Sashe 124
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
faruwa ne?" Nan suka fara sanar da ita halin da Sageer yake ciki a takaice dai Shidin ba kowa bane Sai Dan tantangaryar me Aikatau, zubewa mom tayi a kasa hannu akai tana rusa kukan bakin ciki Fadi take, "yau wanne irin iftila'i zan gani a rayuwa?" Musbahu ne yace, "a'a mlm bazaki Tara Mana jama'a anan ba tashi zakiyi kibar Mana Nan" mom cike da kunar Rai Tace, "bazan bar Nan ba saikun fitomin da 'yata azzalumai shima Sageer din Allah ya Isa me kudin bogi bamu yafe Masa ba wahalar da mukai a kansa" sabitu ne ya dauko sanda yace, "Bari nazo na make ki idan baki tashi Nan wajen ba" ya Fadi hakan Yana nufota da sauri mom itama ta Mike da sauri Dan saura kadan ya muka Mata sandar ta goce ai kuwa a guje tabar wajen tana barin warin takalmin ta a wajen tamkar mahaukaciya, Saida tayi nisa dasu ta rabe gefe tana saukar da Numfashi Tace, "Bari naje gidan Jamila sheggu matsiyata itama gidanta kullum a rufe maza da Mata na zarya saikace gidan karuwai" Nan tayi gaba tana takawa da kafa duk Wanda ya ganta bazaiyi zaton me hankali bace Koda yake marabar ta da tababbe kadan ne. Anty shafa data Gama ramewa tayi baki sai dogon baki take tikar aikin gidan Sageer, tun Bayan da sukayi aure Abubuwa suka canja Kama daga Rashin Bata hakkin ta zuwa kayan abinci da abin more rayuwa Bata da banbanci da wacce take Aikatau a gidan Sageer karshe ma boys quarter ya tura ta tun Bayan sati da auren su kenan yace baya bukatar ta, wayoyinta da duk wani kayan kallo kin Bata yyi saita koma tamkar wacce take prison ba Abinda ta sani na game da halin da duniya take ciki, cikin yaransa masu take Masa baya da masu gadi ya Basu ita kyauta yace duk Wanda yyi ra'ayi ya bashi dama yahau kanta, Hankalin Anty shafa ya tashi matuka duk Wannan iyayi da masifa tata Saida suka tafi ba shiri take kuwa ta fara canja kamanni daga baki2 zuwa yellow2 Toh dama farin na kanti ne yanzu kuwa Babu Mai wani lkcn ma man gyada take shafawa ko Dan tayi kyalli, 'yan matansa da yake kawowa kullum safe Rana dare itace Nan me musu hidima duk yawan su Haka Dan dole ta horu dayin girki Dan tun a farko2 data kwaba musu abinci a ranar kusan kwana Sageer yyi Yana jinkar ta sai kace ya samu jaka wani irin takaicinta yakeji da alama dai Shirin da sukai Masa na boka beyi lasting ba, dake ba sanin inda yake tafiya take ba shiyasa duk kwanakin Nan da baya Nan Bata kawo cewar kamashi akai ba, ba Kuma tasan cewa mom tana zuwa ba Toh itama so take tabar gidan Babu Hali sbd wa'annan tsagerun yaran nasa da suka maidata kamar jaka kowa yaji bukatarsa yazo ya rage zafi a kanta. Acan bangaren Jamila ma dai kusan hakan ne tun a satin farko take ganin abin Kamar wasa na Faisal saidai Inaa ta Kare musu kallo tsab Basu da mutunci ko kadan Abinda ya Kara daga mata hankali shine yadda taga hatta a cikin mazan ma neman kansu suke Haka ma matan, tun a lkcn ta tsorata kwarai taso barin gidan Faisal yace ba Shiga ba fita, tanaji tana gani Haka aka maidata 'yar Les din dole mazan Kuma akwai masu amfani da ita ta dubura Kai Abinda dai ya kasanta duk ta lalace itama ba kwanciyar hankali. Mom na zuwa kofar gidansu Jamila taga wasu maza na dirawa ta Bayan katanga, abin ya bata mmki, kafarta daya ba silifas Haka ta karasa jikin gate din gidan Nan taci Karo da motar 'yan sanda kowa sai rige yake Yana Shiga wasu Ana damko su ciki kuwa harda Faisal kafin wani lkci an hankado keyar Jamila da wasu mata, kusan suman tsaye mom tayi lkcn data hango Jamila baka Kirin Kamar wacce Tai wankan bakin Mai sai wuya zololo Kamar na zakara a kideme ta Isa garesu tana fadin, "Jamila? Kece Haka?" Juyowa Jamila tayi tana ganin mom ta fashe da kuka, matar dake rike da Jamila ta tura keyarta ita Kuma tana Kiran Mom, cikin 'yan sandan ne da suka Zo yace, "ko itace uwar taku?" Da mmki Jamila ta kada Kai jikinta na kyarma, kallon wata macen 'yar sanda yyi yace, "itama hado da ita" a firgice mom taja baya tana fadin, "da nayi me Kuma?" Kamata matar tayi Tace, "idan kinje can kyayi bayani" "yau mun Shiga uku mun lalace wacce irin jarabawa ce take afko Mana lkci guda?" Mom ta Furta hakan tana share hawaye, Jamila na hango ta daga dayar motar da sukazo tanason mata mgn ba dama Dan ba'a hadewu waje daya ba Nan akayi dasu police station, Ashe kafin suzo Nan can gurin Anty shafa gidan Sageer kenan aka fara zuwa farat daya aka musu aka damke su Saida aka kaisu station kafin aka kamo su Anty Jamila, Dr. Sadeeq na ganin wucewar su ya zaro wayarsa Yana Kiran daddy, dauka daddy yyi Dr. Sadeeq yace, "an gama hado kansu daddy" daddy yace, "good job Sadeeq zuwa gobe zamu shiga kotu dasu" Dr. Sadeeq yace, "toh Allah ya nuna mana." washe garin ranar kuwa kotu ta cika makil ciki harda Dr. Omar da Meera da sukazo sune ma last din zuwa, 'yan b.u.k duk an taru, ga lectures da professors kowa na wajen especially 'yan faculty of medicine, Saida kowa ya hallara kafin aka titso keyar masu lefi tun daga Kan Saratu, Nas, Sageer dake ta fisge2 sai su Faisal da wa'annan tantiran 'yan iskan da aka taddasu gidan Faisal da Sageer, Suna shiga kuwa kowa ya dinga binsu da kallo hardai ma su Saratu da fuskokin su ya nuna Alamar yagu da yakushi, ba komai Yaja hakan ba sai damben da suke tayi da Nas lkcn Suna cell kullum ta Allah sai sunyi fada Suna aibanta junasu da mugayen kalamai kala2 Toh dama amintar da ba'a ginata a tubalin gsky ba karshen ta Dana sani ne, Nan fa aka fara hayaniya kowa na tofah Albarkacin bakinsa, dad Yana can bangaren su daddy da Kuma Abba kowa da Abinda Yake sakawa a ransa hardai dad dake bin mom da kallon takaici ya Rasa ma Toh meya gani harta kaishi ga Aurenta? Abba kuwa kwallar takaici ya goge a fakaice gani yake kusan duk yafi kowa Shiga kunar rai na Abinda Ahalin sa suka ja Masa, ga matarsa Koda yake ya Dade da sakinta tun bayan data bar gidansa da Wannan safiyar asuban ga Kuma dansa Sageer da aka tarwatsa Masa rayuwa akasashi yin rayuwa Kamar ta mafarki wacce Babu tabbas a ciki, Alkali ne ya doka guduma Nan kowa yyi tsitt Ana Jiran aji ta bakinsa, Bayan karanto dukkan lefin kowa kotu ta bukaci Saratu ta Amsa lefinta, Saratu jikinta na rawa Tace, "duk Abinda aka fada tabbas na aikata da hadin Kan Wannan matar Nas" ta nuna Saratu, a kufule Nas Tace, "sbd ta kwabe Miki shine Zaki ce Wannan matar? Amma dai Allah ya tsine aminta dake saratu" Saratu Tace, "aminta Dani Koh ke? Akan mugun nufinki game da Hajia Aisha na fada tarkon shaidan a maimakon na tona Asirin ki tun a lkcin zuciya da son banza ya rinjayeni na aika Wannan mummunan Abu" Nas ce ta bude baki zatayi mgn aka daka mata tsawa hakan yasa tayi shiru tana Muzurai, Alkali ya bukaci yadda akai suka kulla abin Nan Saratu ta fara sanar dasu tun daga ranar da taji subutar bakin Nas da Kuma yadda zuciyar ta Raya mata Kan Hajia Aisha na Wannan mummunan aiki, Nan jama'a suka hau salati kowa da Abinda yake tofawa a kansu daga masu tsine musu sai masu musu mugun baki zantuka dai kala2 yanzu Kam Sageer ya gamsu kwarai da Abinda ke faruwa a gabansa ji yyi kamar duniyar zata kifa dashi sbd shiga rudani, su Anty shafa, Jamila, mom kuwa jikinsu ne ya Kama rawa mom Fadi take, "Kun cucune 'ya'yan Nan yanzu duk dukiyar da muka kashe Ashe akan Wannan tantangaryar kolo dinne? Allah ya Isa kudina" Anty shafa Tace, "har yanzu mom zancen kudi kike? Bakya tuna cewa hakkin Ameera ne ke bibiyar mu??" Nan kotu ta sake dakatar da surutan da ake tayi, Alkali yace, "bayan Wannan mugun aiki da mata tayi kwanakin baya da dadewa Wannan yaro Sadeeq yaje wata kotu dashi yaron Nan Omar ya Masa sharrin fyade hakan ya jawo zubewar mutuncinsa da Kuma barinsa skul din idan da Hali inason ganin prof Akilu da duk lectures din da suka sa hannu wajen korar sa, shi kansa Alkalin da yyi shari'ar zamu so ganin sa" kamar yadda Alkali ya bukata kaf Suna wajen Dan Dr. Sadeeq bebar ko daya ba Saida yabi lungun da sako ya lalumo duk Wanda keda sa hannu wajen zubewar mutuncin abokin sa, Nan fa 'yan surutai suka Fara tashi Ana tuna Abinda ya faru baya, bayan Alkali ya tsaida surutun nasu ne ya karanto asalin gskyr karar da Dr. Omar ya kawo akan Ameera, kowa na wajen yyi mmki kwarai wasu sun tuna lkcn da abin ya faru Wanda suka manta Kuma na kusa dasu na kokarin tuna musu, shiru wajen ya dauka Alkali na duban Sageer da yyi tsamo2 tamkar kazar data fada ruwa yace, "shin hakane ko kuwa kanada abin Fada akai?" Girgiza Kai Sageer yyi cikin Jin kunya matuka yace, "karar a kaina take ba akan Omar ba domin Shidin ceton ta yazo Yi a lkcn a takaice dai hakkinta yakeso ya kwatar Mata a kotu ni Kuma nayi amfani da kudi na juyar da komai kansa hatta barinsa skul da hannu na ciki" Nan fa cikin prof Akilu ya duri ruwa dama tun Daren jiya sai zawo yake sbd firgici especially da yasan asalin Dr. Omar da Kuma waye Sageer, sauran da suka sa hannu wajen korar sa ma kowa hankalin sa ya tashi sosai, Alkali yace, "toh madallah" Yana gyara medicated glass dinsa yace, "Saratu da Nas an yanke musu hukuncin karasa Rayuwar su gaba1 a gidan yari hade da horo me tsanani Babu beli sbd mugun aikin da suka aikata dan sun wargaza farincikin mutane da dama sunsa Yara biyu sunyi