← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 190

Sashe 66

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanci tashi har lokacin bikin nuraddeen yazo. Nan muka shirya inamu2 sai Nigeria, Sultan ya riga mu yin gaba saboda wani aiki daya taso masa. Kwana biyu muka yi a Abuja muka wuce 'yalleman. Abinda nake tunani kuwa shi ya faru dani dan kowa muka hadu sai ya tambaye ni "yaushe ne naku bikin?" Ni dai kawai da dariya nake bin su. Munir kuwa kamar jela haka yake bina duk inda nayi, mutane kuwa da sun ganmu sai suce "our next amarya da ango" ni kuwa haushi kamar ya kashe ni. Kuma wai duk da muna tare amma haka nake ganin sa a gurin 'yammata, da karya da akuya kowa ya gani indai da skirt a jikinta to sai ya bita, sai dai in ya ganni ya maze kamar bashi bane ba. Sultan kuwa rikice min yayi wai lallai sai ya taho gurin bikin, a cewarsa ai shikenan sai ya gaida duk uncles dina kuma 'yan'uwana ma duk sai su gan shi, da kyar na hana shi, kuma nasan abinda yake damunsa shine yasan dole muna tare da munir, sau da yawa in muna waya in yaji muryar namiji sai ya tambayeni "waye wannan?" Sultan akwai kishi, ni har tsoro yake bani, na hana shi bina 'yalleman saboda bana son haduwarsu da munir dan ba za'a kwashe da dadi ba, na fison sai naje gurin iyayena formally kafin su hadu. Masha Allah anyi biki lafiya an gama lafiya, nayi ta yiwa 'yan'uwa rabon kaya kamar yadda na saba, nuraddeen ya gina gidansa mai kyau anan 'yalleman din inda nan zasu zauna shida amaryarsa, muna zuwa ganin gida kuwa na saba da amaryar dan itama mai son mutane ce, nan muka yi exchange din number. Ana gama biki uncle Aliyu ya kira ni palon waje, ni nasan kwanan zancen kuma na shirya. Ina shiga na ganshi shida uncle Rufa'i na gaishe su na zauna a kasa. Uncle Aliyu yace "maimunatu kinsan dalilin kiranki da nayi?" Na gyada kaina. Yace "to ya muke ciki?" Nace "Uncle da akwai wani, ina son kusa masa rana yazo ya gaishe ku. Na so ya gaida daddy tun a England amma kuma basu hadu ba, insha Allah daddy yana dawowa zai je ya same shi sai kuma yazo gurin ku kuma" Uncle Rufa'i yace "madalla, Allah ya sanya alkhairi. In yazo mun ganshi kuma zamu saka ayi bincike a kansa. Kin tabbatar shi kike so" na sunkuyar da kaina bance komai ba, yace "to Alhamdulillah. Shi kuma munir ya kuke ciki dashi?" Nace "Uncle shi Munir ai na riga na gaya masa, shi ne dai yaki hakura har yau. Ni dai uncle wannan din dai..... " yace "wannan din dai shi kike so?" Nayi shiru. Uncle Aliyu yace "kar ki damu Maimunatu, babu wanda zai miki auren dole, maganar munir zamu san yadda zamuyi da ita yadda ba za ta bata zumunci ba. Shi wannan da kike magana akansa ya sunan sa? A ina yake? Dan waye shi?" Nace "sunansa Abbakar Sadiq, A abuja yake" na danyi shiru sannan nace "dan sarkin Abuja ne" uncle rufa'i yace " ah, kice da princess muke magana" na rufe fuskata ina dariya. Uncle Aliyu yace "ban san 'ya'ya nawa ke ga maimartaba ba, amma nasan akwai wani dan sa fitinanne. Whatever dai ki kai shi gurin yaya ambassador din in ya dawo, tunda shi ya fini sanin kan Abujan. Allah yayi miki albarka" nace "Ameen, nagode uncle" .

Bamu bar 'yalleman ba sai da su daddy da yaya Walid suka zo tukunna, kwanan su biyu sannan muka koma Abuja gaba daya. Ranar da muka koma a ranar Sultan ya zo. Duk gidan a hargitse yake saboda ana general cleaning da ake yi dan haka a mota naga Sultan. Ina shiga da sallama yace "look what you have done to me" na kalle shi sama da kasa nace "me nayi kuma?" Ya nuna min wuyansa, baki ga ramar da kika saka ni nayi ba" nayi dariya nace "ni banga wata rama da kayi ba Sultan, gashi nan kayi wani fresh da kai har da ajjiye tumbi" da sauri ya shafa cikinsa, ganin yana kokarin daga shirt dinsa nayi sauri na dauke kaina ina dariya, yace "please dan Allah tumbi nayi?" Nace "wasa nake maka fa" ya wani bata fuska "amma wannan ai mugun wasa ne, kinsan kuwa yadda bana son tumbi? Amma ke kinga yadda ki ka yi kiba kuwa? Dama ku fulanin nan haka kuke da wayo,sai ku tafi ruga kuje kuyi ta cin dadi,kuci kaji,kuci zabbi, kusha nono" nace "kuma muci kwai ba. Karka damu indai 'yalleman ce har sai ka gaji da zuwanta" daga nan muka koma hirar yaushe gamo, na bashi labarin yadda muka yi da uncle Aliyu, yace "daddy fa?" Nace "tare da shi muke yanzu, zan tunawa mommy ta gaya masa, sai ya baka rana ka zo" shi kuma ya bani labarin ya samu maigirma galadima da maganar, yaji dadi sosai kuma yace in dai ance ya turo iyayensa to yazo direct ya gaya masa, shi zai yi masa komai. It's like everything is falling in place, matsalata daya yadda zanyi convincing daddy ya karbi Sultan, amma shima na samu solution, project din da na rubuta akan sultan zan bashi, in yaki yadda kuma ince masa yayi bincike.

Da daddare na samu mommy na tuna mata maganar Sultan nace ta gayawa daddy, tace zata gaya masa amma yace mata gobe zai koma England, da akwai wadansu takardu da zai cike amma ba zai dade ba zai dawo. Naji babu dadi amma we are ready to wait. Washegari tunda na tashi nake jin zuciya ta babu dadi. Irin feeling din da mutun yake ji idan something is wrong, nayi ta tunani ko zan tuno wani abu da nayi ba dai dai ba amma na kasa tunawa, sultan na kira na tambaye shi if he is alright, kuma daga muryarsa na gane bashi da wata matsala, jin yadda nake jin babu dadi yasa yace zai zo da yamma. Yamma nayi na shirya cikin doguwar riga purple mai ratsin pink nayi rolling pink veil, ina gama shiryawa sultan ya kira ni yace yazo, part din su ya Walid na saka aka bude masa ya shiga sannan na fita, ina shiga palon na tarar dashi ya bude fridge ya dauko drink yana sha, na tsaya ina kallonsa nace "wannan wanne irin bako ne? Daga zuwa zai bude wa masu daki fridge" ya juyo ya kalleni dan bai san ma na shigo ba, yace "waye bakon? Ni a gidan nan ai sai dai in sauki wadansu" na shiga na zauna tare da gaishe shi, ya amsa sannan ya zauna akan center table din gurin yana kallona, yace "so... What's the problem?" Nace "I don't know, kawai dai ina jin ba dadi ne, I just want to confirm if you are alright" yayi murmushin nuna jin dadin sa yace "am OK, I really am. Maybe akan tafiyar daddy ne kike feeling bad, tunda ba dade wa zaiyi ba ai babu problem ko?" Na kirkiro murmushi nayi masa. Nan ya zauna yake ta bani labarai da zasu saka ni farin ciki, in no time kuwa sai gani na ware ina dariya sosai. Yana cikin bani labarin Amir yayi wata budurwa kanuri sai kawai ji muka yi an bude kofar palon, a tare muka dago kai muka kalli kofa, ya Habeeb ne a tsaye, yadda muke kallon sa shima haka yake kallon mu, Sultan ya mike da murmushi ya doshe shi yana mika masa hannu, kallo daya yayi masa ya wuce shi ya karaso inda nake zaune a daskare, ya nuna sultan ya hannu yace "Moon me wannan yake yi a gidan nan?" Na bude baki amma na kasa cewa komai ganin yadda kamannin yaya Habeeb suka juye "I asked you a question, me wannan yake yi a gidan nan" murya na rawa nace "gurina yazo" na kalli sultan naga mixed expression a fuskarsa, na sake mayar da kallona kan yaya Habeeb wanda har yanzu ni yake kallo, yace "amma ya muka yi dake, you told me he is not your type that you are just using him for your project, ko? Rasa amsar da zan bashi nayi, na sake kallon Sultan, he is getting angry, nace "yaya Habeeb please don't do this" yace "don't do what? Ke fa kika cemin da kin gama using dinshi for the project zakiyi masa kafa, that's exactly what you told me, kuma yanzu kin gama so banga dalilin da yasa zaki cigaba da ganin sa ba, i see no reason why you should waste his time any longer" yana fadin haka ya juya ya koma gaban sultan ya tsaya yace "look man, this should be the last time da zan ganka tare da kanwata, you are not her type, ita da kanta ta fada, she was just using you for her project kuma ta gama, so ala raka taki gona" gaba ki daya kamannin sultan sun chanza, idonsa ya rikide ya zama jajawur, bai ce da yaya Habeeb komai ba sai ya karaso inda nake, da sauri na mike tsaye nace "Sultan listen to me, abinda ya fada ba haka bane, you of all people know I love you" ya Habeeb yace "bullshit" wani irin juyi sultan yayi ya danki wuyan ya Habeeb yayi baya dashi ya hada shi da bango, a zabure na karasa gurin na fara kokarin kwace yaya Habeeb nan da nan hawaye suka fara zuba a idona, hawayen da Sultan ya gani a idona ne yasa ya saki Ya Habeeb shi kuma duk da shakar da yasha amma bakinsa bai mutu ba, yace "kai kana tunanin kowa mahaukaci ne irinka? Waye kake ganin zai dauki 'yarsa ya baka?" Ya juyo kaina yace "ke kuma ki sani, am going straight to mommy" daga haka ya juya ya fice.
Chapter 66 · 0% Book details