← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 190

Sashe 99

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun safe Amira tana gidan mu, sun hadu ita da Amina suna ta ware min kayan da zan saka a kowanne event, ni kallo kawai nake bin su dashi saboda already Sultan ya bada dinkunan mu ni dashi na kowanne event, anko zamu ke yi, wanda kuma na mata ne kadai shima ya dinka min abinda zan saka, hatta takalmi da jaka babu wanda bai saya ba, hotunan yake turomin ni kuma ina zaba, tunda yanzu mun zama mage da bera bama zama a guri daya. Sai da suka gama shan wahalar su sannan nace "kun gama?" Suka juyo suna kallona nace "to sai ku mayar min da kaya jikin akwati basu zan saka ba" na gaya musu tsarin mu da Sultan, Amira ta bata rai tace "kuma dan wulakanci shine kika barmu muke ta wahala, amma wannan akwai munafukar amarya, shine zaku ware ke da angonki ku tsara abinku ba zaku fada wa 'yan committee ba" nayi dariya nace "'yan committee manya, wai dan Allah me kuke cewa in kun zauna meeting din ne? Yarinyar nan babu abinda ba tace min akan Amir ba amma yanzu in ka gansu suna kus kus sai ka dauka they are lovers" ta kara bata rai tace "lovers fa kika ce? Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni kuwa me zanyi da wannan? Dan Allah yanzu ke a ganin ki mun dace?" Nace "sosai kuwa" tace "to amma kuwa ya kamata kije ayi miki wankin ido" Amina dai dariya take yi tace "Moon kinga yadda kika koma kuwa? Shi yasa yanzu in dai kina guri Sultan ba sosai yake fahimtar magana in an yi masa ba. Oh Allah. My future husband where are you? Am waiting" dariya nayi sosai nace "to ke ki lallaba munir mana?" Ta zaro ido waje "a 'uzubillahi, kije ki wanke bakin ki please. Ai ni da kike gani sabo zan bare a leda. Munir shi kam in aka ce masa gwanjo ma ai an rufa masa asiri" ta jawo ni tazo dai dai kunnena tace cikin rada "gayamin, Sultan sabo ne ko tsoho" na ture ta ta fada kan gado, nace "you will never find out" Amira tace "ni fa har yanxu ban sayi gown din da zan saka ranar bridal shower ba, kowa ya gama shirin sa ban dani, bayan itama da akwai abubuwan da ban saya ba" nayi sauri na zauna kusa da ita nace "kinga kawata, kuje ke da Amina gurin Mommy ku lallabata ta barni in fita, sai muje in kaiki ki siyo, wallahi na gaji da zaman gidan nan. Tunda sunce rana ce basa so in shiga ai yau babu ranar ma" Amira tace "ni kinsan Mommy yanzu ba shiri muke yi da ita sosai ba, sai dai ko Amina" na juya gurin Amina nace "please yaya Amina, kije ki tambayar min" ta bata rai tace "to in kun fita me zaki siyo min?" Nace "duk abinda kike so" nan ta jera min uban list na abubuwan da take so in siyo mata, duk nace naji na yarda. Ta fita muka zauna zaman jira. Sai da tayi wajen minti talatin sannan ta dawo tana bata fuska, har na sare, sai kuma tayi dariya tace "an barki, amma ki saka dogon hijab da nikab" murna kamar in cinye Amina, dan ji nake gaba daya na tsani kaina saboda zaman gida. Na kira Sultan a waya na gaya masa zamu fita da Amira, yace "OK, in kun gama ki yi min magana, nima ina son zamu je wani guri" nayi shiru bance komai ba, yace "please say yes mana, yaushe rabon da in ganki wajan three days" nace "ina zamu je?" Yace "where it all began, ina so muje muci abinci a Hilton, anan na fara ganinki" kawai sai naji ba zan iya ce masa no ba, nace "OK" yana ta murna na kashe wayar. Da sauri na shirya muka fita, har wadanda suke palo basu gane ni ce na fita ba saboda na rufe fuskata, daya daga cikin motocin Sultan na gani na leka naga key a jiki kawai na shiga na tayar, Amira ta shiga muka tafi. A gate mai gadi kin budemin yayi sai da nayi magana yaji muryata sannan ya bude yana dariya. Wani supermarket tayi min kwatance, ni ban taba shigar sa bama ina dai ganinsa a hanya, ita ma tace bata taba zuwa ba an dai ce mata akwai kaya masu kyau a can. Muna zuwa muka yi packing, na chire nikab dina na ajiye a mota, muka shiga, karshen haduwa gurin ya hadu, kaya kam akwai su, ga shi komai a tsare, nan da nan Amira ta fara lodar kaya, ni kam ban sayi komai ba saboda babu abinda nake bukata, a wajen siyan gown tayi ta ruwan ido, nace "wallahi in ba zaki dauka ba zan tafi in barki, Sultan fa yace zamu hadu in anjima" ta tsaya ta saki baki tana kallona, tace "dama rakonin da kika yi na munafunci ne? Dama gurin sultan zaki tafi? Wallahi kinsan ba karamin aiki na bane yanzu in kira Mommy in gaya mata" nayi ta bata hakuri ina lallabata "ba wani gurin zamu je ba fa, abinci kawai zamuje muci a Hilton, kuma motar sa daban mota ta daban" tace ta hakura ba zata fada ba amma sai in barta ta gama siyayyar ta a hankali. Sai da ta gajiyar dani sosai sannan tace ta gama, muka tafi gurin biyan kudi. Da POS ta biya kudin, aka bamu receipt muka fito, muna shiga mota na dauko waya ta da niyyar kiran Sultan naji Amira tace da karfi "what?" Na juyo ina kallonta da waya a hannuna naga wayarta take dubawa, nace "ya akayi?" Ta nuna min screen din wayarta naga alert ne na siyayyar da tayi yanzu nace "menene?" Ta nuna min receipt din, ni har lokacin ban fahimci me take nufi ba, tace "duba ki gani, sun kara min 10k a cikin kudina" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amira, let it go, wallahi na gaji" tace "wallahi bazan hakura ba sai sun biya ni kudina, haka kawai dubu goma a banza, zo muje sai sun biya ni kudina" kamar zanyi wa Amira kuka haka na fita na bita muka koma ciki. A gurin cashier ta fara masifar sai an biya ta kudinta "How can you guys be so incompetent, ku kara min kudi har dubi goma?" Cashier kaman zata yi kuka tana bawa Amira hakuri amma Amira ta shafa wa idonta toka tace sai an biya ta, ni dai ina ta kallon agogo naga har karfe biyar, nasan duk inda six tayi Mommy zata kira ni tace in dawo gida, kuma gaskiya bana son missing date din mu da sultan, na karasa gurin rigimar naji cashier din tana cewa da Amira "madam kudin sun riga sun shiga account din shagon nan, ba zamu iya fitar dashi ba sai dai ki dau wani abun na kudin ki" Amira tace "ni na gama siyan duk abinda nake so in saya, babu abinda zan dauka kuma, kawai kudi na kawai nake so a bani" cashier tace "I can't do that madam, only the manager can do that, sai dai in zaki yarda in kaiki gurinsa inyi masa bayani sai ya biya ki kudinki" naga tsoro karara akan fuskar cashier din, daga alama tana tsoron manager din, nace "Amira ki zo mu tafi, ni zan biya ki 10k dinki" tace "wallahi bazan tafi ba chafdi, nasan sauri kike ki tafi gurin Sultan, in ya kira ki bani shi in yi masa magana" ni dai duk raina a bace, tausayin cashier nake yi, mistake tayi muka maybe zata iya loosing job dinta akan haka, da har nayi deciding inyi tafiya ta in bar Amira su karata amma sai na sake tunanin maybe in na bisu gurin manager din zan iya bashi hakuri kar ya kori cashiet din. Sai da ta fara yin waya ta tabbatar yana office sannan tace muzo muje, ta shige gaba muna binta a baya, ta hau stair muka bita zuwa hawa na uku, da kyar na karasa ina ta haki, taje bakin kofar tayi knocking, aka yi magana daga ciki, ta bude tayi mana alamar mu jira a waje sannan ta shiga ciki, Amira kam ba zata jira ba dan haka ta tura kofar ta shige ciki, nima na zo kofar na tsaya.
Chapter 99 · 0% Book details