← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 128

Sashe 73

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lkcn da Meera ta dauko kular Abba tana shigowa parlo ta tarad da Dr. Omar zaune Kan kujera Yana latsa wayarsa, Dan Karasawa tayi wajensa a hankali tace Abba Yana dakin shi ne? Saida ya share wasu seconds kafin ya dago Kai ya dubeta Adan kaikaice sannan yace, muje, Yyi mgnr Yana tashi tsaye kafin ya fara tafiya, Bin bayansa Meera tayi tana karewa yanayin tafiyar tasa kallo har suka Isa kofar parlon da Abba yake, daidai zasu Shiga Dr. Omar ya gyara yanayin fuskar sa Yana duban Meera dake bayansa yyi Mata Alamar ta matso, matsowa tayi gefensa tana jiran taji mezai ce mata, Dan kallonta yyi a gefen nasa ya kawar da kansa Yana knocking din parlon Abba hade dayin sallama, Abba dake ciki yyi gyaran murya Alamar su shiga, Buda kofar Dr. Omar yyi Nan suka shiga parlon Abba Yana zaune Kan carpet Yana Jan carbi, dubansu yyi da fara'a yanajin Dadi har cikin ransa, Meera ce ta aje kular hannun ta hade da Dan bowl din da zata zubawa Abba tuwo ta aje tana fadin sannu Abba ya zaman shiru mun barka Kai kadai, tayi mgnr da murmushi, murmushi Abban yyi a ransa Fadi yake Allah sarki hafsatu ai indai zaman shiru ne na Saba da Wannan, Dr. Omar ne yace Abba da fatan hankalin ka ya kwanta da Nan din ko? Yyi mgnr Yana karewa yanayin parlon kallo, 'yar dariya Abba yyi Yana girgiza kansa Alamar eh, Meera na gaban Abba tana dibar Masa tuwo, Dr. Omar na juyowa yyi arba da tuwon samo din da Meera tayi da miyar Kubewa, Da mmki ya zuba mata Ido batare daya dauke ba, Meera na Dagowa kanta taga Ashe ita yake kallo, Dan firgita tayi da kallon nasa har tuwon da ta dauko na neman zubewa, dungurar shi Abba yyi Yana tsare shi da ido, da sauri Dr. Omar ya shafa kansa Yana tattaro fara'a sosai yace Kamar kinsan Abinda Abba yakeso kenan yyi mgnr Yana dauke kansa hade da duban Abban, Abba na murmushi kawai ba mgn, Meera ta sauke ajiyar zuciya ta dauka wani lefin tayi Nan ta tura Masa abincin gabansa sannan ta dauko robar ruwa ta aje Masa, Saida ta Gama jera Masa komai kafin tace Abba zandan fita tayi mgnr da ladabi, girgiza Kai Abba yyi Yana sa mata Albarka a zuciya, anan Meera ta Dan saci kallon Dr. Omar taga bama ita yake kallo ba a hankali Tace sai Anjima tayi mgnr tana ficewa, Koda taje daki ma kayanta ta cire don yin Wanka, bayan ta Gama wankan ne ta shirya ta nutsu kafin ta debo nata abincin taci a daki, lkcn data fito da plate din hannunta a lkcn Dr. Omar ya shigo parlon Ya dawo daga wajen Abba, Meera na ganin shi ta karasa a hankali Tace ban sani ba ko zakaci tuwon na kawo maka? Tayi mgnr kanta a kasa, Ji tayi ya dago Kan nata Yana bin kwayar idonta da kallo yace tuwo? Wazai ci maki tuwon? Yyi mgn cikin tsare gira, matsawa baya Meera tayi Tace kayi hakuri shiyasa na tmby, sake matsawa gabanta yyi yace sbd kinaso nayi katon tumbi irin naki Koh? Da sauri Meera ta dago tana girgiza Kai tace No ni ba nufina kenan ba Kuma dai ni Banda tumbi, tayi mgnr kamar me Shirin kuka, Sake matsowa yyi dab da ita yana kallon saitin cikin ta yace idan ba tumbi bane meye Wannan? Yyi mgnr Yana Fisge mata hijab dinta hade da dage mata rigar daidai saitin cikinta, da sauri Meera tayi kasa tana kokarin rufe jikinta taji ya tokare ta, zubawa shafaffen cikin nata kallo yyi da mugun mmki, Ramin cibiyar ta ya kurawa Ido kamar me nazarin wani Abu, Meera data kasa kaiwa kasa ta jawo rigarta daya dage da sauri ta mayar ta yanda take sai a lkcn Dr. Omar ya dago da sauri Yana sakin ta ya dafe goshin sa Dan tsaki Yaja batare daya sake bi ta kanta ba ya wuce sama da sauri. Bin bayansa tayi da kallo a tsorace tana dafe kirjinta daya fara harbawa da sauri da sauri dago Kan da zatayi kenan daidai lkcn Dr. Omar yadan juyo daga can sama idon su ne ya sarke da juna a tare dukkansu kowa ya janye idonsa da sauri ya wuce daki yyinda Meera itama jikinta na rawa ta wuce kitchen.*****A hankali ya gangara cikin B.U.K din Yana karewa yanayin ta kallo wani Abu na taso Masa a hankali, a Haka harya Isa wajen parking din motoci, Saida ya Gama parking dinsa Dr. Omar ya dauko wayarsa ya latsa Kiran Dr. Sadeeq, Bugu daya Dr. Sadeeq ya dauka hade da fadin yeah ka shigo. Yess Dr. Omar ya Furta hakan a takaice, Okay gani Nan zuwa, Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana yanke wayar, aje wayar hannun sa Dr. Omar yyi Yana me sa hannun sa a baki hade da karewa B.U.K din kallo Yana ganin yadda mata da maza ke harkokin gabansu, Yana zaune shiru Haka ya hango Dr. Sadeeq Yana karasowa, Knocking yyi Masa ya bude Masa gidan gaba ya shiga, zama Dr. Sadeeq yyi yace GM da kansa, yyi mgnr cikin tsokana, Dan cije lips Dr. Omar yyi yace ya ake ciki da Shirin mu? Yyi mgnr Yana duban Dr. Sadeeq, Jan ajiyar zuciya Dr. Sadeeq yyi da murmushi yace yanzu Haka yau za'a manne sunayen su a department sunan sa Yana daya daga cikin Wanda za'ayi musu canjin department ko yabar skul din ya karasa mgnr da murmushi, Girgiza Kai Dr. Omar yyi yace Ina fatan sabon H.O.D dinsu da aka sake yyi Abinda ya dace, Dr. Sageer yace ai karka damu Wannan karon Jan wuya ne Insha Allah bazai bada matsala ba is hardly yaci gaba da zama a department din Kai kaga yawan carryovers dinsa kuwa? Cikin takaici Dr. Omar yace shiyasa nake mmkin wanne irin Kan kifi gareshi 2years back ya kamata ace yyi graduation Amma har yau Yana school sbd tsabar Rashin ciwon Kai, Dr. Sadeeq yace Bari dai muga indai shi ba maloho bane yaji an Masa canjin department ko an cireshi a skul zai magantu Koda yake Yana takama da kudinsa maybe yace zaiyi amfani dasu, Dan murmushin gefen baki Dr. Omar yyi kafin ya hade Rai yace zuwa yanzu zai fahimci kudi ba komai bane domin ba'a ko'ina suke yiwa mutum amfani ba, Dr. Sadeeq yace kwarai kuwa haka mgnr ka take, karar wucewar motoci sukaji suna juyawa suka hango zugar motocin Sageer ne ke tafe a layi zuwa cikin makarantar, kallon juna sukayi kafin Dr. Omar ya fara Shirin tada motar sa, Dr. Sadeeq ya kalleshi da sauri yace Ina zamu? Dr. Omar na fitowa daga inda yyi parking yace can department dinsu zamu, Dr. Sadeeq yace haba Kai kuwa Kai da muke yin Abu cikin sirri Taya zamu fito karara tun yanzu? Dr. Omar nabin layin dasu Sageer sukayi be tankawa Sadeeq dinba saima dage glasses din motar sa da yyi ya zamana duhu ake gani daga waje Babu me ganin na ciki, Dr. Sadeeq ya dafe goshi Yana sake fadin please ko badan mu ba kayi tunani akan sabon H.O.D dinsu kada wani Abu ya sameshi, sai a lkcn Dr. Omar ya juyo Yana kallon Dr. Sadeeq yace tunda kace Jan wuya ne Ina kyautata zaton Babu Abinda zai sameshi, Dr. Sadeeq yace No sharrin mutanen Nan fa yawa gareshi Abinda zaka duba kenan, daidai lkcn Dr. Omar ya Karasa gaban Department dinsu Sageer becewa da Dr. Sadeeq komai ba yyi parking dinsa daga nesa dasu cikin wasu motoci tsilla-tsilla da aka jera aje a wajen, kallon Department din yyi Business Administration ya fadi hakan a ransa, kallon Sadeeq yyi a fili yace Business Admin yanada kyau sosai da ace ya maida hankali tabbas da yaji dadinsa especially da kace babansa babban mutum ne da kuwa Kota bangaren business ne Saiya taimaka Masa, Tunda ya fara mgnr Dr. Sadeeq tsura Masa ido yyi Yana tunanin ranar da Dr. Omar zai fahimci ai a company din baban Sageer din yake aiki, Amma a fili kuwa 'yar dariyar yake yyi kafin yace kasan wasu yaran masu kudin Basu cika bawa ilimi muhimmanci ba sbd sun taso cikin Gata Kuma suna ganin komai kudi zaiyi musu shiyasa Basu wani damu ba, girgiza Kai Dr. Omar yyi yace Allah ya kyauta, Ameen Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana hango taruwar wasu mutane bakin department Ana Dan hayaniya sama2 tabo Dr. Omar daya fara latsa wayarsa yyi, Dagowa yyi Yana Masa Alama da ido lpy? Dr. Sadeeq ya nuna Masa bakin department dinsu Sageer yace kamar fa har an manna Dan ga mutane can tsaye sun cure gu daya Ana hayaniya, kallon wajen Dr. Omar yyi daidai lkcn suka ga fitowar Sageer a fusace ashe Sageer tun Yana gida aka Kira aka tsegunta Masa cewar anyi Masa canjin course, shine ya shigo makarantar a fusace badan Haka bama tunda ya fara harkokin bikinsa ya daina waiwayar B.U.K, Koda Sageer ya shige motar sa ma a guje suka bar makarantar bayan sun Gama bade Kura daga inda suka tashi, Saida suka tafi duka kafin Dr. Omar yyi kokarin fita, da sauri Dr. Sadeeq ya kamo hannun sa yace Dan Allah karka fita duk yadda akayi akwai masu sa Masa ido a skul dinnan kada ya fahimci kana bibiyar sa Bari ni naje yyi mgnr yana kokarin tashi, tsaki Dr. Omar yyi Yana Fisge hannun sa daga rikon da Dr. Sadeeq yyi Masa yace matsoraci baya zama gwani ka Barni Wannan fadan bana zaune bane Bayan Haka ma ni already sunana ya baci a skul dinnan banaso kaima sunan ka ya shiga ciki idan hakan ta faru Kuma bazan taba yafewa Kaina ba, yyi mgnr Yana dauko wata facing cap yasa Akan lallausan gashin kansa tare da wani mask dinsa daya dauko take ya badda Kama ya koma kamar ba Dr. Omar din ba, Kallon Dr. Sadeeq yyi yace ka jirani anan mota kada ka fito yanzu zan dawo, girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi Dan ya Rasa bakin mgn yanzu, Canja yanayin tafiyar sa yyi ya saki jiki Kamar Wanda zaije nasa department din, Kai tsaye office din H.O.D ya nufa, Yaje zai bude kofa kenan yaji
Chapter 73 · 0% Book details