← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 128

Sashe 47

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

cewa komai Dr. Sadeeq din yyi shiyasa yanaji Yana gani ya yanke wayar, dafe goshin sa yyi Yana Kara Jin tausayin Omar din dukda yasan zuwa yanzu Kam Omar ba abin tausayi bane Allah ya daga darajar sa. Shikuwa Dr. Omar Aljihu ya maida wayar Yana me bude dakinsa ya fito, lkcn daya fito Saratu harta bar gidan sai Sahabatu yau da Bata fita ba tana kwance lamo a barandar su, Dan kallon ta yyi a kaikaice kamar zai wuce sai Kuma ya fasa da mmki yake binta d kallo yasan dai tunda yarinyar Nan ta budi Ido a sana'a Bata cika zaman gida ba sai zaman Tasha Ana Saida abinci Idan ta dawo gida kuwa wani abincin zatayi Koh bcci, yau kuwa tunda aka ganta a gida har Wannan lkcn da dalili, matsawa yyi jikin rumfar yace, "ke lpy?" Yyi mgnr fuskar sa a hade, Banza tayi Masa batayi mgn ba, ransa ne ya baci sosai cikin tsawa yace, "ke ba mgn nake Miki ba?" Dagowa tayi ta kalleshi cikin tsiwa tace, "Wai ba Ummah ta Hana kamin mgn ba?" Kallon ta yyi shaye da mmki zaiyi mgn kenan yaji an kamo hannun sa ta baya juyowa yyi yaga Abba daga Masa hannu yyi Alamar ya kyaleta, sake juyawa Dr. Omar yyi still mmki bebar shi ba, sai Kare Mata kallo yake, ganin irin kallon da yake binta dashi yasa Sahabatu tayi saurin kauda idonta gefe tana juya musu baya. Sai a lkcn Omar ya kalli Abba, Dan risinawa yyi yace, "barka da safiya Abba da fatan ka tashi lpy" Girgiza Kai Abba yyi Yana murmushi, Dan murmushin Omar yyi kafin yace, "toh zamu fita asa Mana Albarka" kallon mmki Abba yyi Masa a ranar auren ma sai anje aiki? cikin sauri Dr. Omar ya katse Abba Dan ya fahimci inda Abba ya dosa Dan Haka yace, "exam zamuyi Dan Haka ba wani dadewa zamuyi ba asa Mana Albarka" Dan murmushi Abba yyi Yana girgiza Masa kansa, anan dai yyiwa Abba sallama ya tafi. Saida ya fito bakin titi kafin ya tare me napep hade dayi Masa kwatancen gidan sa Dan acan ma motar sa take. Bayan me napep ya sauke shi ne ya bude gate din gidan, shigowa yyi Yana karewa gidan kallo kamar yau ya fara Shiga, da mmki yake kallon can jikin kofar parlo mutum a kwance an rufe har Kai, Dafe goshin sa yyi sbd tunowa da Meera an kawo ta jiya take haushinta ya dawo Masa, da saurin sa ya Isa Kan barandar ya Rasa dame zai tasheta kawai yasa kafa ya shureta, a figirce Meera ta tashi tana waige2 zaton ma Koh karnukan ne suka hauro gidan, Kanta na kasa ta fara bin sawun takalmin data gani tsaye a gabanta da kallo, a hankali take binsa da kallo tun daga kasa har izuwa can sama, ja baya tayi da sauri tana binsa da kallon mmki, Hade ransa yyi sosai fuskar sa Babu Alamar fara'a a tattare dashi, Wani irin bugawa kirjin Meera yyi sbd yadda taga Yana binta da wani irin matsiyacin kallo, bakinta na rawa Tace, "sa.s..sannu da zuwa barka da safiya" ta Fadi hakan a jere, cikin tsawa yace, "sbd samun waje irin naki har kikai Wannan lkcn kina bcci? Wacce irin malalaciya ce ke?" Darammm, kirjin Meera ya sake bugawa da karfi, hakan yasa ta Mike tsaye tana ja da baya tace, "kodai baka gane ni bane? Ameera ce fah wacce ka Aureta Jiya" wani irin kallon banza yyi Mata Yana sake matsowa inda take yace, "aure?" Girgiza Kai Meera tayi tana kallon sa, Dan ja da baya yyi Yana meyin wani irin tattaki kafin ya dago ya kalleta yace, kinyiwa abin gurguwar fahimta" a tsorace Meera tace, "me kke nufi?" Dr. Omar yace, "me kuwa nake nufi? Dake duk a tunanin ki sai ki Sami namji kamar ni ya aureki? Tatsitsiya dake na aureki ko na Raine ki???" Ya Furta hakan Yana wara Mata manyan idanun sa kanta, zaro nata manyan idanun tayi tana dubansa da mugun mmki, Ci gaba da mgn yyi yace, Koda yake, yes Aurenki nayi Amma bawai irin auren da Kika Saba ji anayi ba, Kai tsaye Zaki iya Kiran auren da auren daukar fansa" zaro ido sosai Meera tayi tace, "me nayi maka da zaka dauki fansa a Kaina?" Ta Fadi hakan bakinta na rawa, "Me kikayi min kike tmby?" Ya Furta hakan da karfi har Saida Meera ta firgita da karar, kasa cewa komai tayi saima sake matsawa can gefe da tayi, Dr. Omar yace, "keda shegen munafukin naki Sageer duk saina koya muku hankali" "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" Meera ta Furta hankalin ta na tashi a rikice ta kalli Dr. Omar tace, "Wlhi ba Abinda kke tunani bane, ni Babu ruwana dashi ban sanshi ba, Dan Allah kayi hakuri nayi maka bayanin dalilin dayasa na bada shaida a kanka ranar" wani irin takaicin ta ne ya sake Kama shi, Wai yyi hakuri tayi Masa bayani? Cikin zafin Rai yace, "wannen irin bayani zakiyi min Bayan kin Gama tozarta ni a idon duniya? Me zakice min Bayan kin Gama wargaza min lissafi? Dana San taimakon ki Abinda zai jawo min kenan da tun wuri ban Kai Miki taimako ba..." Meera ce ta katse shi da fadin, "cewa fa yyi...." "Shut up.." Dr. Omar shima ya katseta da tsawa Dan bayajin zai iya tsayawa ya saurari dukkan karerayin ta, Kame bakinta Meera tayi jikinta na rawa, kallon yanayin gidan Dr. Omar yyi yace, "Kinga Nan? Ya nuna Mata farfajiyar girgiza Kai Meera tayi, yace, "Good kisa a ranki kamar Aikatau kikazo Yi gidan Nan idan d kinada hankali ma tun jiya ya kamata ki fara tunanin bakida da wata daraja a idon Wanda Kika aura, Dan Haka ki sani a kullum ta Allah inason Naga field dinnan a share Tass ko kwayar ganyen bishiya bana bukatar gani" bin farfajiyar gidan Meera tayi da kallo hankalin ta a mugun tashe ta dawo da kallon ta Kan Omar taga ya bude kofar parlo, Parlon ba lefi dadan girman sa me dauke da dakuna biyu acan sama da wasu a kasa, "Keee.." ya Furtawa Meera hakan, Meera tace, "Na'am" ta Furta a tsorace Dan ita yanzu gaba1 ma Dr. Omar din tsoro ya fara Bata, Nuna Mata sama da kasa yyi duk Kura sbd be fara using da gidan ba yace, "inaso kafin na dawo ki Tabbatar kin share kinyi mopping idan na dawo na tarar baki gyara ba Zaki fuskanci mummunan hukunci" daga Kai Meera tayi Bata Amsa ba, "Bakyaji ne?" Ya Furta hakan da tsawa a firgice Meera tace, "inaji" Tsaki Yaja me sauti yace, "Toh banason Ana Amsa min da jiki furuci nakeso Understand?" "Yes" Meera ta Furta itama, "Good Dr. Omar ya Furta Yana zube Mata keys din Kan kujera batare daya kalleta ba yace, "your time start Now matukar na dawo na samu ba yadda nace ba you will be in trouble" "Toh" Meera ta Furta, Tsaki yyi ya fice daga parlon Koh sake waiwayen ta beyi ba Yaja motarsa ya fice a gidan Bayan ya janyo gate ya rufe ta ta waje. "Hasbunallahi wani'imal wakil, A'uzubika limatullahi tammat min sharri makalaq..." Abinda Meera ta dinga Furta kenan tana maimaitawa a ranta hade da bin Dr. Omar din da kallo cikin tsoro da firgici "Yau wacce irin rayuwa nake Shirin fuskanta ni marainiyar Allah Ameera??" Ta furta hakan a fili hade da fashewa da kuka.
Chapter 47 · 0% Book details