← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 128

Sashe 111

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Littafin na kudi ne 200 Zaki turo ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻* 8/20/20, 10:22 AM - Ummi Tandama: Kokarin cire bakinta daga nasa take Amma Ina Sam ta kasa sbd ba rikon wasa yyi mata ba, Riko ne da yake nuna yyi kewar ta he missed her a lot, Sadeeq ne ya dawo daga wajen bayan ya Amsa wayar Yana shigowa parlon yyi gamo take kuwa yyi turus Yana komawa baya bakinsa na furta, "Astagfirullah..." Yana fadin Haka ya juya da sauri, furucin sa ya dawo da Dr. Omar duniyar da yake neman zarmewa, sakin bakinta yyi Yana sauke numfashi a hankali, cikin matukar jajircewa Meera tayi ta maza ta banko Masa Harara tana Shirin mikewa taji ya riko mata qugu, fuska ta hade tana kallon kwayar idonsa da suka fara rinewa Tace, "mlm ka sakar min jiki" murya can kasan makoshi yace, "haramun ne Dan na taba matata?" Ya Kare mgnr Yana mata wani irin kallon daya bugi kirjinta a hanzarce kuwa ta dauke kallonta daga gareshi tana juya manyan idonta Tace, "kanada abin mmki" dage gira daya yyi Yana Mata Dan iskan kallon Nan yace, "kamar ya?" Hararar sa tayi kafin Tace, "be kamata ace kana wasting time dinka a wajen wacce tazo tai maka Aikatau ba, Matsayin ka da class dinka sunfi dacewa da yarinyar daka aura kwana biyu da suka wuce" Dan cije lips dinsa Omar yyi kafin yace, "Ki manta da komai domin ni na shaida kece Kika dace da class Dina Meera" ranta ne ya sosu kwarai tasan ba komai yasa yace hakan ba saidan kawai sbd jikinta, hakan yasa a Dan kausashe tace, "sbd jikina Koh?" Saurin girgiza Kansa yyi yace, "Sau nawa zance Miki ba Haka bane?" Samun nasarar ture shi tayi ranta na zafi tace, "idan bance Haka ba me kkeso nace maka ya Omar? Ka taba kula da damuwata ne tun bayan da mukayi aure? Ka taba tsayawa ka fahimci hakkin ma'aurata akan matan su? Kai bama Wannan ba aure anayin sa ne Dan so da kauna a zatona lkcn da kazo neman aurena zaka kasance me sharemin hawaye ne a lkcn Dana Rasa me sharemin, na zaci kaunace silar auren mu Ashe ni nayiwa abin Rashin fahimta, Ashe kaidin fansa kkeson dauka Kaina Akan Abinda Sam banida hakki a ciki, taurin ranka da nuna isarka ya Omar yasa kaki saurarata bare na fada maka dalilin amsar Dana bayar a kotu, kayi threatening Dina ta hanyoyi da dama marasa dadin ji da sauraro Wanda yake nuna tsantsar tsana da keta Babu Alamar tausayi Koh So na a ranka, koh zuwa yanzu banji da kunne na soyayya tace ta kawo ka ba sai anyi mgn kace ba Haka kke nufi ba a hakan kke tunanin zan aminta da cewar ba jikina kkeso ba...?" Ta karasa zancen nata lkcn da take share hawayen dake malala Kan kumatun kafin tayi Dan Murmushin takaici taci gaba da fadin, "tunda ka rusamin budurcina ya Omar ka fara son kasancewa Dani, baka so ni Ada yadda nake ba Saida ka samu rabo a jikina, Abinda bazan dauka ba kenan ya Omar ka sakeni kawai naje na auri Wanda zai Soni tsakani da Allah....." Ta Ida mgnr cikin fashewa da kuka sosai sbd cin karfinta da yyi kawai ta bude kofar parlon ta fice da sauri. Sadeeq na waje yaga fitowar Meera tana kuka hakan ya bashi damar Shiga parlon da mmki, Dr. Omar kuwa yadda kasan ruwa ya cinyeshi Haka yakeji, tabbas Abinda Meera ta fada Masa gsky ne, Kuma ta fishi gsky shiyasa beyi nufin hanata mgn ba sbd kawai ya gano meye matsalar sa da ita domin ya gyara kuskuren sa Kuma tabbas yaji lalle ba karamin kuskure ya tabka ba, meyasa tun farko ya kasa tsayawa yaji dalilin bada amsar da tayi...? Girgiza shi Sadeeq yyi sbd yanata mgn yaji shiru be Amsa ba, firgigit ya dubi Sadeeq kamar Wanda ya tashi a bcci, har yanzu mmki ne bayyane fuskar Sadeeq yace, "Wai meke faruwa ne Omar?" Sauke ajiyar zuciya Omar yyi Yana me cusa hannayen sa cikin lallausan gashin sa Fadi yake, "akwai Kura Sadeeq" zama Sadeeq yyi yace, "wani Abu Kuma ka sake mata?" Girgiza Kai Omar yyi gaba1 ya Rasa ta inda zai Kama sbd tashin hankali dakyar dai ya samu ya sanar da Sadeeq Abinda zai iya fada Masa, gwauron Numfashi Sadeeq Yaja kafin yace, "mgnta ta zama gsky kenan Omar nasha fada maka ba sau daya ba ba sau biyu ba ka tsaya ka fuskanci matarka kuyi mgn ta fahimta Amma kayita botsarwa kana Dora mata laifi yanzu wa gari ya waya?" Nan fa Omar ya gyada Kai hankalin sa na sake tashi zumbur ya Mike yace, "Bari dai naje na fada mata bayin Kaina ba....." "Nuna min shi yanzun Nan naci kwal ubansa" Inna fure ta banko kofar parlon tana kumfar baki, mikewa dukansu Omar da Sadeeq din sukayi, Meera na gefen Inna fure tana Jan zuciya, Asma'u na kokarin Hana Inna furen fadan da take, "cikin ku waye gantalallen Nan Omar?" Kallon kallo sukayi da Sadeeq kafin a hankali suka duka har kasa Suna fadin, "Ina wuni baaba" "da ban wuni ba zaku ganni? Nace da ban wuni ba zaku ganni?" Shiru sukayi Suna dukar dakai, "Toh tunda Kun kasa fitar da waye umara a ciki nasan dai dole cikin dayan biyun, Dan Haka ku saurara dakyau Kai Omar tun kafin Raina ya Gama baci ka tattara naka ya naka da duk wani komatsan ka kabar Mana gida" saurin kallon ta sukai a tare Inna fure Tace, "eh na fada, kaje can ka nemi daidai Kai Amma ba Wannan Ameeran ba" Sadeeq ne yace, "kiyi hakuri baaba sulhu mukazo" "Toh naji me Ido a tsakar ka" Inna fure ta furta hakan tana Kama qugu, hakan yasa Sadeeq ya sunkuyar da kansa da sauri, Amina ce Tace, "Dan Allah Inna fure ki daina musu fada baki ne fah" "ke dallah ja can an Gaya Miki ko wanne bakone Dan arziki?" Tsuke bakinta Asma'un tayi Inna fure ta koma kan su Omar da gaba1 suka sake dulmiya cikin wani tashin hankalin Tace, "Wai ko an sassakaku da icce ne Naga bakwa motsi?" Tashi sukayi a sanyaye Suna jawo traveling bag dinsu Su Alhaji Kabir suka shigo gidan, tun da suka hango Inna fure suka taho da saurin su daidai lkcn su Omar din sun fito, Alhji Kabir ne yace, "lpy kuka fito bamu Gama mgn ba?" Inna fure Tace, "oh wato kune Nan kuka sauke su?" Alhji Kabir yace, "mijin Ameera ne fa da abokin sa" tafa hannu Inna fure tayi Tace, "Amma baka kyautawa yarinyar Nan ba kabiru" kallon mmki suka bita dashi Tace, "har shi umaran za'a kirashi da miji? Kasan kuwa lbrn aurensa da Ameeran kuwa? Ko Dan kwali fa be siya Mata ba bare wani Abu da ake Kira lefe" dafe goshinsa Alhji Kabir yyi Yana matsowa gun Inna fure yace, "haba Inna, habaa yanzu Akan lefen kike ta Wannan fadan?" Inna fure Tace, "Toh lefi nayi? Ka dubi yarinyar Nan ka gani.." ta nuna Meera dake matse kwalla a gefe Tace, "Gata Nan a bushe a kekashe Kai d gani horon yunwa yai mata" rintse idonsa Omar yyi gaba1 yanajin kansa Yana juyawa Kamar ya dare, Alhji Kabir kuwa yace, "duk Wannan be taso ba Inna yanzu dai kiyi hakuri zuwa gobe sai asan yadda za'a bullowa lamarin" Inna fure Tace, "Toh har sai ankai gobe? Ai karshen lamari yyi nesa da jikata ehe" dad ne ya matso a hankali yace, "kiyi hakuri Inna Kamar akwai Rashin fahimta tsakanin su" kwafa Inna tayi Dan tana kunyar dad din Dan Haka Tace, "shikenan Amma dai su San inda zasu kwana badai gidan Nan ba" Alhji Kabir zaiyi mgn kenan ta daga Masa hannu Alamar ta Gama mgn, kallon Meera tayi Tace, "daina zubar da hawayen ki a banza da gata dai Allah ne ya baki" ta Fadi hakan tana Jan hannun ta su tafi, goge kwallar data gangaro mata tayi kafin ta Dan dago a sace tana kallon Omar daya zuba mata Ido fuskar sa cike da dunbin damuwa, saurin kawar da idon nata tayi tabi Bayan Inna fure batare data sake waiwayen su ba, Alhji Kabir ne ya matso inda suke yace, "kuyi hakuri kunji" Dan murmushi sukai Masa Sadeeq yace, "Wlh ba komai Abba Bari muje gobe Insha Allah saimu dawo" Alhji Kabir yace, "naso ace anan kuka kwana sai ayi mgn ta fahimta a nutse" yanzu Kam Omar ne yyi mgn da fadin, "ba damuwa Tomorrow morning Insha Allah zamu dawo" Ba Haka Alhji Kabir Yaso ba Toh Amma ya ya'iya? Sallama suka ma Dad dake gefensu kafin suka wuce, Suna fita kuwa sunsha kwana kenan Ahmad Kuma ya shigo gidan sunyi sabani kenan. Suna tafe ba Wanda yake mgn a cikinsu kowa na tunani a ransa especially Omar da gaba1 baya cikin nutsuwar sa ji yake kamar yabar wani bangare ne acan gidan, Suna fitowa bakin titi suka tsari abin hawan dazai kaisu hotel. Zama Omar yyi a bakin gado bayan ya fito Wanka shiru yyi kawai ya zurfafa a tunani, Sadeeq dake Kan sofa ma shirun yyi gaba1 tausayin frnd din nasa yake dukda Yana ganin lefin sa da ace tun wuri yabi Abinda yace da duk Haka Bata faruba, Toh Amma zaiyi kokari da kansa ya tmbyi Meera meyasa tayiwa frnd din nasa sharrin fyade a kotu? Wanda ya jawo zubewar mutuncinsa da Kuma karatun sa??, A bangaren Omar kuwa Dan kishingida yyi ransa duk a dagule besan Taya zai fassarawa Meera cewar shifa tun fil'izal ya kamu da matukar kaunar ta b, ya Dade da begenta a cikin ransa, idan akwai Wanda yake kauna Bayan iyayensa Toh kuwa itace, be gane hakan a kansa ba Saida aski yazo gaban goshi, Yanason structure dinta Toh Amma ai kauna da soyayya ba karya bane dole akwai shauki Akan Abinda kkeso, juyi yyi akan gadon sbd yadda yakejin Meera a cikin Fadar zuciyar sa sai yanzu ya fahimci ashe ya Dade Yana dakon soyayyar ta be sani ba girman Kai ya Hana shi gane hakan, dake wutar dakin ganin a kashe
Chapter 111 · 0% Book details