← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 128

Sashe 13

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safna data kasa rike dariyar ta tace,

"Kai Hajjaju granny yace fah"

mahuci Hajjaju ta mako ma Safna tace,

"kema ungo Nan wato hade min Kai zakuyi Kuna kirana da sunan Arna Koh?"

Safna tace,

"bafa sunan Arna bane"

Hajjaju tace,

"ku gayamin wanne cikakken musulmin ne ake kiransa da girandi? Sai kace wani Sigari"

Tashi Sageer yyi Yana bokaro baya hade da takunsa daya saba na tataccun gayun bariki yace,

"matsalarki kenan granny bakya tsayawa ki fahimci Abu"

yyi mgnr Yana ficewa a dakin,

"Oh ni Jikar balarabe"

hajjau ta furta tana rike haba tace,

"Wannan DA Bansan gadon wa ka iyo ba Wlh Sam dangina Babu tantiri irinka."

Safna tace,

"Hajjaju Angon ki ne fah"

Hajjaju tace,

"Allah ya sauwake me zanyi da Wannan zubin 'inyamuran? Karfi da yaji ya maida kansa wata kabilar can."

Safna tana dariya tace,

"bakida dama Hajjaju Allah yabar Mana ke"

dariya Hajjaju tayi tace,

"matsa min kafata 'yar Albarka."

Nan Safna ta matso tana yiwa Hajjaju tausa.
8/15/20, 8:01 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....🐓*
( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Na
*Nuceeyluv😘*

9....

A bangaren Dr Omar kuwa da sassafe ya Gama shirinsa tsaf lkcn Sahabatu na yin abincin siyarwa Wanda take fita dashi Yana fitowa waje Sahabatu ta Miko Masa kula tana fadin,

"ga Karin kumallon, kallon ta yyi kamar bazaiyi mgn ba can yace,

"barshi kawai"

Sahabatu tace,

"ummah tace akai da safe"

jin hakan yasa Dr. Omar ya karba batare daya ce komai ba ya fice, Sahabatu binsa tayi da kallo zuciyarta na raya Mata abubuwa a kansa kamar yadda ta Saba, Dr. Omar Kam zafin hanashi fadan da ummah tayi ne kan Sahabatu ke Bata Masa Rai, a da Yana sa Mata ido sosai sbd yadda yaga tarbiyar kanwar tasa tana neman lalacewa samari barkatai take tarawa ga Rashin kamun Kai kamar wata motar haya kowa nata ne, Omar baya gani ya kyale Saiya tanka wani lkcn har duka zai Mata musamman idan saratun Bata Nan saidai idan ta dawo sahabatun ta Gaya Mata karya da gsky Nan kuwa Saratu zatayi ta balbalin masifa tana fadin bakin ciki yake wa 'yarta Dan yaga Tanada farijin jini, shi omar idan yaji ummah na fadin haka abun har mmki yake bashi toh shi Kuma ba danta bane da tafi nuna kulawa kan Sahabatu? Kuma a ganin sa Sahabatu ai jinin sa ce Dole yyi Mata hukunci, toh Amma sai yaga kamar ummah na nuna masa banbanci da ita, sai yaga kamar tafi son Sahabatu a kansa, saidai yasa hakan a ransa Kila kodan shi Dan fari ne shiyasa ake boye soyayyar sa irin ta mutanen Da, baya manta Rana ta karshe daya tarar da Sahabatu tana Hira da wani gajan yaro a kofar gida Suna zaune ko Gap Babu sun manne sosai a ranar yyiwa Sahabatu dukan kawo wuka sbd yadda yaga suna lalume junansu dake lkcn darene Kuma Babu haske ta wajen, Saratu dakyar ta kwaci Sahabatu a wajen Dr. Omar cikin mugun bacin Rai tace Kai Maru matukar kaidin Dan halak ne daga yau karka Kara yiwa 'yata Sahabatu fada akan kome matukar ka kuskura ka Mata Koda tsawa ne Wlh kaji na rantse saina daga maka nono idan yaso ka lalace kabi duniya tayi mgnr zuciyar ta na tafasa haka kurum ba Ita ta haifesa ba yazo Yana nuna Mata Isa akan 'yarta?, Wannan kalaman da Dr. Omar yaji yyi matukar girgiza shi harya fara tunanin Anya ba canjashi akayi wajen Ummansu ba? Wacce irin tsanace tayi Masa haka? Astagfirullah Dr. Omar yyi Istigfar sbd gani yake kamar shedan ne yake nema yyi Masa Wasa da hankali ya dauki hakan a Matsayin tasa kaddarar kenan, toh tun daga ranar shi da Sahabatu sai kallo Babu fada bare tsangwama hakan ya bawa Sahabatu damar sheka ayarta yadda takeso.......

"Umaruuu..."

yaji an katse Masa tunanin da yake Ana kwada Masa Kira sosai a Bayan sa da sauri ya waiga yaga Ashe mlm Shamsu ne, mlm Shamsu na tahowa da sauri yace,

"tunda ka fito nake maka mgn naji kamin shiru zatona baka jini ba na sake Kira Nan ma haka da alama tunani kke kana tafiya kodai jikin mlm dinne?"

Omar yadan tattaro jarumtar sa ya Buda baki dakyar yace,

"barka da safiya"

mlm Shamsu yace,

"barka dai ya me jikin?"

A takaice yace,

"Alhamdulillah"

"Masha Allah"

mlm Shamsu ya furta Yana ci gaba da fadin,

"ko can ka nufa?"

Girgiza Kai Dr. Omar yyi bece komai ba, mlm Shamsu yace,

"toh Madallah Dan Allah ka gaishe min shi da jiki Nima zanzo duba shi Insha Allahu"

Dr. Omar yace,

"okay"

yyi mgnr Yana wuce shi. Mlm Shamsu ya bishi da kallo yace,

"Oh Kai Kuma kullum fuskar ka a hade tamkar hadari"

yyi mgnr Yana tafiya shima.

Ya fito kan titi kenan ya hango motar Sadeeq na kokarin karya kwanar layin su, Sadeeq dake cikin mota ya hango shi shima Dan haka ya karaso wajen da sauri, Dr. Omar ya leka ta window yace,

"Ina ka nufa haka da sassafe?"

Sadeeq yace,

"kaifa ka cika rainin wayo Wlh kana ganin dai Ina na nufo ka tsaya tmby na"

kafada Dr. Omar ya daga Alamar I don't care yace,

"Taya Zan San Abinda ke ranka?"

Sadeeq ya bude Masa kofar gaba yace,

"shigo muje sai nayi maka bayani"

Dr. Omar ya Shiga Yana Dan murmushi yace,

"Yasu hajiya?"

( mahaifiyar su Sadeeq kenan) Sadeeq yace,

"duk suna lpy tace ma tana yiwa Abba sannu zasu zo duba shi Anjima"

Dr. Omar yace,

"da Basu wahalar da kansu ba ai Ina kyautata zaton yau ma za'a sallame shi tunda abin yazo da sauki"

Sadeeq yace,

"muna fatan hakan"

suna Dan Hira jefi2 haka suka Isa har cikin AKTH.

~~~~~
Sageer gaban Hajia Aisha kansa a Duke yaji ta sake fadin,

"mgn nake maka Sageer"

Sageer yadan kalli gefen sa ya basar kafin yace,

"ni mummy har yanzu fa yaro ne ni"

Mummy tace,

"ni Banga yarinta ba anan Sageer ka dubi shekarun ka kusan 38 Amma har yanzu banji kana zancen tsaida matar aure ba Bayan kanada yadda zakayi"

Sageer yadan tabe baki Yana fadin,

"haba mummy ni kullum sai kuyi tamin zancen aure Bayan ga frnds Dina Nan Babu Wanda ya aje Mata beside ma ni ban shirya zama tsoho ba yanzu"

Mummy ta Kama haba tana kallon Sageer tace,

"Ikon Allah dama aure tsoho yake maida mutum?"

Sageer yace,

"sosai ma kuwa haka kawai kafin wani lkci a dinga cemin baba haba aji down Wlh ban shirya ba Sam."

Mummy ta hade fuska tace,

"su 'yan matan da kke Hulda dasu meye ribar zama dasu da kke?"

Sageer yadan fara kame2 can yace,

"mummy wa'annan ai abokan karatu ne Dole ayi Hulda da Mata tunda Ana university"

yyi mgnr cikin basarwa, mummy ta girgiza Kai ita Sam lamarin Sageer Yana daure Mata Kai ba Abinda zata Mai sai fatan shiriya, komawa jikin kujera tayi tace,

"Abban ka Yana dab da dawowa daga Paris saika San Abinda zakace Masa"

tura baki Sageer yyi ya Mike tsaye Yana Kade bujen wandon sa yace,

"nifa gsky Ana takurani dayawa haka kawai kamar jariri koyaushe sai an juyani kamar waina"

Yyi mgnr kasa-kasa yadda Hajia Aisha bazata ji ba, Hajia Aisha tace,

"me kace?"

Sageer Yana Dan waigowa yace,

"ah No mummy I'm not saying anything"

ya fada Yana barin falon gaba1 Hajia Aisha tace,

"Allah ya shiryeka Shirin Addinin musulunci"

tayi mgnr tana lumshe idonta.

****
Yau Kam wanka iya wanka anyi shi, wanka na kece raini ma kuwa dake Anty shafa da Anty Jamila sun kware wajen Shiga kanti yasa suka samu tubarrakin bobs da mazaunai, Dan duk Mai suka sa musu ya Kara fitowa dukda sunsan side effect nashi hakan be hanasu shafawa ba, saidai duk yadda suka so beyi Kama da na masu natural ba domin aka hadasu da Meera sai sun Raina kansu Dan ma dai Ameera na yawan sa doguwar riga ne Amma dukda haka shape dinta na fitowa sosai irin figure 8 dinnan ne sama da kasa komai yaji Masha Allah idan akace sumar Kaine kuwa tamkar Jinin indiyawa dukda baya samun gyara sosai hakan be hanashi kyau da santsi ba abindai tubarkallah, kallon kansu a madubi sukayi kowacce Tasha riga da wando damammu sai wata 'yar iskar kinomo da aka kawo aka Dora akan rigar wacce take shara-shara da ita da Babu duk daya, wani siririn gyale suka kawo suka saka fuskar Nan Tasha makeup kamar kuwa zasu je zaben kyau, Ameera Kam sai ganin ikon Allah take Ana haka mom ta leko, mom tana ganinsu tace,

"wow My babys kunyi kyau"

ta fada tana zama bakin gadon su, Dukansu dadine ya Kama su suna dauko jakar hannun su sukace,

"yau mom da wuri zamu wuce sbd Tsaro"

mom ta Miko musu kudi tana fadin,

"dad dinku ma ya Dade da fita shine ya Baku kudin kashewa na Baku"

Rungume mom sukayi suna fadin,

"Kai Wlh mom ke ta dabance"

mom tace,

"ai babban farincikina Naga yarana suna walawa cikin arziki"

dariya sukayi dukansu suna Sanya takalmin su a kafa sukace,

"ai ba karamin dabara kikai Mana ba mom da tuni muna can kauye wajen su Inna fure"

Mom ta kamo hannun su suka fice tace,

"ai tsuntsu daga sama gasasshe na samu Abinda nake fata kenan"

Nan sukaci gaba da hirar su suna shewa har mom din kamar wasu kawaye, Ameera na jinsu saidai tayi murmushin takaici kawai sannan ta Mike a gurguje ta gyara kan gadon nasu da suka Bata dama tuni ta share dakin hade da mopping Dan tun Asuba take aikin gidan gaba1 gado ne karshen gyarawa lkcn sun Gama batawa saita gyara, dake tun asubar takeyin wankan ta yasa ta jawo Ghana masgo dinta ta dauko wata riga da skirt ta saka dakyar ma skirt din ya shigeta sbd sun Mata kadan yo yawancin kayan nata ma sunyi Mata kadan sbd ba'ayi Mata dinki, saidai idan sun dawo ta roki su Anty shafa su Bata kayansu da suka gaji dashi dama yawanci haka suke Mata kuncen su shine nata Bata samun sabon Kaya tunda aka dauke hankalin Dad daga gareta ta rasa Wannan damar,
Chapter 13 · 0% Book details