Sashe 108
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*200 kacal ya Isa ki samu cmplt littafin Nan ta hanyar turo da ita ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆ðŸ»* 8/19/20, 9:05 AM - Ummi Tandama: Wara Masa ido tayi tana Dan hade fuska Ahmad ya saki murmushi yace, "karya nayi?" Hararar sa tayi tazo giftawa yyi azamar kamo hannun ta da sauri kuwa ta goce tana dafe kirji hakan yasa Ahmad ya zuba mata idonsa, sake banko Masa Harara tayi tana Dan saita nutsuwar ta Tace, "Ya Ahmad don't try this again" "I'm sorry" ya Furta a hankali, kwafa tayi kawai ta fice itama harsu Inna fure sun Isa gaban motar sa, Yana biye da ita a baya isarsu wajen yasa su Inna furen Suka shige bayan mota itama Kama murfin kofar tayi zata wuce yace, "ki shigo Nan Mana Meera" tamkar bataji sa ba ta bude kofar Inna fure Tace, "ki shiga can din Ameera kinji?" Girgiza Kai tayi badan taso ba ta bude gaban ta shige, tana Shiga kuwa Ahmad ya tada motar sa suka fice daga gidan Suna Hawa Kan titi kuwa Meera tasa kanta gefen window tana karewa garin Adamawa kallo, Sun zaga ko'ina da ita kowa akace Masa 'yar Aminatu Jikar hadiza wato yayar inna fure sai yyita mmki, manyansu ne dai duk Basu manta ba saidai masu hankalin suke Jin kunyar wofintar da zumunci da akayi, sun gaji matuka, a hanyar su ta komawa ne ma Ahmad yace, "zan biya daku shopping Inna" Inna fure Tace, "Kai ba Dani za'ai Wannan gantalin ba na gaji" Abinda yakeson ji kenan Dan Haka yace, "Asma'u ku shirya Anjima bayan Kun huta zamu fita" yyi mgnr Yana dauke Kai Dan karma Meera ta Musa, Inna fure ce tace, "jikinku da kwari ku zaku iya zuwa Amma Banda ni" Asma'u Tace, "saiki fada Mana Abinda kikeso mu sayo Miki" Inna fure na tabe baki Tace, "ku kuka sani Amma dai a Tabbatar jikata ta zabi son ranta" 'yar dariya Ahmad yyi yace, "Kai Inna dukanmu ma ai jikoki ne" Inna Tace, "na sani Ita meeran dai banaso kunya ta hanata daukar komai" Meera sai a lkcn tayi murmushi hakan yasa Ahmad yace, "Kinga ma dariya take Miki" Inna Tace, "atho ai tasan gsky na fada." Su Omar na cikin jirgi Sadeeq ya dubeshi yadda yake ta duba agogon hannun nasa ne yaso bashi dariya gashi dai karshen gudu a jirgi suke Amma hakan da alama be wadatar dashi ba, Dan zungurin sa yyi hakan yasa Dr. Omar ya dubeshi, Sadeeq yace, "yanzu da kkeso mu Isa wajen Nan da wuri ka tanadar wa Meera kalaman da zaka Bata hakuri?" Dan shiru Omar yyi sai yanzu ya tuna fa akwai Kura a gaba, Amma cikin mazewa yace, "it's normal nasan ta yadda zan biyo mata" gyada Kai Sadeeq yyi yace, "that's good" Basu wani Jima sosai ba kuwa sai gasu a garin Adamawa, tunda Omar ya fara taka matattakalar jirgin Nan yakejin wani irin Sanyi na dukansa lalle yazo garin Adamawa garin Fulani da nono Dangin sahibar sa Meera, a hankali ya Gama saukowa hannun sa rike da traveling bag dinsa, Sadeeq na gefensa shima da Abinda yake kallo can, Suna fitowa daga airport din Omar ya duba pocket dinsa inda ya aje address din su Meera Yana dubawa kuwa ya karance tsab Toh dama harya haddace tun ganin farko da yyima takardar saidai sbd gudun Saba lamba ya dauko ya sake dubawa, taxi suka tare wacce zata kaisu har inda suke so, Koda Omar yyima driver bayanin inda suka nufa yace ya gane wajen, tafiya suke sannu a hankali har suka fara gangarawa unguwar Alhji Kabir Dan Anan ne ma Dad ya bada Address din tun daga hanya Omar yake leken window kirjinsa na bugawa a hankali Dan besan da wacce fuska Ameera zata karbeshi ba bare Kuma ace Ahalin ta, Suna zuwa daidai katon gate din gidan Alhaji Kabir Suma daidai lkcn Ahmad ya danno tasa motar, su Omar biyan me taxi din sukayi harma ya haura kudin daya bukata ya karba kuwa da murnar sa Yana godiya, me gadinsu Ahmad ne ya bude musu gate suka wuce ciki yyinda Dr. Omar da Sadeeq suna Kara matsawa jikin gate kafin su wuce suka hango sojoji na shawagi a tsakankanin wajen, Dr. Omar da Sadeeq ne suka kalli juna a tare, shi Omar kallon mmki yake shikuwa Sadeeq kallon tsoro yake a hankali yace, "Shikenan ai Omar ka kawomu inda za'a harbe mu" Dan tsaki Omar Yaja Dan shi Bata Wannan yake ba hakan yasa ya Isa gaban soldiers din gadan2 ba tsoro ko kadan a tare dashi, gaban Wanda ya bude gate din gidan yaje Yana kokarin rufe gate din Omar yyi sallama, Dagowa yyi Yana Kare Masa kallo da gani ma kabila ne ya Amsa Masa da tasa hausar da Bata Gama isarsa ba, Bude baki Omar yyi zaiyi mgn ya hango bayan wata mace wani Namiji na bude kofa Dan already su Inna sun wuce ciki gabansa ne ya buga da karfi Yana kokarin kauda tunanin Abinda yake Dan yasan ba lalle hasashen sa ya zama gsky ba Kawai yaga Abinda idanun sa suke ta matukar son gani wato Meera na yiwa Wanda ya bude mata motar murmushi...., A rude Omar yayi hanyar Shiga ciki bakinsa na rawa yake fadin, "Meeeeraaaa...." Kamar saukar tsawa Haka Meera taji muryar da ko a mafarki taji bazata manta ba wato Omar hakan yasa ta kalli bakin gate din a firgice, soldiers din wajen ne suka taso da hanzarin su Suna tare shi Nan suka fara fadin, "Who are you?" Mika hannun sa Omar yyi Sam bebi ta kansu ba Amma Kuma sun rike shi gamgam fadi yake, "Meera pls kizo nan" Ahmad da ya Shiga mmkin Wannan Al'ajabi ya dubi Ameera da jikinta yaketa rawa yace, "waye Kuma wancan?" Kin bashi Amsa tayi kawai ta wuce cikin gidan da gudu tana kokarin danne hawayen daya taho mata, hakan yasa shima Ahmad din yabi bayanta da sauri, bangaje soldiers din Omar yyi Yana komawa baya duk sai suka zuba Masa ido, dafe kansa yyi Yana cije lips, Sadeeq ne ya kamo hannun sa a hankali yace, "haba Omar ai da saika Bari a Kira maka ita ko?" Fisge hannun sa Omar yyi ransa na zafi yace, "da aurena a kanta Naga tana yiwa wani katon murmushi ya kke tunanin zanji hakan a Raina?" Dan sauke ajiyar zuciya Sadeeq yyi Yana jansa gefe yace, "look Omar Nan ba kano bane kowa sarki ne a wajen zamansa mu bakine Omar bamu San komai Akan Wannan family din ba ya kamata ace mun biyowa abin ta sama" Tsaki Omar yyi Dan gsky har yanzu bawai ya huce bane kawai bayason ya zubar da mutuncin sa ne ya fada gidan mutane, Dan bubbuga kafadar sa Sadeeq yyi kafin yace, "Ina zuwa" wajen soldiers din ya nufa a nutse yace, "Dan Allah ko me gidan Nan yana Nan?" Daya daga cikinsu ne yace, "dazun Nan ya fita maybe Anjima ya dawo" "Okay" Sadeeq ya Furta hakan Yana koma gun Omar dake ta faman cika Yana batsewa, dafa kafadar sa yyi sannan yace, "Kayi hakuri har me gidan ya dawo Omar tanan ne zamu San ydda zamu Kama bakin zaren" cije lips dinsa Omar yyi har yanzu murmushin da Meera ta sakarma saurayin Nan be daina sukar sa a zuciya ba, Suna tsaye kuwa saiga motar Alhaji Kabir ta shawo kwana shi da dad ne a ciki, inda Allah ya taimake su ma ba ciki Suka shige da motar ba, dad ne ya fara fitowa take kirjin Omar ya fara harbawa yanzu da wacce kalma zai tari mutumin Nan daya bashi 'yarsa ya mata rikon sakainar Kashi? Sam dad be lura da su ba saima Hira da suke da Alhaji Kabir dake zuge glass Yana Shirin fitowa, Saida ya fito dad ya juyo domin su tafi idonsa ya sauka kansu, kallon su yake saidai ya kasa tuna inda ya sansu Sadeeq Kam duk kunyace ta ishe shi saikace shine Omar din, Alhaji Kabir dake be gane su waye ba Yana ganin su ya dauke kai dake Suna jikin gate din wani gidan makocinsa be kawo cewar bakinsu bane, Dan zungurin sa Omar yyi ganin Suna kokarin wucewa Dan shima dad din ya daina kallon su Sadeeq ya dubeshi mgn kasa2 yace, "ka musu mgn man" Omar ya dubeshi da sauri Yana Masa mgn da Ido, Dan sauke ajiyar zuciya yyi kafin yyi ta maza ya Isa gaban su dad ya musu sallama, Juyowa sukai Suna Amsa Masa har Omar din dake ta Bayan Sadeeq, gaishe su sukayi a mutunce Suma suka Amsa musu a mutunce Alhaji Kabir yace, "saidai ban gane ku ba 'yan samari" Dan yake Sadeeq yyi yace, "dama baki ne daga kano" sai yanzu dad ya sake Juyowa Yana Kare musu kallo, Alhj Kabir yace, "ikon Allah Kuma wajena kukazo?" Dan sosa keyarsa Sadeeq yyi yace, "ehto dama dai...." Sai Kuma yyi shiru Yana Jin nauyin furucin da zaiyi, Omar kuwa tunda Sadeeq ya fara mgn kansa a duke yake zuciyar sa na harbawa da sauri2 besan me zaije ya dawo ba da alama dad din Ameeran ma ya manta su tunda yake musu kallon Rashin sani, "Continue...Inajin ka" Alhji Kabir ya katse shirun, bakin Sadeeq na rawa yace, "uhum...dama..ni da mijin Ameera ne mukazo" Sai yanzu hasashen da dad yake ya zama gsky hakan yasa shi daure fuska, Alhaji Kabir kuwa kallon mmki yake musu yace, "wancan din ne mijin nata?" Dad kuwa cewa yyi, "akwai wani sauran alaka da suke dashi ne bayan sakin wulakancin da yyi Mata?" A razane Omar ya dago hankalin sa a mugun tashe Yace, "i'm Very sorry dad Amma ni Wlh ban saketa ba" Jin Wannan furucin na Omar yasa Alhaji Kabir yace, "toh Wannan mgnr Bata tsaye bace ku biyomu ciki a tattauna" gaba dad yyi be sake sauraron su ba, su Omar kuwa sunji Dadi kwarai da Alhaji Kabir ya bukaci da su shiga ciki. Inna fure na shirun tube hijab dinta a parlon mamy mahaifiyar Ahmad taga fadowar Ameera da gudu tana kuka, saurin rikota tayi ta zauna kan kujerar hankali tashe tace,