← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 128

Sashe 38

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"tsabar mutumin Nan ya Raina Mana hankali duk yadda muka taimaka Masa Akan case din Ameera da Omar be gani ba?"

Mom ta zaro Ido a tsorace tace,

"wani abune ya faru?"

Kasa mgn Anty shafa tayi sbd takaici sai Anty Jamila ce da tun dazu take cika take batsewa tace,

"Sbd shi tantiri ne Wai Aurenta zaiyi?"

Mom na dafa kirji tace,

"ita wa?"

"Ameera Mana"

Anty shafa ta fada kamar ta fashe Dan haushi, tafa hannu mom tayi tana fadin,

"yau mun hadu da mayya kaska Ashe har yanzu Bata saki kurwar sa ba?"

Anty Jamila tace,

"Wlh nidai na gaji mom zuwa Wannan lkcn duk shegen dayace Yana sonta da aure gwara a lika Mata shi mu huta wanna jaraba har Ina"

mom tace,

"Ku barni da ita Insha Allahu Wannan shine Karo na karshe dole a aurar da ita bazan lamunci Shiga hancin da take muku ba"

Anty shafa tace,

"shima Sageer din da alama saimun biyo Masa ta Bayan gidane mutum sai shegen nacin tsiya kamar bunsuru"

mom ta jawo hannun su suka zauna kan kujera mgn kasa2 tace,

"Kunga yadda nake baza mulkina a gidan Nan Koh?"

Suka girgiza Kai, tace,

"Kunga yadda na raba uba da 'yarsa ko?"

Suka sake girgiza Kai, Mom ta saki munafukar dariya tace,

"Dan haka kar kuji komai Akan Sageer kusa a ranku kamar yazo hannu ne dole cikinku ya auri daya"

Take suka rungume ta cikin jin Dadi suna ganin ma kamar anyi an gama ne.

Meera na bayan labule tana jinsu, wasu zafafan hawaye ta share tana tunanin itakam batasan wacce irin rayuwa take ciki ba, Komawa daki tayi ta zauna tana tunano Rayuwar ta tacan baya, wasu Abubuwan ta manta kadan take iya tunawa, zata iya tuno lkcn da kanwar kakarta tazo Akan zata tafi da ita can garin mamanta adamawa, sosai Dad ya kekasa kasa yace shi baza'a rabashi da 'yarsa ba Kuma hankalin sa bazai kwanta ba idan basa tare, haka badan taso ba Inna fure ta hakura Akan zata dinga zuwa dubata, wani zuwa da Inna fure tayi sai taga gaba1 Meera ta lalace kamar ba wacce ta sani ba a lkcn Inna fure tace dole sai ta tafi da Meera, a Wannan lkcn tuni mom ta juyarwa da dad tunanin sa shiyasa ya rufe kunya ya Yayyafawa Inna fure Rashin mutunci har Yana ikrarin kwadayine yasa ta likewa Meera Dan kawai ya dinga Basu wani Abun, Wannan furuci na dad ya konawa Inna fure Rai kwarai hakan yasa Tasha Alwashin bazata sake waiwayar inda suke ba idan Meera ce Gata Nan su jika su Sha, Toh dake Inna furen ce ma me zumunci hakan yasa Meera ta Rasa Dangin mahaifiya sbd Babu me zuwa inda take sabanin lkcn da mamanta keda Rai har hutu yaran Dangin maman suke wajensu yanzu da Babu ranta kowa ya juya Mata baya, Matse idonta d yyi ja tayi tana ayyanawa a ranta da alama guduwa zatayi tabar gidan Dan Abubuwan da ake Mata ya fara girman kanta.

•••••�
Washe garin ranar kuwa kamar yadda Abbansu Sadeeq ya fada hakan ce ta kasance d wasu frnds dinsa biyu suka tafi nemarwa Dr. Omar auren Ameera, lkcn Dad bekai ga fita ba dake 10am ne Yana gida yaji Ana sallama dashi, Zuwa yyi inda ake Masa sallamar Yana bin bakin fuskokin da kallo, bayan sunyi musabaha Dad yace su shigo parlon baki, hakan kuwa akayi Saida suka zauna sannan Abban Sadeeq ya gabatar da kansu, dad ya karbesu da fara'a sannan yace,

"Inajin ku meke tafe daku?"

Abban Sadeeq yace,

"muna rokon iri ne daga gareka"

dad yace,

"iri kamar wanne?"

Abban Sadeeq yace,

"Yarinyar ka Ameera muna nemawa Danmu Dr. Omar Aurenta"

shiru dad yyi Yana dubansu da mmki yace,

"Ameera?"

Abban Sadeeq yace,

"Itadai Allah yasa ba'ayi Mata miji ba"

Dan numfasawa dad yyi yace,

"Ba'ayi Mata miji ba"

"Alhamdulillah"

duka suka Amsa da fara'a kafin Abban Sadeeq yace,

"Da alama Insha Allahu mun dace"

Dan murmushi Dad yyi Yana tuno maganganun Mom na jiya Akan Meera bin maza take hakan yasa har kotu aka kaita Akan case din gashi an koreta a makaranta, Dad yaji haushi kwarai Dan haka tun daren jiya yake tunanin Kai Ameera can kauye ya aurar da ita Dan bazai iya da Wannan abun kunyar ba...,

"Kayi shiru bakace Mana komai ba"

Abban Sadeeq ya katse Masa Dan guntun tunanin daya tafi, Dad yyi gyaran murya yace,

"shikenan Amma da sharadi"

Abban Sadeeq yace,

"Toh Alhaji Ibrahim meye sharadin naka?"

Dad ya numfasa kafin yace,

"Inason aurensu bazai wuce sati biyu ba"

da fara'a sosai Abban Sadeeq yace,

"indai Wannan ne Babu matsala Insha Allahu za'ayi komai kafin sati biyun"

Dad yace,

"sbd banaso ayi komai din nace kada ya wuce 2weeks ma'ana bama bukatar lefe ko wani kayan Al'ada Abinda musulunci ya amince dashi za'ayi wato iya sadaki ma ya wadatar kayan da yyi niyya Kuma idan taje can sai yyi Mata a dakinta"

Shiru wajen ya dauka kowa Yana bin dad d kallon mmki, Abban Sadeeq ne yace,

"Toh hakane Alhji duk Abinda ka fada be sabawa shari'a ba Amma baka ganin kamar zai zame Mata abin Gori?Kasan mu fa mu maza"

Dan murmushi Dad yyi yace,

"Ai tunda Abinda nace haka Addini ya tanadar so no need ayi dogon sharhi akai"

Gaba1 wajen suka Amsa da,

"Masha Allah, Allah ya Tabbatar da Alkhairi"

"Ameen"

dad ya Furta, anan dai sukayi Masa sallama suka tafi.

Bayan tafiyar su ne dad ya iso cikin parlon su, lkcn Mom tana karyawa ya shigo zama yyi kawai bece komai ba, mom ta dubeshi tace,

"harsun tafi?"

Dad ya girgiza Kai yace,

"eh bakin Ameera ne"

mom ta zaro ido sosai cikin mugun furuci tace,

"wani alkaba'in ta sake jawowa Koh?"

Girgiza Kai dad yyi Yana sake balancing Akan kujera yace,

"Neman Aurenta akazo Yi"

tari mom ta farayi da sauri sbd ruwan tea din data kurba yasa ta kware dalilin Jin furucin Dad, Saida ta nutsu kafin tace,

"waye yakeson auren nata?"

Ta fada a tsorace kada ace Sageer ne yyi saurin Aiko magabatan sa sbd yace Aurenta zaiyi, cikin Rashin damuwa yace,

"Wani Wai Dr. Omar."
8/15/20, 8:03 PM - Ummi Tandama: *200 ne kacal👌🏻ba yawa Domin sanin yadda Zaki biya ki nemi Wannan number 09039118754*

......🐓🐓🐓

Na
*Nuceeyluv😘*

23....

"Dr. Omar?"

Ta Furta hakan hankali tashe sbd tasan har dashi yaranta suke so, Dad yace,

"Kin sanshi ne?"

Saurin girgiza Kai Mom tayi tana saita nutsuwar ta hade d murmushin yake tace,

"wannan Abu yyi kyau Allah ya Sanya Alkhairi"

"Ameen"

dad ya Furta kafin yaci gaba da fadin,

"Nan da 2weekes ne auren na fada musu ba sai sunyi lefe d sauran abubuwa ba sadaki ma ya Isa"

Dukda mom tayi farinciki d hakan Amma cewa take,

"Haba Alhji Ana aure ne ba lefe?"

Dad ya yatsina fuska yace,

"Wannan shine babban hukuncin ta sbd abun kunyar da take neman jawo Mana badan Allah ya turo shi bama kauye Zan kaita"

kauyen yafi dacewa da ita mom ta Fadi hakan a ranta Amma a fili kuwa tace,

"Bari nazo Ina zuwa"

ta Fadi hakan tana mikewa da sauri Dan duk hankalin ta a tashe yake kada aje yaranta su Rasa Dr. Omar din, tashi Dad Yyi shima ya wuce dakinsa sbd karasa shiri Yana fada Mata ta sanarwa da Ameeran Toh kawai mom tace tana ci gaba da tafiya batare data waiwayo shi ba.

Su Anty shafa na bcci kowacce ta ware kafa tana sheka bcci sukaji an daka musu duka a cinya, a firgice suka Mike suna bin mom da kallo, lkcn Meera tana can kitchen tana aikin nata na wanke2, Mom na zama gefen gadon tace,

"Kuna Nan a sheme za'ayi muku tsakiyar da ba ruwa"

Gwalo Ido sukayi suna gyara zaman su Anty Jamila tace,

"Me kike nufi mom?"

Mom tace,

"Ina Wannan mutumin da kuke bani lbri?"

Anty shafa tace,

"wa kenan? Kinsan mutanen dayawa"

tsaki Mom tayi tace,

"Dr. Omar"

Kallonta sukayi da mmki har suna hada baki wajen Furta,

"meya faru?"

Mom cikin damuwa tace,

"Dazun Nan magabatan sa sukazo nema Masa auren Ameera ni Wlh yarinyar Nan ta cuceni bansan wanne irin kafi uwarta tayi Mata kafin ta mutu ba"

Jin dariyar su tayi sama2 hakan yasa ta dubesu sosai tace,

"Kai Anya a cikin hayyacin ku kuke kuwa? Kunsan Akan wa nake mgn?"

Dariya sosai suka sake barkewa da ita dakyar Anty shafa tace,

"Wlh kedai mom kinada rikicewa"

mom tace,

"idan na rikice sbd d wa nayi?"

Anty shafa tace,

"Wai duk akan Dr. Omar kike Wannan damuwar?"

Mom na dubansu d mmki sosai tace,

"Koh bashi bane kukace kunaso na skul dinku?"

Anty Jamila ce ta amshe zancen da fadin,

"wlh kin bamu dariya, sannan Wannan abun d yyi yazo Mana a daidai dama munata neman solution din da zaisa a daina ganin wanzuwar Ameera a gidan Nan"

Kan mom ya kulle kwarai Dan haka tace,

"ku fahimtar Dani ban gane me kuke nufi ba"

Anty shafa tace,

"Dr. Omar dai Dan kyau Yana da kyau Masha Allah Amma fa Babu kyan Aljihu"

Ta karasa mgnr tana dariya, Mom ta zaro Ido tace,

"Kamar ya?"

Anty shafa na daidaita dariyar ta tace,

"Dr. Omar ba kowa bane......"

Nan ta kwashe komai Abinda Sageer ya sanar dasu jiya ta fada Mata Kai harda Kari akai, sosai mom ta rike cikinta sbd dariya Dan tunda Anty shafa ta fara mgn dariyar ta kubce Mata, Nan suka hadu su ukun suna dariya, kafin tace,

"kuce Allah ya taimake mu"

Anty Jamila tace,

"kwarai kuwa domin anyi walkiya kowa ya gane asalin sa"

mom tace,

"aikin banza ni na dauka yadda kuke lbrin sa wani shege ne Ashe saurayi ba kwabo ne"

Anty shafa tace,

"kede Kya fada mom Banda iyayi da kaifin Kwakwalwa Babu komai"

Mom tace,

"Toh za'aci kyau ne? Ai sai yanzu naji dadin Abinda dad ya yanke"

Anty Jamila tace,

"me yace?"

Mom tace,

"ya sanar musu Banda lefe Sadaki kawai idan taje can yyi Mata"

habawa tuni suka tuntsure da dariya harda tafawa Fadi suke lalle zamu yarda Kullon mangwaro mu huta da quda, Nan dai sukaci gaba da shewarsu hade da tattauna yadda bikin zai kasance.
Chapter 38 · 0% Book details