Sashe 110
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
So...... The long awaited episode is here. Monday Washegari tun Mommy tana dakinta kafin ta fito naje na sameta, na gaisheta ta amsa. Sai kuma nayi shiru, ta kalleni tace "akwai abinda kike so ne?" Na danyi shiru ina tsoron kar ta hanani, tace "in ba zaki yi magana ba I have so many things to do" nace "Mommy dama zamu dan fita ne in an jima da Sultan" tace "in an jima kamar yaushe kenan?" Nace "kamar bayan magrib" tace "duk tsahon ranar nan bata ishe ku ku fita ba sai da daddare?" Nayi shiru a raina ina cewa 'shikenan, baza ta barni ba' tace "kun san dai gidan nan a cike yake da 'yan sa'ido da tsegumi bana don ku jawo mana wata maganar kuma" nace "to Mommy" tace "Allah ya kaimu, kuje, amma duk inda kukaje kar ku kai karfe goma" na ji wani dadi a raina, da sauri nace "thank you mother" ta harare ni, ni dai na tashi na fita tun kafin ta chanza ra'ayi. Bayan munyi break muka tafi saloon akayi mana gyaran gashi, kusan duk 'yammatan tare muka tafi har Hafsat, acan akayi mana manicure da pedicure, bamu dawo ba sai la'asar. Tun la'asar Sultan ya kira ni yace mu hadu acan. Naji haushin me ya saka ba zaizo ya dauke ni ba. Ina yin sallar magrib nayi wanka na dauko wani bakin material dina da aka dinka min a cikin kayan fitar biki na saka, riga da skirt ne anyi masa ado da golden, na gyara fuskata da light make up, ni kaina nayi mamakin irin kyan da nayi, na dauko golden mayafi karami nayi rolling, mayafin ya sauko ya rufe kirjina, na fesa turare na fita, dakin Mommy na fara shiga na ce mata na tafi, ta kalle ni sama da kasa tace "wannan mayafin yayi karami, ki daura dankwalin kayan sai ki saka babban mayafi, nace "yes mother" na koma dakina na dauko dan kwalin ina kallonsa, ni ban iya daurin dankwali ba shi yasa da wahala kagan ni da dankwali sai dai inyi rolling mayafi. Dole na nemo Amina, nan ta sakani a gaba wai sai ta kara min kwalliya wai wacce nayi tayi kadan, ta zauna ta tsara min kwalliya sannan tayi min daurin dankwalin shima, ina kallon kaina naga kamar ba ni ba, na juyo nace mata "Amina ba'a fara bikin ba fa, wannan kalliyar ai sai mutane suyi ta kallona" tace "to zauna kar mutane su kalle ki, ke da ba'a yi miki abin arziki" nace "thank you" ta kofar baya na fita, motar Mommy na gani a farko dan haka ita na shiga. Wajan 7:30 na isa Hilton, na kira sultan a waya yace "am sorry love, ki shiga nayi mana reserving table, gani nan zuwa, ki bani five minutes" na sake jin haushi nace "yanzu ni da nake mace ni zan je in jira ka? Maimakon ace already kana jira na acan?" Ji nayi bai wani damu da bacin raina ba yace "Sorry, yanzu ba zaki gane ba sai nazo tukunna" na kashe wayar ina tsaki a raina, na shiga ciki. Ina shiga naga wata waitress tazo ta tare ni ta tayi min jagora zuwa wani table a can corner din gurin, ga mamaki na sai naga the same table ne da muka zauna ranar da muka hadu. Na zauna akan the same seat din da na zauna ina kallon bakin kofa. A take na fahimci abinda sultan yake nufi, so yake abin yayi looking exactly kamar ranar da muka hadu, nayi murmushi, wannan shine dalilin da yasa yayi insisting in taho ni kadai kuma yace in shigo in jira shi, na kalli wajan naga babu abinda ya chanza. Ina zaune kawai naga waitress ta kawo min tea ta ajiye, na sake murmushi, wato ya tuno da tean da nake sha san da ya shigo. Na dauki tea din na fara kurba ina tina ranar, ranar bridal shower din Hafsat, Munir ya takura min, kawayen mu ma sun takura min da tambayar ina Ibrahim, I was so pissed up a lokacin na fito kawai na taho nan saboda ina son inji ni ni kadai, ashe destiny ne yake kirana. Na kai cup din tea din bakina zan kurba kenan na hangoshi ya shigo, kasa shan tean nayi na ajiye cup din tare da sakin baki ina kallonsa. Dark blue wandone a jikin sa three quarter da kuma light brown body hug short sleeved shirt, rigar tayi squeezing. Exactly kayan da suke jikin sa ranar da na fara ganin sa, gashin kansa a hargitse. Ya dan tsaya a bakin kofar yana karewa gurin kallo hannunsa a cikin aljihunsa. Tsayuwar da yayi exactly yadda na zana shi a project dina, except for murmushin da yake yi. Ya juyo ya kalli side din da nake zaune. Idon mu suka hadu, bansan sanda na mike tsaye daga zaman da nake ba. A hankali ya fara tahowa inda nake tsaye fuskarsa da murmushi, yace "Assalamu Alaikum" ban iya na amsa masa ba, yace "Mind if I join?" Sai a lokacin na rufe bakina na gyada masa kai ina dariya kasa kasa, maimakon ya zauna sai ya zagayo bayana ya rike min kujerata na zauna first sannan ya zagaya ya zauna a exact kujerar da ya zauna almost two years ago. Yana kallona yace "kinyi more than kyau, bama zan iya fassara yadda kike looking ba, kawai dai kinyi kyau" nayi dariya tare da dan shagwabe fuska nace "ba kai bane kace zakayi min special kwalliya shine nima kasa ni nayi kwalliya ashe kai abinda kake planning da ban" yayi dariya yace "kar dai kice kwalliya ta bata burge ki ba, da ita fa nazo na siye zuciyar ki" nace "waye yace maka a lokacin ka sayi zuciyata?" Yace "to yaushe na saya?" Na danyi tunani sannan Nace "nima ban sani ba. Kawai dai naga ta zama taka ce, ban masan sanda aka yi ciniki ba ballantana in san sanda na sayar maka" yace "hummm, ni kuma kinsan sanda kika sayi tawa? The first moment dana dora idona a kanki nasan cewa I am hooked for life, tun daga ranar kuma har yau ke kike controlling dinta" a lokacin aka fara serving din mu abinci, muka fara ci muna hira muna dariya, it's like mu kadai ne a duniyar, babu tunanin kowa babu tunanin komai a zukatan mu sai mu kadai. Yace "gwara fa ki samu kici abinci fa sosai, dan after today ba lallai bane ki samu damar cin decent meal ba kuma sai a gidan ki" nace "that goes also for you" yace "wa? Ni akwai wani abu da zai hanani cin abinci a kuwa? Amma nasan abinda zan ke yi miki in an fara bikin nan, kullum dura zan ke zuwa ina yi miki, kar azo a gama biki kuma ki kare da zuwa asibiti a bar ni da tagumi" na harare shi bance komai ba. Mun jima muna cin abinci sannan muka gama, ko bayan da muka gama ma aka gyara table din bamu tashi ba muka cigaba da hirar mu. Yana ta bani labarin friends dinsa da suka zo. A lokacin ne yake gaya min cewa 'yan gang bang duk sunzo, hotel daya duk suka kama suka sauka. Sai naji babu dadi, ni har na manta ma da zancen su, na dan bata rai, yace "what's wrong?" Nace "I thought ka rabu dasu, me suke yi kuma a bikin ka?" Yace "It's just biki kawai, kuma we have been friends shekara da shekaru, yanzu ba zai yiwu ace bikina yazo kawai sai dai suji labari ba" nace "why not? Ni dai sam bana son su wallahi, I don't want you with them" ya jawo kujerar sa kusa dani ya langwabar da kai yace "baby, I can't just send them away, babu dadi ai. Yaushe rabona dasu ma, yanzu fa duk mun girma kowa ya kama gabansa, in ba abu irin wannan ba bama haduwa. Yanzu kuma in aka gama bikin nan ba lallai ne mu kuma haduwa ba sai bikin wani kuma" na kalleshi cikin ido nace "ba zaka je bikin kowa ba" dariya yayi yace "yes ma'am, an gama. Please ki dan saki ranki mana" nayi murmushi yace "yauwa, ko ke fa" hannun da ya rike naji ya fara shafawa a hankali yana kallona, nayi sauri na kwace hannuna naja kujera ta baya, ina kallon fuskarsa yana so yayi dariya amma ya maze nace "wato tsokanata ma kake yi ko?" Ya dan bata fuska yace "ni din? Ni na isa in tsokane ki?" Nayi kwafa nace "as if I don't know you. Na san ka fa Sultan. Babu abinda ban sani naka ba" yace "really kin sanni?" Nace "yes, like the back of my hand. Na san ka ciki da bai" devilish smile dinsa ya fara, a take na fahimci so yake ya juya min magana ta, na bata rai, bai damu ba yace "yanzu da gaske kina nufin kinsan Sultan? Baby girl I let you know only what I want you to know. There is a part of me that you don't know, there is a part of me that even I don't know. Amma kar ki samu damuwa, we will soon explore that part very soon. But I think rannan mun dan buda page daya na wannan chapter din" ya sunkuyo saitin kunne na yace a hankali "In America" ji nayi tamkar kasar gurin ta tsage in shige ciki, wato abinda Hafsat ta fada gaskiya nr bai manta ba. Ina jinsa yana dariya kasa kasa ganin yadda fuskata tayi ja saboda kunya, ba tare da na kalle shi ba na saka hannu na dauki jaka ta na mike, yayi saurin rike hannuna na kwace na yi gaba da sauri kamar zan tashi sama. Da kyar na samu na dauko key din motar saboda yadda hannu na yake karkarwa. Ina bude motar yana karaso wa gurin "am sorry Love, ki tsaya in kaiki gida dare yayi" ban ko kalli inda yake ba na shiga motar zan rufe kofar ya rike yace "please ki bari in karki gida, I promise ko magana ba zan yi miki ba" har yanzu da akwai alamar dariya a muryar sa, ya zaiyi yayi wasa da wannan maganar? Amma