← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 128

Sashe 107

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

gani 'yar mutunci ce ba irinsu gatsau2 ba" Sadeeq ne yace, "waye Kuma gatsau2?" Hajjaju ta gyada Kai Tace, "hmmm.. Bari dai Dan Nan yarinyar Nan matar Sageer Nan sukazo Wai ya kawota mu gaisa sai gashi tana cira hanci sama tana min kallon uku saura Kwata Kai kace taga Kashi" "ikon Allah" Sadeeq ya Furta hakan, Hajjaju Tace, "da gani irinsa ya dauko marasa mutunci ni so nake Naga idon 'yar jakar uba" murmushi Omar yyi yace, "keda Jikar ki?" Hajjaju Tace, "wa? Allah ya kiyaye Kai Bari kaji ma nifa tun ranar dakazo duniya nasa shakku akan Wannan shegiyar matar Nas" Sadeeq ya Kama haba yace, "tohhh kina wajen aka haifeshi?" Hararar sa Omar yyi Hajjaju kuwa Tace, "bana wajen, Amma Ina Shiga dakin jikina ya bani akwai wata a kasa musamman danaga ta firgice kafin nayi zurfin tunani a kanta saiga mahaifin sa ya shigo Toh abinka da dama can Suna neman haihuwar sai a kanshi Allah ya Basu murnar Wannan ya kawar da tunanin kanta Wlh, ai da tun a lkcn Basu samu galaba kanmu ba" cije lips dinsa Omar yyi yanajin wani irin zafi a ransa wato ma ko dumin uwarsa beji ba aka rabashi da ita, Hajjaju Tace, "ai Wannan mata Saratu ta cucemu Nan Nan aka kawota a fige Wai 'yar gudun hijira Ashe Annoba ce bamu sani ba" mikewa Omar yyi Dan idan yaci gaba dajin Wannan kayan takaicin ransa ne zaici gaba da baci and bayason Bata mood dinsa Dan sugar babe yakeson gani, Yana tashin kuwa Sadeeq ya Mike a sanyaye Dan shikam gaba1 tausayin Omar din ne ya sake Kama shi, sallama sukai Mata ta bisu da Addu'a tana fatan su Isa lpy su dawo lpy, bangaren da Abba yake suka nufa Nan ma Basu wani Dade ba suka fito sbd lkci Yaja saidai Omar ya bashi sakon mlm habu Akan yaje can su gaisa, Suna fitowa waje kuwa daddy shima ya fito cikin Shirin, gabansa sukaje suka kwashi gaisuwa a gurguje ya Amsa musu suka wuce mota har bakin gate Mummy da Safna suka rakasu har suka bacewa ganinsu, Omar kejan motar daddy a baya Sadeeq a gefen sa, hakan yasa tafiyar tasu tayi sauri Dan a guje yake tafiya daddy be hanashi ba sbd shima Yanason wucewa inda aketa kiransa ne, Koda sukaje airport ma 11:57 ne, Suna zuwa Ana Kiran sunan su Dan Haka suka yiwa daddy sallama a gurguje, fuskar su cike da murmushi suka rabu Yana daga musu hannu har suka shige jirgin be daina kallon su ba, Saida jirgin ya fara kokarin tashi daddy ya juya zuciyar sa fari Tass lalle jini ba wasa bane sai yanzu yasan yanajin Nishadi, jirgin su na Gama yunkura kuwa yyi samaaa sai Adamawa...* Kallon kanta Ameera tayi a madubi lalle hausawa sun iya mgn da sukace idan kanada kyau ka Kara da Wanka Toh kuwa Tabbas ta shaida hakan, Dan ita kanta sai ta zamewa kanta Kamar abin kallo dukda ba wani heavy makeup tayi ba Amma hakan be hana kyawunta fitowa sosai ba, Dan murmushi tayi lkcn da take kokarin yafa gyalenta, tabe baki tayi a fili tace, "Banda aure, Koda Allah ya hada fuskata dashi Toh kuwa furucin farko dazan Fara Masa shine bani takarda ta..." Tayi mgnr tana Mika hannun ta kamar Yana gaban ta, cije lips dinta tayi ta lumshe Ido tana kokarin danne Abinda ya taso Mata acan kasan zuciya hannun ta bisa kirjinta a fili tace, "no Meera by now ya kamata ace kin zama jaruma, just continue acting like Babu Abinda ya dameki hakan zaisa ki samu salama a ranki, ki dauki kanki Kamar kin fada wata sabuwar duniyar tamkar ba meeran da aka sani ta farko ba" tana Kare mgnr ta bude idonta tana kallon kanta a mirror a hankali Tace, "yes I can do it..." sallamar Asma'u ce ta katse ta daga surutan da take, hakan yasa ta juyo da sauri tana Amsa mata, da fara'a Asma'u Tace, "Ashe ma harkin shirya" murmushi itama Meera tayi Tace, "eh Shirin ma fitowa nake kikazo" Asma'u Tace, "Toh muje Inna harta Sha ado tana jiranmu a parlo" Ameera Tace, "tsohuwa da ado?" Asma'u Tace, "tab Inna fa akace maki mujedai ki gani" Suna Isa kuwa Ahmad ya turo kofar shima ya zuba kwalliya kamar Wanda zaije daurin Aure harda Karin hula, shigowar sa kuwa ba Wanda idonsa ya nuna Masa sai Meera idonsa na kanta yake matsowa kadan ya rage ya Fadi sbd bigewar da yyi da kujera yyi ta maza ya tokare, Inna fure ce ta Mike Tace, "Toh tunda kowa ya shirya ai saimu tafi, muje Koh?" Ta Kare mgnr tana kallon Ameera data sunkuyar da kanta, Asma'u Kam dariyar Ahmad take cikin ranta tana tsoron ta fasa a fili ya hanata tafiyar ma gaba1, Fara tafiya sukayi Ahmad na gefen kujera daidai lkcn da Ameeran zata wuce ne yyi mgn kasa2 Yana fadin, "you look so beautiful sis...."
Chapter 107 · 0% Book details