← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 128

Sashe 114

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Littafin na kudi ne, 200 Zaki turo account din Nan 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻* 8/22/20, 8:44 PM - Ummi Tandama: Nan parlon ya sake yin shiru Banda kukan Meera ba Abinda akeji, ba Kamar bangaren Omar daya daskare a wajen idonsa Akan Meera Yana mata wani irin kallo Wanda ya banbanta da duk wani irin kallo daya taba Yi mata a baya, Wannan kallon da yake mata kallo ne dayake haskowa daga can Fadar zuciyar sa, a take ya dinga Jin wasu irin kibiyar so da kaunar Meera na rige-rigen dira a hadaddiyar Fadar zuciyar sa, yanzu ne asalin zuciya da gangar jikinsa suke yiwa Meera kallon kauna badan ya kwashi Ni'ima a jikinta ba, jinta yake har cikin bargo da jijiya, tausayinta da Kuma zazzafar kaunar ta na safara a dukkanin magudanar jininsa, ya kasa daina kallon ta domin ya manta da wasu a wajen...Abban Ahmad ne yyi gyaran murya kafin yace, "tabbas mgnr Ibrahim Haka take akwai Rashin fahimta a tsakanin su duka biyun a kowanne bangare kowa yanada laifi mgnr gsky ko waye akace anyi sanadin barinsa karatu Yana matakin karshe na gamawa bazaiji Dadi ba especially medicine dinnan da a Nigeria ba karamin cin kwakwa suke ba yajin aiki da duk Abubuwan su Yana Jan su lkci me tsawo kafin ka kammala, Suna Shan gwagwarmayar rayuwa kafin su kawo Wannan stage din na matakin karshe, kaii dolene ma mutum yaji haushi Toh Amma inda matsalar take Dr. Omar beyi dogon bincike ba kafin ya yanke hukunci akan Ameera, Haka zalika Ameera shaidar data bayar tayi wauta kwarai dgske ba lalle saita Amsa hakan ba da ace tayi dogon tunani da tun a lkcn tayi hanzarin sanar dashi Koda ace yaki sauraranta ko Kuma take ta nuna mutumin dake rike da gun a Kotun gsky tayi kuruciya sosai" gyada Kai dukansu sukayi Banda Omar da har yanzu keta kallon Meera Sam besan ma me suke tattaunawa akai ba, dubansa Abba yyi yaga dai kamar baya tare dasu hakan yasa ya dubi dad, mgn sukayi kasa2 kafin Abba ya dubi Inna fure da duk tausayin yaran biyun ya kamata yace, "Mama tunda abin nasu yazo da Haka to sasanci Yana a tsakanin su saidai mu matsa dan Basu waje" kafin ma ya Ida mgnr Inna fure ta Mike zuciyar ta na fatan ace sun shirya, mikewa su dad sukayi suka fice Sadeeq dayaga Omar din har yanzu Yana wata duniyar yadan zungure shi, firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi Yana waigen Sadeeq bakinsa na rawa be Furta Masa komai ba yyi Kan Meera da take share hawaye, ganin hakan yasa shima Sadeeq din ya fice, Tashi Omar yyi ya matsa gaban Meera a hankali, Zama yyi dab da ita zuwa lkcn Meera Jan zuciyar d take ya ragu sai zuciyar ta dake harbawa da sauri duk tanajin motsin sa kusa da ita, dago hannu yyi zai jawota jikinsa ya kasa ya gwada hakan kusan sau uku Ana hudun ne ya samu kwarin gwiwar jawota jikinsa zuwa saman faffadan kirjinsa ya rungume ta tsam take kuwa suka sauke ajiyar zuciya a tare, habarsa na bisa Kan lallausan dogon gashinta sbd rolling din da tayi ya warware Yana shakar kamshin man kitson data saka sunyi kusan 5secs a Haka kafin a hankali yace, "i'm sorry Meeraaa.." ya Fadi sunan Yana Jan shi a hankali, har cikin ranta taji sunan nata Amma dai ta maze ta dago daga rungumar da yyi mata tana kallon kwayar idonsa da suke a lumshe Tace, "nice ya dace na baka hakuri sbd nayi maka asarar Rasa karatun ka daka Dade kana fama akai Kuma..." "Shiiiii...." yasa yatsan sa daya akan tattausan lips dinta yace, "it's okay Meera mu manta baya kawai" riko yatsan nasa tayi hakan yasa ya zuba mata Ido sosai, Dan sauke numfashi tayi kafin Tace, "dole ne na baka hakuri ya Omar domin kaidin na daban ne I mean ba kowane zai iya daukar Wannan abun daya same ka ba ka godewa Allah kanada kwarin zuciya" Dan murmushi yyi kafin yace, "shiyasa nace mu manta baya Meera kisa a ranki tamkar Babu Abinda kikamin a baya Nima Ina neman afuwar ki plss" ya Ida mgnr Yana hade hannayen sa biyu, hannayen ta biyu tasa ta rike hannun nasa tana Dan dubanshi a hankali Tace, "ni wacece da bazan yafe maka Dan karamin Abinda kamin ba? Abinda nakeso tun wuri shine ka fahimci gskyr Kuma Alhamdulillah anzo wajen Ina fatan Allah ya yafe mana gaba1" "Ameen" Dr. Omar ya furta hakan da murmushi Meera Tace, "Toh tunda...tunda.." sai Kuma tayi shiru, Wara mata idonsa yyi yace, "tunda me?" Meera nayin kasa da kanta Tace, "tun..da dalilin dayasa ka aureni kenan har yanzu kana iya bani takarda na Allah ya hadaka da Zabin ranka Koda yake ma ai ka samu tunda tana gida...." Ta Ida mgnr a rarrabe, shiru taji yyi bece komai ba hakan yasa ta dago tana dubansa sai taga Ashe itan yake kallo, "Ya Omarr.." ta ambaci sunan sa tana Dan girgiza shi zaton ta beji me Tace ba dazun, Dan cije lips yyi kafin ya Kama duka kafafun ta biyu Yana duban kwayar idonta yace, "tunda...tunda..tunda.. me hakan yake nufi Meera?" Zaro idonta tayi a hankali Tace, "bafa Haka nace ba" ta Ida mgnr tana Dan tura baki, "Oh Toh wacce takarda kike nufi? Takardar tsire ko balangu?" Girgiza Kai tayi da sauri tace, "No ya Omar.." "yess Meera" shima ya katse ta d mgn kafin yaci gaba da fadin, "toh idan ma takardar tsiren ne ko balangu meye a ciki? Tunda nasan unborn ke bukata" ya karasa mgnr Yana kallon saitin marar ta kasa2 zaro idonta tayi a firgice tana kokarin matsawa baya ya rikota ta Fado jikinsa, dago Kanta tayi tana kallon sa dab da fuskar sa domin har hancin su ya hade Dana juna sunajin fitar Numfashi juna Tace, "Ka daina Wannan tunanin ya Omar ni Abinda nake nufi shine takardar sak...." Bata Ida mgnr ba kuwa ya manne bakinsu tare, anan ya Shiga tsote tattausan lips dinta zuwa cikin harshen ta, dakyar Meera ta kwace tana maida Numfashi Tace, "Ya Omar mgn muke ta fahimta Amma kana kawar da zancen meyasa Haka ne?" Dubanta yyi na tsanaki kafin a takaice yace, "Karen hauka ne ya cijeni dazan sake ki Ameera?" Zaro Ido tayi dan batayi tsammanin hakan daga gareshi ba, bakinta na rawa Tace, "Toh amma ya Omarr auren namu fa..." "Ya Isa Haka Ameera" ya Fadi hakan Yana Dan Hade fuska, ja baya ta fara Yi yayi saurin tallafo fuskar ta Yana sassauta hade fuskar da yyi kafin yace, "look Meera Koda ace bansan gskyr ba bana tunanin zan sake ki bare yanzu Dana San gskyr Abinda ya faru" lumshe idonta tayi tanajin wani irin Abu na yawo a tsakankanin zuciyar ta, hakan yasa Dr. Omar yaci gaba da fadin, "mgnr gsky shine Raina na baci a duk lkcn da Kika ambaci sakin Nan Meeraaaa..." Bude idonta tayi ta zube shi a cikin nasa cikin wani irin yanayi sai yanzu ta fahimci Abinda ke yawo a tsakankanin zuciyar tata ba komai bane face kaunar Omar da tun fil'izal take Masa, ba ko shakka ta fara sonsa a lkcn da shi din baima San tanayi ba daga ranar daya nuna fushinsa akan Abinda Sageer yaso Yi Mata daga Wannan ranar ya samu gurbi a zuciyar ta, shirun nasu shiya bawa dukkanin zuciyoyin su damar da Isar da sako ta cikin idanun su da suka kafe da juna, wayar Omar ce tayi ringing hakan ya dawo dasu duniyar kallon kaunar da suke ma juna, firgigit kuwa suka farka Meera na Sunkuyar da kanta sbd kunya, shi Kuma Omar din na zaro wayar sa a pocket, ganin Mummy yasa shi daga wayar Yana amsawa da ladabi, Mummy Tace, "yauwa Ameer akwai wani Abu da za'a Kara ne bayan Abubuwan daka lissafa?" Dan kallon Meera yyi kafin yace, "no Mummy I think Abinda nace ma ya Isa saidai Kuma ki tmbyi Safna tunda kusan komai zaizo daya" Mummy Tace, "oh Toh da sauki ma Amma dai dukda Haka wa yafi wani?" Ya fahimci me tmbyr Mummy ke nufi hakan yasa shi sake duban Meera sosai, tana zaune ne kanta a kasa matsawa yyi gefenta ya mikar da ita Meera na Masa kallon mmki, Mummy na fadin, "hello, hello kanajina kuwa?" Omar daya Gama karewa Ameera kallo yace, "hello Mummy Kamar ntwrk mgnr yasa shi daukewa" Mummy Tace, "eh bani answer tmby na" Dan cije lips dinsa yyi Kamar Yana gabanta a hankali yace, "tafi" yyi mgnr a hankali, badan Allah yasa Mummy naji sosai bama bazata ji me yace ba, "Alright" ta Fadi hakan tana kashe wayar, dama hannun sa a bisa kuqun Meera yake ya mayar da wayar cikin Aljihun sa sai a lkcn Meera ta janye rikon da yyi Mata tace, "ni zan wuce ciki" "kina tare da mijin naki Zaki wuce ciki?" Ya mata mgnr Yana rungume hannu a kirji, Dan juya manyan idonta tayi kafin Tace, "Wai bakasan Nan parlon Abba bane?" "Oh! Really?" Dan hararar sa tayi tana sauke Kai, "It's okay yanzu ma saimu koma kano ai" kallon sa tayi da sauri Dr. Omar ya girgiza Kai yace, "yess". Acan bangaren su dad da Abban Ahmad kuwa Suna barin parlon Sadeeq na bayansu Inna fure kuwa tana fitowa ta dubi Sadeeq Tace, "Wai waye ne Wannan Dan iskan Sageer da Kuma waccar 'yar banzan Shafa?" Sosa Kai Sadeeq yyi yace, "ehto gsky sanin waye Sageer lbri ne me tsawo ita Kuma wacce ta Kira da Anty shafa tare nake ganinsu saidai bansan hadinsu ba" Inna fure Tace, "yanzu Haka cikin kawayenta ne masu bakin ciki sukai mata Wannan cin mutuncin Koh?" Dad ne yace, "Mama ba kawayenta bane" kallon sa sukai da mmki, Inna fure Tace, "ka sansu kenan?" Cikin takaicin zuciya dad yace, "yaran matar da nake aure ne da" Salati Inna fure taja ta dire tana tafa hannu tace, "yau Naga debabbun 'ya'ya Kai Wannan mata sadeeya Allah ya Isa tsakaninmu da ita, saidai kayi hakuri Ibrahim Amma Wlh sadiya ta cutar da jinin ameena" Dan Numfashi dad Yaja hakan yasa Abban Ahmad
Chapter 114 · 0% Book details