← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 190

Sashe 167

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tashe shi, ya na kallona nace "ta koro ni" har da dan rawarsa yace "uwa dadi" na dan fara kuka shagwaba, ya bude min bargo kusa dashi yace "shigo in rarrashe ki" na ajiye jakar hannuna na shige jikinsa, har da kara cusa kaina na zagaye shi da hannayena, a cikin kunnena yace "ana so ana kaiwa kasuwa ko?". Yau nayi baccin da banyi ba a cikin kwana goman da nayi a Riyadh, washe gari ma sai daki aka kawo mana breakfast. Kwanan sultan biyu a Riyadh su Hafsat suka koma England, naji babu dadi saboda na saba da ganin ta kwana biyu, har airport muka rakasu suka tafi. Sultan yanzu ya saki jikinsa sosai da ummeensa, dan har hira da dariya zan gansu suna yi tare. A ranar ne kuma Ummee tayi deciding zata nuna mu a gurin 'yan'uwanta. A ranar da daddare ummee ta dauke mu ta kai mu gidan su, gurin mahaifiyarta, mahaifinta kam ya rasu last two years. 'Yar dattijuwar tana ganin mu ta gane sultan, sai kuka, ta rungume shi tana ta godiya ga Allah, bata iya turanci ba dan haka da larabci take magana, sai dai abinda bamu gane ba ummee tayi mana bayani, tace " ashe da akwai rabon zan ganka Abubakar? Kakanka har yabar duniya yana nadamar rabaka da mahaifiyar ka da suka yi, muna neman afuwar ka ka yafe mana," mun jima a gurin ta sannan muka tafi, sai da tasaka muka yi mata alkawarin ba zamu bar garin ba sai mun dawo gurinta. Daga nan gidan uncle din Ummee muka tafi, wanda yanzu shine kamar head of the family n su, ni dai gaba na yana ta faduwa ina tunanin yadda zamu kare dashi tunda har dashi aka je aka dauko ummee, ga mamaki na sai na ga sun karbe mu sosai, ya jawo sultan jikinsa yace "Abubakar din mu ya dawo gida" matan gidan ma sosai suka karbe mu, duk sun san da maganar sultan, 'ya'yan gidan ne dai sai kallonsa suke suna cewa dama khairat tana da 'da? Yayi mana nasiha sosai akan cewa ba laifin khairat bane ba, laifin sune su iyayenta, su suka rabata da mijinta da 'dan ta saboda pride dinsu, ya nuna wa sultan kuma cewa nan gidan su ne, kowa anan dan'uwansa ne babu banbanci, da zamu tafi yace "ina sadiq din kuma? Shi yaushe zaizo?" Duk kannin mu bamu da amsar wannan tambayar. Muna mota zamu koma gida na yiwa ummee tambayar da ta dade a raina nace "ummee ni kuwa ina don inji me yasa likacin aurenki kika samu matsala amma lokacin auren zayed shi bai samu matsala ba" tace "da akwai dalilai. Na farko ni mace ce zayed kuma namiji ne, a gurin zaben miji maza sunfi samun freedom akan mata, saboda mu mata muna da weakness, nan da nan za'a yaudare mu shi yasa iyaye suka fi saka idonsu akan spouse din mata akan maza. Dalili na biyu shi zayed kusan rabin rayiwarsa a England yayi ta, dan haka sanda ya tashi aure in banda wadanda suka je nema mishi auren babu wanda zai ce yasan matar sa, bayan anyi auren ma a England din suka zauna bai kawo ta nan ba har sai da ta haihu, zayed is older and stronger than I was, dan haka babu wanda zai kalli matarsa yace wani abu a kanta, dalili na uku kuma the most important shine, tsakanin aure na dana zayed shekara talatin, three full decades, abubuwa da yawa sun chanza, duk yawancin masu akida ta tribalism a family din mu babu su yanzu sai kalilan, suma kuma sunyi sanyi sosai" na fahimci bayanan ta, na kara tambayar ta daya abinda yake zuciya ta, nace "to yanzu ummee idan Takawa ya dawo kina ganin ba zai samu matsala ba kenan?" Tayi shiru kamar bata jini ba, sai naji babu dadi a raina, I shouldn't have asked that, sometimes surutu na yana sakawa in wuce limit dina, nace "am sorry ummee I shouldn't have asked that" tace "Sadiq ba zai zo ba ai, da ace zai zo da tare zasu zo da sultan, tunda kika ga basu zo tare ba to ba zai zo ba". Ban kuma tambayar ta komai ba, sultan ma kuma tunda muka fara maganar baice komai ba. Washegari muka cigaba da zagayawa gida jen 'yan'uwan ummee, kuma Alhamdulillah muna samun karbuwa a gurin su, duk da few of them ne suka san da zaman sultan a duniya. Rannan mukayi waya da Mommy, tace min " Ibrahim fa yazo neman auren Amina a gurin Daddy" da murna ta nace "laaa, amma shine Amina ko ta kirani ta gaya min?" Mommy tace "ai Amina ta tayar da rigima, tace ita yanzu bata son shi" nace "me ya faru?" Tace "wa ya sani ne, taki gaya min komai, shi yasa na kira ki ko zaki tambayar mana ita, kinga yaron nan sai faman zirga zirga yake amma ko fita gurinsa taki yadda tayi ballantana suyi magana, kuma naga daddyn ku sosai yana son hada wannan auren" nace "insha Allah Mommy zanyi mata magana, ko menene ma zamu sani". Ina kiran Amina ce min tayi "babu wani abu da zaki gaya min in chanza mind dina fa" nace "kin san ma maganar da zanyi miki kenan?" Tace "ai kowa maganar da yake min kenan, tunda ni ce mai auren nasa kuma nace na fasa banayi ba shi kenan ba sai a kyale ni" nace "OK munji mun kyale ki kin fasa auren sa, to amma ko zamu iya sanin dalili?" Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "he doesn't love me. Duk abinda yake fada a baki ne kawai amma vai kai zuci ba" nace "ya zaki ce haka Amina? Wani abin yayi miki daya nuna miki cewa baya sonki?" Ta fara kuka tace "har yanzu Moon ke yake so, yana kulani ne kawai saboda muna kama dake, bana son in aureshi muyi ta samun matsala akan hakan" nan ta bani labarin abinda ya faru tsakanin su kwanan baya, nace "amma Amina tunda kika ga ya dawo ai ina ganin ya kamata ki saurare shi, ballantana kuma da maganar aure ya dawo, meaning he is serious this time around. Bansan menene a zuciyar Ibrahim ba amma nasan yayi nadamar abinda yayi wa matarsa ta farko, kuma yayi mata hakan ne saboda baya sonta, bana jin zai kuma making the same mistake a kanki, idan da baya sonki da gaske da ba zai ce zai aure ki ba" na jima ina bata shawarwari, da gaske Amina tana son Ibrahim dan haka na san zata sauko ne ta sake bashi second chance. Bayan munyi waya da Amina sai nayi deciding inkira Amira in ji ita ma ya take ciki, na kira ta ta dauka da murnarta, tace "Moon naje gidanki aka ce ba kya kasar ma, ina kuka tafi haka babu ko sallama?" Nace "munje saudi gurin ummeen sultan" tace "dama 'yar can ce?" Nace maka kawai "eh" munjima muna hira sannan tace "kanin ki yazo gurina rannan" da sauri nace "and?" Tace "I don't know Moon, sam banji wani abu a raina akansa ba. Amir ma yazo yana gayamin maganar aurensa, he said if am interested in him, bayan auren nasa we will talk. Moon nayi addu'ah nayi istikhara amma banji komai a raina game da Abbas ba, I tot I had something for amir amma tunda yayi min maganar aurensa naji na hakura" nace "yanzu me zakiyi Amira?" Tace "Moon alhakinku ne yake ta bina har yanzu, shi dama alhaki ai kuikuyo ne, me shi yake bi, happiness dinku dana katse muku shi ya saka zanyi spending the rest of my life in sadness" nace "ba haka bane Amira, shi ubangiji ai mai gafara ne, yana yafiya kuma yana son bayinsa masu nadama da neman gafara, sai dai laifin da kika yi ba ubangiji kika yiwa ba, mu kika yiwa, dan haka ubangiji ba zai yafe miki ba har sai mu mun yafe miki. Ni na yafe miki ba tun yau ba, amma abin tambayar shine, kin nemi gafarar Ibrahim? Shi kika fi cutarwa, shine yafi kowa shan wahala kuma har yanzu bai huta ba, shawara ta gareki shine, ki je ki nemi Ibrahim ki roke shi gafara, na tabbatar zai yafe miki, in kuma ya yafe miki, na tabbatar zaki ga chanji sosai a rayuwar ki, saboda hakkin wani baya taba barin mutum yaci gaba a rayuwa". 2 hrs ·
Chapter 167 · 0% Book details