Sashe 90
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.......Acan bangaren Meera kuwa bayan sun saki junan su da dad ya kamo hannun ta yace, "mu Shiga daga ciki Meera" girgiza Masa Kai tayi hawayen farinciki na wanke mata zuciya Wai yau dad dinta shi ke mata kallon 'yar cikinsa sabanin a baya da aka juya Masa tunanin sa akanta, da kafar dama tasa kafarta tana Addu'a ba komai take tunawa ba sai yadda zata hadu da mom, tun daga farfajiyar gidan nasu ma ta fahimci komai an Sauya shi hatta painting gidan an sake, shiru taji Babu alamun motsin komai har suka kaiga Shiga parlon su still Babu Alamar da mutum a gidan, Bayan sun shiga parlon ne Meera ta kalli dad tanason Yi Masa mgn taji yace, "ki saki jikin ki Meera gidan Nan ni kadai nake rayuwa a ciki tun bayan wasu kwanaki so no more tension" a kidime Meera ta dubi dad bakinta na Furta, "Mom fa?" Dan murmushin takaici yyi kafin yace, "I don't know" sake wara idonta tayi sosai zatayi mgn yasa hannun sa a baki yace, "kije daki ki shirya ba wani dadewa zamuyi ba daga Nan Adamawa zamu wuce" Adan firgice tace, "Dadd" girgiza mata Kai yyi yace, "Wannan Alkawari ne na daukarwa Kaina duk ranar da muka hadu baza mu dau lkci ba zan sadaki da dangin mu ni da mahaifiyar ki" wasu irin siraran hawaye ne suka zubowa Meera tana share su da sauri Tace, "Thank you Dad" murmushin shima yyi yace, "har yanzu banyi komai dazai sa ki gode min ba Meera, I have a lot of Abubuwan daya kamata na sauke Miki su a Matsayin mahaifi, shiyasa nakeso muje can din Bayan Haka inason mgn da mijinki kafin mu tafi" wata irin faduwar gaba ce ta dirar wa Meera yanzu me zatace wa Dad game da Aurenta? Sunkuyar da kanta tayi tana matsa 'yan yatsunta bakinta Kuma na rawa ta kasa furta komai bataso ta sanar da Abba zuwanta bada izinin mijinta bane a samu matsala dukda dai taga yanzu dad ya sauko sosai, shirun nata da tayi ne yasa dad ya shiga nazarin ta sai yanzu yaga Tarin ramar da tayi harda Dan kashin wuya idonta a zuge kowa ya gani yasan tana cikin damuwa hakan yasa yaji tunani ya shige shi kodai Aurenta ne ya mutu? Musamman daya ganta da trolley dinta, Jan Numfashi yyi Yana gyaran murya Sam bayason takura mata domin ita din ta kasance gudan jinin sa wacce duk duniya baida wani sama da ita, a nutse yace, "karki damu Meera kije can dakin ki ki huta zansa a kawo Miki abinci kinji?" Daga Kai tayi Alamar Toh, hakan yasa dad ya Mike hade da mata sallama ya fice, bayan tafiyar sa kuwa yasa Meera ta zubawa parlon nasu Ido sai yanzu ta fahimci gaba1 kayan parlon ma an canja su tun daga labulaye har izuwa kujeru carpet da sauran su, Mikewa tayi da nufin tashi taji ta kasa, kasanta taji na mata zafi ainun dama tun data baro gidan Omar dauriya kawai take, dakyar ta samu ta lallaba ta Mike tana Dan dogara hannun ta bisa marar ta ta wuce dakinta daya kasance harda su Anty shafa ada, take ta fara tunanin Toh Wai duk meke faruwa ne? Ina su Anty shafa suke? Dan batasan da batun auren su ba, tana Shiga dakin kuwa ta ganshi a gyare tamkar mutum na rayuwa a ciki komai an canja an saka Sabo, a Haka ta sake lallabawa ta shige toilet hannunta dafe da bahon wanka take hada ruwan dumi, Saida ya taru kafin ta shige ciki ruwan na ratsa marar ta kuwa ta Mike a zabure gaba1 zafi ne ya isheta saidai tasan ba Abinda yafi hakan mgni a gareta Haka dai ta sake komawa ruwan tana rintse idonta duk haushin Omar ke dawainiya a ranta, ta sake ruwan dumi yafi sau biyar Saida taji Dan dama2 kafin ta fito daga ciki, yanzu Kam da sauki Dan Bata Wannan dingisawar tafiyar ta ma tadan daidaita, tana dawowa daki ta Isa gaban mirror kayan shafa ne kala2 ta dubesu da murmushi cikin Jin Dadi wato dai dad a kowanne lkci ma Yana jiranta? Allah sarki iyaye Nan idonta ya fara ciko da kwalla sbd tuno Ummanta da tayi, a Haka taci gaba da shafa cream bayan ta Gama ne ta wuce wadrobe tana budewa shima cike yake da kaya, wayyo Allah Dadi ya sake kamata Nan ta fara ruwan Ido harta samo doguwar riga me sauki tasa a jikinta, Saida ta shirya tsaf ta sauko kasa tanajin cikinta na kadawa sbd yunwa, fitowar ta kenan taji Ana knocking budewa tayi taga wata mace da basket a hannun ta, Bayan sun gaisa a mutunce ne tace, "gashi inji Alhaji" karba Meera tayi da godiya ita Kuma matar ta tafi, dawowa parlo tayi ta wuce can dining area tana zuwa ta fara hadawa kanta tea me kaurin gaske zama tayi kawai ta fara Sha a hankali tanajin dadin cikinta, tunanin Omar ke mata yawo a kwanya tana tuna Daren su na jiya, idan ta tuna Wannan Abu ba karamin Kona mata Rai yake ba Kai ita a takaice ma gani take kamar raping dinta yyi badan son ranta ba, ba komai ke Bata haushi dashi ba saidai idan ta tuna jikinta kawai yakeso ba itan ba Dan har yau Bata manta Wannan kalmar Wai kece "matar so din" sbd ya Raina mata wayo taja tsaki a fili, shigowar dad yasa ta kawar da tunanin Omar tana kallon sa fuska a sake Dan bataso ya gane Abinda take ciki, Dad daya shigo da 'yar fara'ar sa yace, "kin Gama shiryawa?" Meera Tace, "eh" "Good kici abinci enough yanzun Nan zanje na shirya mu wuce" Meera ma zaro Ido Tace, "dad tun yanzu?" Kallon agogo yyi kusan 11:45am yace, "Ameera me zamu jira? Na Gama shirya Mana komai tun kafin kizo already ma fitana na sanar da mutanen Adamawa zuwan mu so ki zama ready jirgin 12pm zamu bi" Haka kawai taji kirjinta ya buga ya zatayi da auren Omar a kanta Kuma? Da son samu ne a kallah ace ta karbi takardar ta kafin su tafi saidai tana ganin hakan da Kamar wuya ba lalle ta samu cikin sauki ba infact ma batason yasan inda take, da Wannan tunanin ta Mike itama bayan ta Gama ta wuce daki Dan shiryawa, 11:50am har sun fito a shirye Dan Meera ma kayanta ta canja zuwa bakar jallabiya tayi rolling kanta da gyale hannun ta rike da trolley din data gani sabbi a dakinta, Saida suka Gama kashe duk wani kayan wuta suka rufe ko Ina kafin suka fito daga gidan, sabon me gadin nasu Ayuba na bakin gate dad ya bashi kudi masu yawa hade da wata farar takarda Ayuba ya karba bakinsa yaki rufuwa yanata zabga godiya kafin yace, "Wannan farar takardar ta miye?" "Address Dina ne nacan Adamawa incase anzo nemana saika bayar" "Toh Madallah Allah ya tsare" mlm Ayuba ya Furta hakan Yana sata a Aljihu, Nan sukayi Masa sallama suka tafi, suna zuwa kuwa Ana Kiran sunan su Dan Haka Basu wani Dade ba Suka shige cikin jirgi sai Adamaw. Dr. Omar na Gama parking kofar gidan su Sadeeq ya sake zaro wayarsa da nufin kiransa, bugu daya kuwa Sadeeq ya dauka Dr. Omar yace, "Ina kofar gida" Sadeeq yace, "ka shigo Mana" "No abin bana zama bane" Dr. Omar ya furta hakan Yana katse wayar da mmki Sadeeq yabi wayar da kallo Toh ko meke damun Omar Kuma? Jawo kofar parlon sa yyi kafin yyi nufin fitowa daga gidan, Yana fitowa waje kuwa ya hango Omar cikin mota ya tsurawa kofar gidan kallo kamar me nazari, Karasawa Sadeeq yyi Omar ya bude Masa gidan gaba ya Shiga, kallon sa Sadeeq yake tun dazu yyinda Omar ya kawar dakai gefe Yana tunanin Abinda zai furtawa Sadeeq, "ka kirani Kuma kayi shiru akwai matsala ne?" Sadeeq ya katse musu shirun da tmby, Juyowa Omar yyi Yana kallon sa kafin yace, "taimakon ka nakeso" Sadeeq ya gyara zaman sa sosai yace, "go ahead Inajin ka" Dan cije lips dinsa Dr. Omar yyi kafin yyi ta maza yace, "gidansu Meera zaka rakani" a mugun firgice Sadeeq yace, "ban gane Wannan tmbyr taka ba Omar" lumshe ido omar yyi duk hankalin sa gaba1 nakan Meera yace, "nidai kamin Abinda nace" juyar da kansa Sadeeq yyi yace, "Wannan Abu Dan sauki? Kaje wajen ita Ameerar Mana ta fada maka Address din gidansu kazo Nan kana tmby ta ga wacce tafi kowa sani kusa dakai" kallon sa sosai Omar yyi yace, "Wai meyasa bazaka gane ba Sadeeq?" Sadeeq shima ya juyo Yana kallon sa sosai yace, "Toh me kkeso na gane? Kai tsaye fa kazo Wai na rakaka gidansu abun ba dadin ji kwata2 mutum sai fadin Rai ka kasa cire Abu a ranka Fisabilillah duk kiyayyar ka da ita ya kamata ace ka mutunta Ahalin ta Amma abin kunya ace matar daka aura ko kadan bakasan gidansu ba wacce irin rayuwa ce Wannan?" Dukda Sarai Dr. Omar yasan gsky Sadeeq ke Gaya masa Amma hakan be hanashi daure fuska ba, sannan yace, "matsalar ka kenan daga anyi maka tmby daya simple question maimakon ka bawa mutum simple answer saika tsaya kana dogon sharhi akai" "sbd na fada maka gsky ai dole kace Haka" "Toh naji yanzun ma ai Abinda nake kokarin Yi kenan nasan gidan surukai na" Dan murmushi Sadeeq yyi yace, "Toh ko Kai fah? Yanzu kaga saika koma gida ka fadawa Meera ta shirya kuje" dafe goshinsa Dr. Omar yyi duk yadda yaso ya biyowa abin ta bayan gida Dr. Sadeeq ya tare Dan Haka ya dubeshi sosai cikin nutsuwa yace, "Bata Nan" da mugun mmki Sadeeq yace, "Ameeran? Ina taje?" Cije lips dinsa yyi kafin yace, "gidansu" "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" Dr. Sadeeq ya saki salati Yana tafa hannu yace, "sakayyar da zakayiwa 'yar mutane kenan Omar?" Omar ya katse shi shima da fadin, "Kai bafa Abinda kke tunani bane just ta tafi ne da kanta shiyasa nakeso muje tun Abu beyi nisa ba" Kokarin bude kofa Sadeeq yake yace, "Toh mgnr gsky badani za'ai Wannan gangancin ba" da mmki Omar yace, "zuwa wajen matar tawa shine gangancin?" Sadeeq yace, "au yaushe ka maida ta a Matsayin