← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 128

Sashe 56

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu tasa ta share hawayen nata, kafin ta nufi kitchen duba ledojin data Debo a boot dinsa take Nan ta samu duk wani Abinda take bukata, fiddo komai tayi ta jerasu kafin ta matsar da wani gefe Dan kada ta batawa kanta lkci, Saida ta wanke gandar sosai kafin ta kunna gas ta Dora ta a tukunya cokali ta samu ta jefa a ciki tana fatan ace yyi sauri kamar yadda akaeso daga Nan ta samu doyarta ta fara ferawa. Acan bangaren Dr. Omar kuwa tsurawa sabon dakin nasa Ido yyi komai yyi kyau yadda yakeso gashi tiles din dakin sai kyalli yake kamar Wanda aka lashe, tunda ya shigo gidan dazu yake mmkin yadda tayi gyaran be zaci zata iya duk Abinda ya Sata ba, tabe baki yyi ya fara rage kayan jikin sa kafin ya bude toilet Nan ma abin ya birgeshi yadda yaga komai fari kall kamar Wanda za'a kwanta ciki, sauke ajiyar zuciya yyi ya sakar ma kansa ruwa Bayan ya turo kofar, Koda ya fito ya Gama Shirin sa tsaf dan yazo da wasu kayan gidan, Waje ya fito sbd dab ake da Akira Sallah Kuma yanaso yaje yaga Abba kafin yyi Masa sallama ya dawo, lkcn daya sakko daga sama Meera Bata sani ba Dan tana can kitchen ta kure wutar gas sai aiki take Dan har ta Gama ma firar doyar yanzu gyaran kayan Miya take kafin tazo ta fara dakan sakwara, Kota kanta bebi ba ya rufe parlon yyi waje, yanzu Kam motar sa ya dauka Dan yanaso yyi sauri, Kafin wani lkci har yaje can unguwar su, lkcn daya iso Ana Shirin Shiga Sallah dake Already yyi Alwalar sa Dan Haka kawai shima ya shige masallaci akayi dashi, Bayan ya idar ne Yana fitowa yaji an riko hannun sa, juyowa yyi yaga Abba ne Ashe, murmushi yyi Masa sannan suka karasa fitowa waje, Maimakon suyi cikin gidan sai Dr. Omar ya Kama hannun sa sukayi wajen motar sa, har suka Isa wajen motar Dr. Omar bece komai ba Saida ya bude motar yyiwa Abba Alamar ya Shiga, kallon sa Abba yyi d mmki Yana jiran Karin bayani, Dan murmushi Dr. Omar ya sake Yi kafin yace, "Abba shiga daga ciki muyi mgn" Jin hakan yasa Abba ya Shiga Dan yasan mgnr Tanada muhimmancin kenan, Shiga sukayi Dr. Omar ya rufe shima ya Shiga dayan side din ya rufe, tada motar yyi suka bar bangaren unguwar su, can saman layinsu suka koma inda ba mutane sosai Dr. Omar yyi parking Yana duban Abba da tun dazu mmkin Omar din yake ba bakin mgn bare yace wani Abu, Bayan ya daidaita parking dinne Dr. Omar ya dubi Abba sosai yace, "Abba" girgiza Kai Abba yyi Alamar yanajin sa, Dan Numfashi kadan Dr. Omar Yaja kafin yace, "nayi maka lefi domin na boye maka wani muhimmin Abu daya faru Dani ko nace yake faruwa Dani" hankali a matukar tashe Abba ya zaro Ido bakinsa na rawa so yake yyi mgn ya kasa, kallon sa Dr. Omar yyi da tausayi kafin yace, "kwantar da hankalin ka Abba ba wani Abu bane" yyi mgnr Yana rike Masa hannu, sauke ajiyar zuciya Abba yyi kafin ya zuba Masa ido Alamar Yana sauraren sa, Lumshe ido Dr. Omar yyi yanajin zafin ya Furta cewa an koreshi a skul, yanajin takaicin idan ya tuna yadda aka wargaza Masa mafarkin sa, to Amma ya zaiyi? Tasa kaddarar kenan, bude idonsa yyi lkcn harsun fara kadawa daga launin fari zuwa ja Yana Dan daidaita nutsuwar sa hade da kawar d fuskar sa gefe Dan bayason Abba ya fahimci irin bacin ran d yake ciki muryar sa can kasan makoshi yace, "an Dade da korata a skul" A rude Abba ya rike hannun sa Yana jijjigawa kamar zai fashe da kuka sai kakarin mgn yake abin yaci tura yau Kuma wanne irin babban tashin hankali ne ya sake kunno musu? Me Omar yyi Haka da makaranta ta koreshi? Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Abinda Abba yyita lissafawa a ransa kenan duk ya rikice ya rude gashi ba damar mgn, cije lips dinsa Dr. Omar yyi yana me Kara saisaita bacin ransa ya juyo sosai ya kalli Abba, a hankali ya fara zayyane Masa komai saidai ko kadan be sako sunan Ameera a ciki ba, be sanar Masa matakin daya dauka Akan Ameera ba, Yadai ce an Masa sharri ne silar wata Mace, tunda ya fara mgnr hawaye ke zuba Kan fuskar Abba, ba karamin tashin hankali mgnr Dr. Omar din ta jefa shi ba, tsananin tausayin Omar dinne yake Masa kawanya a zuciya, tunda yake mgn yasan cewa anyi aiki da kudi ne wajen Bata Masa suna, ya fahimci anyi Masa fin karfi ne da dukiya, Girgiza Kai yake Yana Kara Jin takaicin Rashin mgnr sa gani yake duk lefinsa ne da tun wuri daya Kira Omar a waya be sanar dashi Abinda ke faruwa ba da tabbas Babu Dan iskan daya Isa ya nunawa yaron Nan dukiya, mutum da gatan sa an maida shi marar Gata.., katse Masa tunani Omar yyi lkcn dayasa tattausan hannun sa Yana share Masa hawayen da suke zuba tun dazu, cikin danne nasa bacin ran ya dubi Abban da murmushin yake yace, "shiyasa tun farko ban sanar maka ba sbd nasan zaka damu, Kuma abune me wahala ka fitar dashi a ranka, Dan Haka ka saurara kaji dayan lbrin" zuba Masa ido kurum Abba yyi yanajin wani iri a ransa, Nan Dr. Omar ya sanar Masa haduwar sa da daddy da Kuma Matsayin sa yanzu a company din hatta gidan da aka bashi duk ya sanar Masa, yanzu Kam Abba murmushi yake sosai sbd dadin daya Kama shi, lalle Dr. Omar kashin arziki ne dashi duk yadda Saratu taso taga ya zama abin tausayi Allah be Bata Wannan damar ba, sosai ya kamu da farinciki har ya kasa boye murnar sa dukda can kasan zuciyar sa yana tsananin tausayin Omar din domin shi shaida ne akan yadda Omar yake d burin ya zama likita, Dan kallon shi Dr. Omar yyi ya danyi murmushi shima kafin yace, "wa'annan Abu biyun sune suka sameni batare da duk kasan halin d nake ciki ba" Kama hannun sa Abba yyi Yana me girgiza kansa a ransa Fadi yake ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....Omar, acan makaranta anyi maka sharri sai Allah ya dubeka, Allah yaci gaba da kareka Akan makiyan ka, Allah ya baka ikon cin nasara a kansu a kowanne yanayi, murmushi Dr. Omar yyi Dan Shidai besan me Abban ke Fadi a ransa ba Yadai ga Yana matsa Masa hannu, Saida suka Dan Jima sosai kafin suka bar wajen, a hanya ya saiwa Abba kaza da kayan marmari nasa daban Haka ma dai ya saiwa Saratu da Sahabatu. Lkcn da suka shigo gidan Saratu na waje tayi zuru2 hankalin ta a tashe tasa Sahabatu a gaba tana Mata mgn ta shareta, shigowar su yasa ta gyara zamanta bataso su fahimci halin da ake ciki, ganin su tare yasa ta tabe baki batace komai ba, har gabanta Dr. Omar yazo yyi Mata barka da gida, amsawa tayi dakyar tana kawar da Kai, kallon Sahabatu data tsurawa Ledar hannun sa Ido yyi, Mika Mata Ledar yyi beyi mgn ba, kamar kuwa yasan maikon data hango ne take kallo ai kuwa kamar ta fusge masa hannu Haka ta karbe tana budewa da sauri jikinta na rawa, a razane Saratu ta juyo tana kallon ta kardai Abinda take tunani ne ya zama gsky? Dan tun jiya take binta ta sanar Mata Abinda ke damunta tayi shiru, bude baki tayi zatayi mgn kenan Taga Har yanzu Dr. Omar Yana tsaye agun Yana kallon ta, Dan daidaita nutsuwar ta tayi kafin ta Harare shi tace, "toh Kuma tsayuwar me kke har yanzu? Kabi ka zuba Mata Ido kamar yau ka fara kallon ta" bin Saratu da kallo Dr. Omar yyi kafin yace, "ummah bakya ganin kamar Bata da lpy Kuma tana Jin jiki?" Matsawa jikin Sahabatu da tun dazu ta yaga leda take fisgar Naman kaza tayi tana tareta tace, "toh Ina ruwanka? Koh Dan kana karantar lpy sai akace Zan barka ka dubamin 'ya?" Da mmki ya kalli Saratu zaiyi mgn kenan ta katse shi tana me daga Masa hannu tace, "kaga ni Dan Allah ya Isa, dama ance Likita Maye ne toh Dan Allah matsa daga gefen mu karka hango Mata 'ya'yan hanji" tabe baki Dr. Omar yyi Yana me dage kafadar sa kafin ya juya yabar musu wajen, Abba kuwa dakinsa dama ya shige Dan tun farkon zazzabin Sahabatu ya fara hangen Abinda ke damunta musamman dashi ne ke zaune a gidan Yana ganin yadda take kwararar amai, Shima Dr. Omar daki ya shige Nan ya fara tattara duk wani Abu nasa me amfani a dakin yasa a wata 'yar karamar jaka, Lkcn daya Gama tattare komai anyi Kiran Isha hakan yasa ya fito a daki Dan zuwa yin Sallah, tare suka jera da Abba har zuwa masallacin Bayan sun fito ma sun Dade a waje Dr. Omar na yiwa Abba Hira, kafin suka shigo gidan sbd Abba na ta nuna agogon hannun Omar din Alamar yaje gida tunda ya sanar Masa yau za'a Kai Masa amaryar, Ba yadda Omar ya iya Haka suka shigo duk so yake yyi Masa mgnr Sahabatu Amma ya kasa bayason Kuma ya Kara tadawa da Abba wani hankalin besan Abba tuni ya Dade da hasashen Abinda yake nufi ba, Bayan ya dauko jakarsa a daki ne ya rufe ya Isa gaban Saratu data fada duniyar tunani Dan batasan sun shigo ba, "Ummah," Dr. Omar ya kirata da Dan karfi sbd yanata Mata mgn Bata Amsa ba, a firgice ta dago kanta tana ganin shine taja tsaki, Har cikin ransa yaji tsakin Dan shi mutum ne daya tsani aja Masa tsaki, fuskar sa Adan hade yace, "sallama zanyi Miki na tafi" kallon sa tayi cikin takaici tace, "Toh daka Zo kana min sallama so kke na rakaka wajen shegiyar matar taka?" Rai ya hade sosai yace, "Ummah?" Juya Masa keya tayi Dan ba karamin haushin sa takeji ba sbd yadda taga duk yaranta biyu sun lalace shi Kuma gashi Nan digirgir a nutse kamar Wanda aka jika aka bashi yasha, a tunzure tace, "au har ka
Chapter 56 · 0% Book details