← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 128

Sashe 91

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mata Kuma?" Dan kawar da kansa Omar yyi zuciyar sa na bugawa, Sadeeq yace, "saidai ka nemi wani ya rakaka Amma badai ni ba kaga tafiyata" yyi mgnr Yana barin motar, da sauri Omar ya fito daga dayan side din Yana nufar inda Sadeeq yake yace, "wanne irin wulakanci ne Wannan Ina maka mgnr matata ta tafi kana gayamin bazakaje ba?" Kama haba Sadeeq yyi Yana kallon sa up and down yace, "idan ban manta ba fa Kai ango ne, Toh kaje kaji da salmar taka man" takaici ne ya sake Kama Omar yanajin Kamar ya kifama Sadeeq Mari yace, "kaifa Dan rainin hankali ne Sadeeq ni da'allah shige mota muje" zube hannayen sa a cikin Aljihu Sadeeq yyi yace, "Toh baba" ya Fadi hakan Yana kallon sa, Dogon tsaki Omar Yaja ya lura idan ya biye Sadeeq sai ayi azahar Basu daina mgn ba hakan yasa shi saukowa ya matso kusa da Sadeeq din Yana dafa kafadar sa yace, "Please and Please Sadeeq na rokeka da girman Allah ka rakani gidansu Meera bakasan irin tashin hankalin da nake ciki bane yau" kallon tsanaki Sadeeq ya Masa kafin shima cikin nutsuwa yace, "meya kawo Wannan sauyawar taka da wuri Haka Omar? A iya sanina dai bakason Meera Banda masaniyar tafiyar ta Amma Ina kyautata zaton murdadden Halinka ne yasa tabar maka gida ko Kuma tun a Daren jiya ka fara Rashin adalci tsakanin ta da Zabin ranka wato Salma" girgiza Kai Omar yake yanajin zuciyar sa na tafarfasa gsky badan akan Meera bane bazai ci gaba da tsayuwa Sadeeq na Yaba Masa mgn ba Dan ya fahimce shi Sarai Abinda ya faru ne baya yake dawo Masa dashi Dan ya gane kuskuren sa, Saida ya dauki wasu seconds kafin ya dubi Sadeeq yace, "da ace kasan Matsalar da nake ciki a yau da baka tsaya ja min aji ba Sadeeq, Abinda na sani shine tafiyar ta a yanzu tafi komai daga min hankali sama da Abinda na baro a baya sbd nasan Wannan idan na koma zan ganshi a takaice ma ni ake jira Wannan kuwa bulayi nake cikin duhu don bansan gidansu ba" ya karasa mgnr da damuwa Sadeeq yace, "Kai kuwa meye ya faru dakai yau naji kana mgnr Bayan matsalar Meera akwai wata?" Kawar da Kai Omar yyi kafin yace, bazaka gane ba Sadeeq na fiso na kashe gobarar dake gabana kafin na sanar dakai Abinda ake ciki" kallon time Sadeeq yyi 11:30 yace, "shikenan muje" wata irin ajiyar zuciya Omar ya saki harta Kai Dr. Sadeeq din ya kalleshi da sauri yanzun Kam ya lura lamarin Omar din babbane, Omar na kokarin shiga wajen driving Sadeeq yyi saurin zuwa wajen yace, "kaga kawo nayi driving bazan yadda na Shiga motar Nan yadda kke a gigicen Nan ba" wurga Masa key din motar Omar yyi shi sauki ma ya samu Dan Haka ya zaga dayan side din ya shiga, sun Fara tafiya a mota kenan Dr. Sadeeq yace, "so finally ka amince Meera a Matsayin matar ka?" Omar da yaji mgnr tamkar daga sama ya juyo da sauri Yana kallon Sadeeq dake 'yar dariya hade fuska yyi yace, "seriously kanada matsala" kallon sa Sadeeq yyi yace, "kodai Kai keda matsala? Gaba1 ka gigice Kan Meera Kai kace ba itadin Nan bace wacce ka Gama aibanta ta ba kana fadin bakaso auren fansa kayi" tsaki Dr. Omar yyi Yana kawar dakai Dan ya lura Sadeeq tsokana yakeji shi Kuma burinsa ace yaga Meera duk tausayin ta ma yake musamman idan ya tuno da yadda ya Gama Tara mata gajiya jiya sai yaji kamar yyi tsuntsuwa ya Isa gareta ko ya samu ya taimaka mata, Da Haka suka Isa unguwar su Meera har Sadeeq yyi parking daidai kofar gate dinsu, ba karamin mmki ne ya Kama Dr. Omar ba daya ga tsari da yanayin gidansu Meera be taba kawowa hakan a ransa ba especially dayasan bataje da wadatattun kaya ba Amma duba da yanayin gidan nasu ya Tabbatar Masa da tafi karfin kodaddun kayan da take sawa Nan ya sake dulmiya duniyar tunani tabbas Rayuwar Meera abin asa Mata alamar tmby ne, mlm Ayuba na saita radio dinsa yaga mazaze biyu sun nufo inda yake aje radio din yyi Yana kallon su har suka karaso wajensa da sallama Mika musu hannu yyi sukayi musabaha da fara'ar sa yace, "sannun ku fah ga waje ku zauna" ya nuna musu Kan dogon bencin dake gabansa, Dr. Sadeeq ne yace, "ah baba akan hanya muke Dan Allah Koh zakayi Mana sallama dame gidan?" Ya karashe mgnr da sigar tmby, "Tabdin" mlm Ayuba ya Furta hakan Yana Kama haba, hakan yasa Dr. Omar ya dubeshi da sauri Yana son sanin meyasa ya Furta hakan, Sadeeq ne ya katse shirun da Fadin "lpy dai Koh?" Mlm Ayuba yace, "kawai Ina jimamin Rashin sa'ar ku ne wllhi" "Kamar ya Rashin sa'a?" Sadeeq ya tmby da mmki shikuwa Dr. Omar bugawar kirjinsa ne ta karu, mlm Ayuba yace, "dazu dazun Nan yabar gidan Nan" sauke ajiyar zuciya sukayi kafin Dr. Omar ya tsoma baki wajen Furta, "ah Toh.. shikenan saimu jirashi Koh idan da dama kace Ana mgn da Ameera" kallon sa sosai mlm Ayuba yyi Yana girgiza Kai yace, "Ashsha...." a Dan tsorace yace, "lpy?" Mlm Ayuba yace, "ai dashi da 'yar tasa suka fice" dafe Kai Dr. Omar yyi cikin matukar tashin hankali bako shakka yasan Ameera hsptl aka kaita duba da yadda yasan yabarta a gida kafin yaje masallaci..., Dafa shi Dr. Sadeeq yyi hakan ya sashi cire hannun sa daga goshi idonsa ya fara kadawa ya dubi mlm Ayuba daya sasu gaba yake kallon su da mmki murya can kasan makoshi Yana Jin nauyin tmbyr da zaiyi yace, "Koh sun fada maka Asibitin da suka tafi?" A tare mlm Ayuba da Sadeeq suka Furta cewa, "Asbiti???" Kawar da kansa yyi da sauri zuciyar sa itama na harbawa da sauri, Dr. Sadeeq ne ya riko hannun sa Yana jijjigawa yace, "ka fadamin Omar kodai akwai Abinda kke boyemin ne?" Shiru Dr. Omar ya Masa Dan bayason mgn yanzu sai yaji daga mlm Ayuba, mlm Ayuba kuwa da mmki ya cikashi yace, "a zahirin gsky Bari na takaice muku zance sunbar garin nan..." A gigice Omar yace, "sun bar gari Kuma?" Mlm Ayuba yace, "kwarai kuwa Dan yanzu Haka ma idan Basu tashi daga jirgi bama Toh suna Shirin tashi Dan shabiyun Rana jirginsu zai tashi zuwa Adamawa..." Wani irin jiri ne ya Kama Dr. Omar bakinsa na rawa yake furta Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, a rude Sadeeq ya Kama shi sbd yaga Yana Shirin faduwa shi kansa ya girgiza da tafiyar Meera dukda besan meya hadasu da Omar din ba, da taimakon Allah Sadeeq ya samu Omar din ya zauna kan bencin da akayi musu tayi dazu, shima Zama yyi Yana rike dashi Dr. Omar gaba1 hankalin sa ne ya dugunzuma idonsa ya sake rinewa sbd tashin hankali Saida yaji hajijiyar ta daina yawo dashi kafin ya mike zumbur Yana kallon mlm Ayuba yace, "Dan Allah ka bani Address din gidansu na Adamawa inason na bisu can" da mugun mmki Sadeeq yace, "are you out of your sense Omar? Wai me kke Shirin Yi ne Kam? Please ka nutsu muyi komai a hankali Mana" wata irin muguwar hararar da Sadeeq be zaceta ba yaga Dr. Omar ya wurgesa da ita hakan yasa Dr. Sadeeq yadan ja baya kadan, mlm Ayuba kuwa dayaga Abinda yafi karfinsa ya Mike da sauri yace, "Bari naje na duba inda na aje" suna tsaye ya fito daga cikin dakinsa na me gadi Yana fadin, "Dan Allah kuyi hakuri na Rasa inda na jefa takardar" A rikice Dr. Omar yace, "haba baba Adireshin gidan nace ka fadamin bawai ka rubuta a takarda ba" yyi Masa mgnr gwari2 yadda zai fahimta, mlm Ayuba yace, "toh ai Nima ba sani nayi ba dazun Nan kafin ya tafi ya bani na aje sbd masu neman sa Wlh na manta inda na jefa" sake dafe kansa Dr. Omar yyi jikinsa na rawa Sadeeq ya jawo hannun sa Yana fadin, "Omar ya kamata ka nutsu kafin a samu mafitar da zamu samo Address dinnan" mlm Ayuba yace, "Insha Allahu zan dubota nasan ba nisa tayi ba Kawai na manta inda na sa ne Kuma fa dazun Nan ya bani" haushi ne ya Kama Omar yanaji Kamar ya make mlm Ayuba badan son ransa bama ya juya Suka shige mota zuciyar sa na Kuna, dubansa Sadeeq yyi a hankali yace, "Don't worry frnd ko Anjima Zan dawo naji ko yaga takardar" Cije lips Omar yyi gaba1 baya cikin nutsuwar sa kafin yace komai yaji wayarsa na ringing sunan Alhaji Abdullahi ne yake yawo Akan screen dinsa, hakan ya sashi dagawa da sauri Yana saita nutsuwar sa Alhaji Abdullahi yace, "Omar ya Kan naka hope dai yyi sauki?" Girgiza Kai Omar yyi kamar Yana gabansa kafin dakyar yace, "eh" karar iskar motace yasa Alhji Abdullahi fadin, "ko ka fita ne?" Omar yace, "eh daddy wani uzuri ne ya taso min" daddy yace, "Alright dama zance maka ka hutar da surukar tamu yau dai dukanmu tare zamuyi lunch" ya Furta hakan Yana murmushi, wani irin bugawa kirjin sa yyi tashin hankalin sa ya karu fiye dana dazu ya kasa furtawa daddy komai bare ya bashi Amsa, shi kuwa daddy be kula da shirun nasa bama yaci gaba da fadin, "sai kunzo" ya karashe mgnr Yana kashe wayar, "Hasbunallahi wani'imal wakil" Dr. Omar ya Furta hakan cikin dimuwa da tashin hankali yane me dafe kansa, kallon sa da sauri Dr. Sadeeq yyi shifa Wannan birkicewa ta Omar ta fara bashi tsoro mutum sai kace me Aljanu, Kai tsaye yace, "Omar Wai lpy kuwa?" Dagowa Omar yyi cikin matukar damuwa yace, "daddy ya sani zuwa da Meera gidansa" "daddy Kuma? Waye hakan?" Dr. Sadeeq ya Furta hakan da mmki Dan shi besan Yana kiransa da daddy ba sai Alhaji Abdullahi, wara Ido Dr. Omar yyi sai yanzu ya tuna gaba1 be yiwa Dr. Sadeeq bayanin Abinda ke faruwa ba, dafe goshinsa yyi yace, "gaba1 kainane ya kulle sorry frnd" Sadeeq yace, "da akayi me?" Nan Dr. Omar ya gyara nutsuwar sa Yana bashi lbrn Rayuwar sa....... da take boye wato rabashi da Asalin iyayen sa da akayi. Acan bangaren
Chapter 91 · 0% Book details