Sashe 154
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yadda yake amma yanzu ya samu relief, please amma ki zo yanzu in ya ganki zai kuma jin dadi" na saki wayar na dora kuka na daga inda na tsaya, Sultan babu lafiya amma ni ina gidan mu bana tare dashi, kuma am 100% sure cewa ciwonsa dalilin maganganun dana gaya masa jiya da daddare ne, ni maimunatu na shiga uku, in wani abun ya sami sultan I will never forgive myself. My Darling Sultan. He calls me his love but I didn't act like love, bashi da kowa sai ni and I too pushed him away. What have I done? Amina ce ta sauko ta ganni ina ta rusar kuka ta karaso da sauri tana tabani tace "Moon lafiya? Jikin ne?" Ban bata amsa ba ta koma sama da sauri sai gasu tare da Mommy, Mommy hankalin ta a tashe tace "Moon lafiya" na share hawayena nace "sultan ne bashi da lafiya, yana asibiti" tace "kuma dai? Astagfirullah, Allah in laifi muka yi maka ka yafe mana". Da kyar Mommy ta matsa min nasha tea kadan, shima ina gama sha nayo mata amansa, tunda na samu ciki ban taba amai ba sai ranar nan. Ni duk burina inga Sultan in san halin da yake ciki, duk wani abinci da maganar ciki ne dani su biyo baya, a gurina lafiyar sultan itace a sama. Ganin yadda na tashi hankali na ya saka Mommy tace mu tafi tare da Amina, in an jima ita sai su zo tare da Daddy, ai kam ban jira komai ba nayi gaba, Amina ma a mota ta same ni, muna zuwa asibitin Amina ta kira number din amir ta gaya masa munzo, ya fito yayiana jagora zuwa dakin da sultan yake. Tun daga window na hango shi a kwance yana bacci. Nayi sauri na bude kofar na shiga. Shi kadai ne a dakin, babu riga a jikinsa amma an lulluba masa bargo har saman kirjinsa, gani nayi ya rame sosai, fuskarsa tayi fari tas. Duniya kenan, wai sultan ne ciwon kwana daya yayi masa wannan kayarwar. A hankali na karasa na dauki hannunsa na rike a nawa, muryata har ta dashe saboda kukan da nakeyi. Amina ta karaso ta dafa ni tana bani hakuri amma ko kallonta banyi ba. Ni kadai na san me nake ji a raina. Ba wai ciwon sultan din ne yake saka ni kuka ba, abinda yafi damuna shine kasancewar nice sanadiyyar ciwon nasa shine abinda yafi damuna. Ban san ma Amina ta fita ba sai dubawa nayi naga bata nan. Na fara yi masa magana a hankali "Sultan ka tashi dan Allah, menene hakan ne wai kai sai kace ba namiji ba zaka wani kwanta ka kama rashin lafiya. Kace ba zaka iya rayuwa babu ni ba, to ka sani nima bazan iya rayuwa babu kai ba, dan Allah sultan ka tashi kace ka yafe min, zuciya ta ba zata iya jurar ganinka a kwance ba Sultan zuciya ta bugawa zatayi in mutu, kaine rayuwata, kaini jinin jikina, kaine mijina kuma uban 'ya'yana. Sultan kayi hakuri, duk abinda na gaya maka wallahi ba da gaske nake ba. Dan Allah ka tashi, sickness doesn't suit you, ga babynmu kuma yana nemanka yana so ku gaisa." Na dora hannunsa akan mara ta na cigaba da cewa "ka ji shi ko? Kwanan nan zai fara motsi, he is going to grow up to be stronger than you, shi ba zai kwanta ciwo saboda sunyi fada da matarsa ba" na dawo da hannun sama na dora fuskata akai hawayena yana bin hannun nasa nace "my poor darling sultan, my sweetheart my honey, my angel my heartbeat, my life my happiness, my husband my babies Daddy" a hankali naga ya fara bude idanunsa, ya sauke su a kaina, they are the same most beautiful eyes I have ever seen, amma sun dan fada ciki kadan, murmushin gefen baki yayi min yace "indai wadannan kalaman za'a ke gaya min in bani da lafiya to kuwa kullum sai nayi ciwo" na saki hannun sa da sauri gaba daya na fada kansa na zagaye wuyan da hannayena ina sake wani sabon kukan yace "ouch, karki ballani mana baby girl, baki san kin zama 'yar lukuta ba yanzu?" Na dan dake shi kadan a kafada nace "kaine dai dan lukuti, mai kwanciya ya kama rashin lafiya kawai" ya saka hannu daya ya dago ni yana kallon fuskata yace "to ya isa haka kukan in ba so kike a baki gado a kusa da nawa ba" na tashi ina goge hawayena, har yanzu idonsa na kaina yace "you look terrible, da wasu jajayen kunburarrun idanuwanki" na dan harare shi nace "in kawo maka madubi ka kalli kanka kaga yadda ka zama?" yace "no, I don't want to see" ya daga bargon jikinsa, naga daga shi sai gajeran wando da singlet, yace "come here, zo in sammiki zazzabi na" ba musu naje na shige jikinsa na kwanta, ji nayi kamar wacce tayi tafiya nai nisa ta gaji sannan ta dawo gida, irin feeling din nan na finally I am home, na sauke ajjiyar zuciya na kara shigewa jikinsa ina jin zafin jikinsa yana ratsa ni, ya dora hannunsa akan marata yana shafawa a hankali, nace "am sorry sultan, for not telling you about the baby, I wanted to surprise you" murya can kasa yace "it is OK" a hankali yace "do you mean all what you just said. Da gaske abinda kika fada min a dakin ki ba da gaske kike ba?" Na girgiza kaina da sauri nace "wallahi ba da gaske nake ba. Am so sorry I said those words" yace "NO, I am sorry, ni nayi forcing dinki ai kika fada min hakan. Am sorry about what I did Nace "it is OK, ya wuce" mun jima a haka, na dauka ma ya koma bacci, sai naji yace "something weird happened da zu. Takawa yazo dubani" na daga kaina ina kallon fuskarsa da mamaki nace "what?" Yace "yes, i don't know me ya faru, amma ina tunanin Amir ne yaje ya gaya masa, sai dai bansan ya akayi yazo din ba, I just woke up and he was here, he held my hand and then he fainted" nace "fainted?" Yace "yes. Komai ya faru ne da sauri bansan menene ya faru ba, yazo nan, ya kama hannuna sai kuma ya suma, suka dauke shi suka fita dashi, sai doctor yazo ya saka na koma bacci, am just not sure whether da gaske abin ya faru ko kuma mafarki nayi" na mayar da kaina na kwantar a kirjinsa ina sauraron bugun zuciyarsa, na danyi tunani kadan akan abinda yace, we will have to ask Amir menene ya faru. Ba tare dana kalle shi ba nima na fara magana "something weird also happened jiya da daddare" nayi shiru kuma na kasa yadda zan fada masa, sai da yayi magana yace "what happened?" Sannan na cigaba da magana "Hafsat ta hadu da Ummeen ka a Riyadh" farko yi yayi kamar baiji me nace ba, sai kuma ya mike zaune da sauri, taking me with him, yana kallona fuskarsa babu alamar dariya yace "me kika ce?" Na jawo yawa ta na bude masa hoton mahaifiyarsa na mika masa, "Sultan wannan itace mahaifiyarka, you and zayed are cousins". A hankali ya karbi wayar yana kallon hoton, emotions fal a fuskarsa.