← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 128

Sashe 31

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"just look at you da karfin ka, da hankalin ka, ka Isa ka nemi sana'ar Yi ka nemi halak dinka Kai da mutanen ka duk Babu yaro memakon kuyi sana'ar Da zata fishshe ku sai ku tsaya Kan sana'ar kisa? Zaratan samari irinku ku tsaya wasting time dinku Kan Abinda zai zame muku tashin hankali a ranar lahira? Bakusan cewa daga lkcn da kuka cika shekaru 18 zuwa 40 za'a tmbyeku Ina kuka karar da samartakar ku ba? Meyasa bakwa tuna irin Wannan ranar? Baku fahimci cewa duk Abinda ka nema Bata hanyar halal ba baya lasting? I know nasan kunada iyaye, ko 'yan uwa, ko kanne, Kai wasu cikinku sunada Yara ma, Amma kuka zabi ciyar dasu haramun, memakon ku ciyar dasu da gumin halak sai kuke tura musu wuta a cikinsu da hannun ku, sbd son zuciya da lalaci"

ogan 'yan daba da yyi zuru yace,

"Dan Allah kayi hakuri bazamu Yi Masa komai ba tafiya zamuyi"

Dan murmushin takaici yyi kafin ya maida kallon sa Kan daddy daya kafe shi da ido tun dazu yanajin wani irin Abu na taso Masa a zuciya, Dr. Omar yace,

"bani zaku bawa hakuri ba Wanda kukaso kashewa zaku bawa hakuri yyi mgnr Yana kallon daddy"

Ogan 'yan daba har kasa ya duka Yana fadin,

"kayi hakuri Alhaji bazamu sake ba"

yyi mgnr Yana duban sauran yaran sa Suma suyi Abinda yyi, hakan kuwa sukayi Nan suka matso suka bawa Alhaji Abdullahi hakuri, Alhaji Abdullahi ya dubi Dr. Omar yace,

"Tabbas Allah baya bcci, Banda hakkin kowa Amma Dan Adam baya rasa makiya, ban sanka ba Allah ya turo min Kai a lkcn da muke bukatar taimako ko iya haka aka tsaya dole na Kara yiwa Allah godiya sannan idan nine na yafe musu suje indai sunada hankali iya Abinda ka Gaya musu ma ya ishesu karatun ta nutsu"

girgiza Kai Dr. Omar yyi ya dubi ogan 'yan daba yace,

"sai ka tattare yaranka ku fice yanzun Nan, kar naji ko na Kara ganin hanya ta Kara hadani daku matukar Bata Alkhairi bace"

Ogan 'yan daba yace,

"hakan ma bazata faru ba"

yyi mgnr Yana shigewa gaba yaransa nabin bayansa, Saida suka shige motar su ya Tabbatar sun bar wajen gaba1 ko kurar su ba'a gani sannan ya juyo Kan su daddy da suka Mike suna kallon Dr. Omar din, wani irin kwarjini yaga daddy yyi Masa har cika Masa ido yake sbd wani irin girman sa da ya gani, Dan murmushi yyi musu Yana hade hannayen sa sannan yace,

"ayi hakuri nayi Karam bani sai anjiman ku"

yyi mgnr Yana juyawa da nufin tafiya, Ji yyi an dafa kafadar sa ta baya, fasa ci gaba da tafiyar yyi Yana kallon daddy batare da yace komai ba, daddy daya kafe shi da ido Yana kallon sa cikin birgewa yace,

"Ka godewa Allah Dan samari gsky iyayen ka sunyi sa'ar Da me hankali da jarumta Allah yyi maka Albarka Alkhairin Allah ya bibiyi duk inda kke Allah ya rabaka da sharrin makiya"

Wani irin Sanyi dabe tabaji ba a Rayuwar sa shine yaji yanzu, Bayan Abba be taba ganin Wanda yyi Masa Addu'ar dayaji har ransa tana ratsawa ba sama da mutumin Nan, Take duk wani kunci dayake ciki ya fara warwarewa Yana komawa wani irin yanayi na nutsuwa da Nishadi, Cikin murmushi Dr. Omar yace,

"Nagode sosai da wa'annan Addu'o'in kaima Allah ya raya zuri'a"

"Ameen"

Daddy ya furta Yana murmushi Wani Abu na tsirga Masa a zuciya musamman daya tuno babban dansa Sageer, Dr. Omar yace,

"Ina Kan hanya ne Allah ya bamu Alkhairi"

Alhaji Abdullahi yace,

"a'a baza'ayi haka ba inason sanin waye Kai, son samu ma ace mun tafi dakai gidana"

ya karasa mgnr Yana kafe Dr. Omar da ido, Dan kawar da Kai Dr. Omar yyi sbd tun dazu idan sun hada Ido yake ganin wani irin kwarjini da daddy ke Masa, sannan kafin yace,

"Kayi hakuri banyi maka komai Dan wani Abu ba hasalima hanyace ta biyo Dani tanan Dan haka zancen na biyoku be taso ba, mgnr waye Kuma a takaice sunana OMAR SALEES"

"Masha Allah"

Alhaji Abdullahi ya furta da murmushi yace,

"Sunan manya kenan Allah yyiwa rayuwa Albarka"

"Ameen"

Dr. Omar ya Amsa da murmushi Yana matukar Jin dadin fatan Alkhairin da Wannan bawan Allah ke Masa tun dazu, sbd tun ranar da mlm sale ya afka Rashin lfyr mgn shikenan ya rasa sautin da zaiji Wanda za'a Masa fatan Alkhairi, Umman sa zai iya rantsewa tunda yake a Rayuwar sa da wayon sa dai Bata taba Masa fadan Alkhairi ba, Daddy ne ya katse shirun ta hanyar bashi wayar sa yace,

"gashi samun number ka"

yyi mgnr Yana Mika masa, Karba Dr. Omar yyi ya saka, sannan daddy ya Kira yace,

"Kayi saving da Abdullahi"

Daddy ya Fadi sunan a takaice batare daya Fadi full name dinsa ba,

"Okay"

Dr. Omar ya furta hade dayin murmushi, anan yyi musu sallama ya tafi harya kule musu daddy be daina kallon sa ba haka zalika Dr. Omar be daina waiwayen daddy ba har mmki yake Toh mema ya Shiga kansa haka da yake ta yawaita kallon mutumin Nan? Shifa a ka'idar sa ma ko kana kusa dashi ba lalle ya kalleka ba bare yasan kana wajen, shiyasa abin yake ta daure Masa Kai harya kunnan motar daya Gama garawa a layi yabar wajen. A bangaren daddy kuwa Dr. Omar na wucewa ya sauke ajiyar zuciya, Driver ne ya matso cikin girmamawa yace,

"Alhaji da alama yaron Nan ya birgeka Koh?"

Dan murmushi Alhaji Abdullahi yyi Yana kallon driver dinsa yace,

"ban taba ganin saurayi me cikar Kamala da jarumta irin tashi ba, komai da ake bukata Cikakken saurayi ya zama ya hadasu, gsky iyayen sa ba karamin dace sukayi ba Dan irin Wannan daya suke tamkar da dubu"

Driver na kokarin tada motar da 'yan daba suka bar musu yace,

"Wlh mgnr ka hakane dukda ban sanshi ba Amma ji nayi ya Shiga Raina farat daya, ya matukar birgeni sosai a zamanin Nan wanne mutumin ne zai iya tunkarar 'yan daba ya tarwatsa su lkci guda batare da an zubar da jini ba? Gsky Kam Iyayen sa sai hamdala"

Alhaji Abdullahi yyi murmushi kafin yace,

"Shiyasa na takaice sunana sannan na karbi number sa sbd inason sake haduwa dashi bawai rabuwar kenan ba"

Driver yace,

"Toh Allah ya hadaku da Alkhairi"

"Ameen"

Daddy ya furta Yana Kara hasko Namijin kokarin Dr. Omar tare da tunano malohon dansa Sageer, har gobe ya rasa wanne irin Kaine da Sageer tamkar ba jinin sa ba idan yyi wani abun, Amma Babu Abinda zasuyi Masa sai Addu'a da fatan shiriya.

******
A bangaren saratu kuwa, cikin hanzari suka Isa bukkar bokan da suka Saba zuwa lkcn da mutane biyu a gabansu Dan haka Saida suka jira, Bayan Wanda suke gabansu an gama dasu Suma suka Shiga, Saratu tace,

"Boka ka taimake ni yaron Nan Maru Yana neman ballo min aiki"

Boka yace,

"yanason ayiwa mijinki mgni Koh?"

Saratu ta girgiza Kai da sauri tace,

"kwarai kuwa shiyasa nakeso ayi wani Abu akai Dan ban shiryawa hakan ba"

dariyar sa ta hauka yyi kafin yace,

"kinzo inda Matsalar ki zata tafi, Wannan aikin me sauki ne"

Take Saratu da Nas suka washe baki, boka yaci gaba da fadin,

"Yanzu haka na tura Masa Aljanun da zasu mantar dashi Akan zancen, ba iya shi kadai ba, kowama daya danganci mgnr za'a mantar dashi, Babu me Kara tada zancen yabi iska, saidai kafin na hada aikin Nan na hango wani farin haske acikin bincike na"

Zaro Ido Saratu tayi tace,

"me hakan yake nufi?"

Boka yace,

"Nima Abinda ya daure min Kai kenan Amma karku damu zanci gaba da bincike a cikin halwar tsafina harna hango meye musabbabin Wannan hasken"

Sauke ajiya zuciya sukayi kafin Nas tace,

"tunda yanzu Babu matsala ai shikenan koma miye maji daga baya"

boka yace,

"kwarai kuwa Dan na yadda da Kaina ba wani matsala bace"

Anan suka zube Masa kudin da suka kullo suka fito waje cikin farinciki.

~~~~
Tunda ta koma gida take kuka sbd kukan da take da tashin hankalin data fada ciki har wani jiri-jiri takeji kafin wani lkci har wani irin zazzafan zazzabi ya rufeta, Nan ta kwanta a daki tana rawar dari hakoran ta na karawa da juna, Su Anty shafa kuwa Saida suka dawo suka sanarwa mom duk Abinda ya faru, Aiko kamar ta goyasu Dan Dadi sbd sunyi Abinda takeso musamman data fahimci yanzu sun zama na hannun Daman Sageer a kalla itama zata fara kwala Kai idan mutane suka fahimci a cikin yaranta akwai wacce Sageer yakeso, shiyasa Koda suka ga Ameera na kwance Basu bi ta kanta ba saima warwasawar su da suke hankalin su a kwance.

°°°°
Saratu na komawa gida zamanta keda wuya a tsakar gida tana bawa mlm sale lbri hade da dariyar mugunta sbd tasan baxai iya mgn ba sukaji Anyi sallama,

Amsawa Saratu tayi tana bin yaran dake shigo da Kaya niki2 a hannun su, Saratu ta zaro ido d mmki tace,

"Kai Maru ne ya turo ku?"

Tayi mgnr tana sake bin buhun shinkafar da aka aje gefe da katon din su taliya da macaroni hade da kayan shayi na manyan gwangwani, Basu Amsa Mata ba yaran suka fice d sauri Saratu zata sake mgn kenan taji an sake yin sallama, Shiru tayi tana kallon matar data shigo, Cikin mmki da Al'ajabi tace,

"wa'alaykis salam sannun ki baiwar Allah saidai da Alama kinyi batan Kai Dan ba gidan da kike nema Kika shigo ba"

tayi mgnr tana bin budurwar da kallo, Murmushin Mugunta DR. AMINA, tayi tana Dan wurga keys din hannun ta hade da karewa zubin gidan kallo kafin ta dawo da kallon ta Kan Saratu data zuba Mata Ido tana kallon ikon Allah tace,

"Karki damu ni bakuwarku ce"

tayi mgnr tana kallon gefen mlm sale daya zuba Mata Ido da mmki tun dazu, kafin ta maida kallon ta Kan Saratu tace,

"Ina fatan Zan samu karbuwa?"

Cikin sauri Saratu ta Mika Mata wata farar kujera da Dr. Omar ya siyo musu guda biyu sbd zama tace,

"ga waje zauna"

Tayi mgnr tana wucewa Dan debo Mata ruwa,

"dakin barshi ma sauri nake"
Chapter 31 · 0% Book details