi yace Alright, I wish you all the best, Thanks Dr. Omar ya furta kafin yyi Masa sallama. Farkawa Sageer yyi ya ganshi a wani dakin shi kadai ba kowa an rufe ga hannun sa anyi dressing wajen har an cire bullet din da aka harbe shi, cikin tsananin takaici ya ware murya sosai yace Wai uban waye ya kawo ni Nan? Ko rufe bakinsa beyi ba yaga mutane sun shigo da abin duka a hannun su, Sageer yace Kai uban me nake anan? Suwaye ku? Yyi mgnr ransa a bace, basuyi masa mgn ba Kawai suka hau dukansa Kota ita, kururuwa Sageer ya fara Yana zaginsu da dura musu ashar yace indai akan Wannan prof Aliyu ne saina kashe shi bazan fasa kuduri na ba, Basu fasa fasa Masa jiki ba Saida yyi laushi, Saida yyi shiru kafin daya daga cikinsu yace zaka Kara bibiyar Rayuwar Prof Aliyu ko kuwa kanaso mu dauki duk wani record naka mu kaiwa mahaifin ka? Da sauri Sageer ya dago kansa a mugun tsorace yasan duk Wannan mugayen halin da yake daddy be sani ba yanzu idan aka sanar Masa Abinda yake a skul yasan ba karamin hukunci zai fuskanta ba Dan Haka ya girgiza Kai yace lalle ma prof dinnan wato tsabar bakin Hali daga zuwan nasa har ya San ya tattara duk wani record da zai iya kaiwa mahaifina? Wanda yyi mgnr ne yace Toh kana mmkine? Ko ka dauka boyayyen gidan ka da kke masha'a ba'asan dashi ba? Kasan kuwa ba karamin sani yyi maka ba, kallon su Sageer yake yace shikenan naji ya Furta hakan cikin takaici, okay Bari mu sanar da ogan mu yadda akayi suka Fadi hakan suna kokarin rufe shi yace waye ogan naku? Ku hadani dashi Mana, Lekowa dayan yyi yace sbd kana takamar kanada kudin da zaka siye shi dashi Koh? Toh gwara ma ka yadda makaman yakin ka Dan wannnan na musamman ne ba kowa ke ganin sa b yafi karfin tunanin ka ya karasa mgnr Yana jawo kofar da sauri, fitowa parlo sukayi Nan suka tarad da Dr. Omar ya Dora daya Kan daya a parlo Yana sauraron zuwan su, yyinda Sadeeq ke gefe Yana waya cikin risinawa sukace yallabai duk Abinda ka samu muyi munyi shi daga karshe ya amince da bazai Kara bibiyar Rayuwar Prof ba, cije lips Dr. Omar yyi Yana kallon Sadeeq daya Gama Waya yanzu ya Mika masa hannu Alamar ya bashi paper gabansa, Miko Masa Sadeeq yyi shi Kuma Omar din ya Mika musu yace ku bashi yyi signing a kasa shine zai tabbatar da Abinda yace, karba sukayi cikin girmamawa suka koma wajen Sageer, lkcn da sukaje sai cika yake Yana batsewa suka Mika Masa takardar hannun su sukace gashi Nan yace kayi signing anan Dan Tabbatar da Abinda kace, karba Sageer yyi yahau dubawa kafin yyi signing din da murmushi yace Wai ku nufinku Nan Akan Wannan takardar sai ya hanani Abinda nayi niyya? Wani daga cikinsu ne shima yyi murmushin yace ai tunda kasa hannu zance ya Kare Wannan da kke gani itace takardar da za'a mikawa mahaifin ka ita Kuma ka sani a duk lkcn da kukayi yunkurin bibiyar Rayuwar prof a lkcn idon mu na kanku, a maimakon ka ganmu a wajen saidai kaga idon mahaifin ka a wajen ya ganewa kansa irin mugayen lefikan da dansa yake Yi, Ko kadan Sageer beyi zaton rufta shi sukai ba take hankalin sa yyi mugun tashi cikin tsananin takaici ya kaiwa dayan hannun sa naushi Yana muzurai sudai anan suka barshi suka nufi wajen Dr. Omar, kallon takardar Dr. Omar yyi Yana juyata kfin yace Suma yaran a aje a fito dasu, Nan aka tiso keyar su Faisal da aka kulle a wani daki, Haka shima Sageer din aka tiso keyar sa lkcn har dare yyi Bayan sallar Isha duhu ya Shiga sosai hakan yasa Basu gane yanayin gidan ba har suka Gama fitowa, Koda suka fito ma rufe musu Ido akai da kyalle da Kuma hannayen su da aka daure Babu damar su fahimci inda suke har suka bar unguwar gaba1, Saida aka shigo gari dasu kafin aka watsar su can wata gefen wata unguwar Bayan an bude musu Ido sannan wa'annan 'yan sanda suka bawa tasu motar wuta Dan barin wajen. Meera na parlo har yanzu sai duba agogo take Bata ga Alamar zuwan Dr. Omar ba gaba1 hankalin ta ya tashi gashi batasan me zata cewa Abba ba Dan tun dazu yake zuba idon ganin Omar din be gansa ba, daga yanayin yadda yake kallon ta idan ta leko waje yanason Jin Karin bayani ne ita Kuma Taki Karasawa wajen sbd batasan me zata ce ba, a Haka harya shige dakinsa sbd yadda duhun dare yyi, tana cikin safa da marwa kenan taji Alamar budewar kofa a hankali, juyowa tayi a razane sai Kuma taga Ashe Omar ne, da mmki ya bita da kallo saidai beyi Mata mgn ba ya wuce sama da sauri, kallon kofar tayi taje ta datse da sauri kafin ta bishi saman itama, gaba1 ta manta da wani Abu waishi knocking tana zuwa ta tura kofar a rude tanason Jin lpyr sa, Daidai lkcn Dr. Omar ya cire rigar jikinsa ya rage daga shi sai gajeran wando dama tuni ya zare dogon wandon dake jikinsa, take faffadan kirjin sa ya bayyana kirarrar sa ta mazan taka ta fito, Wani irin mutuwar tsaye Meera tayi bakinta a hangame ita Bata karasa cikin ba ita Kuma Bata koma waje ba.
Chapter 76 · 0% Book details