Sashe 176
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fadi, nan muka tsaya muna kallon rana tana setting on the ocean, rana tana gama faduwa kuma sai duhu ya fara saukowa, nan take naji tsoro ya kamani, na duba naga we are in the middle of nowhere, babu gida gaba babu gida baya, na zaro ido ina kallon sultan nace "sultan yanzu idan shark yazo ya cinye mu fa" yace "kin san kuwa akwai sharks a ruwan nan ba" da sauri na kankame shi "na shiga uku, shikenan a teku zamu mutu, ko gawar mu ma ba za'a gani ba, wayyo Daddy" dariya sultan yake min sosai sannan yace "am just joking, babu shark anan" ni dai ban yarda ba nace ya mayar damu hotel din mu. Hankali na vai kwanta ba sai da naji kafa ta ta taka kasa tukunna. Muna zuwa sultan ya dau basket din kifin ya kai restaurant din gurin yace su gyaro mana shi su kawo mana tare da kayan barbeque. Da daddare kifin mu muka gasa muka ci a matsayin abincin dare. Da daddare na tashi na gabatar da salloli na roka wa Baffa rahamar ubangiji. Washegari ma Sultan bai barni na zauna ba ballantana inyi tunani ko kuka. Ya dauke ni muka tafi shopping. Kaya masu yawa ya saya mana ni da shi, bamu dawo dakin mu ba sai azahar, muna zuwa muka hada duk kayan mu da ba zamu bukata ba sultan ya dauka ya tafi shipping station din gurin ya bayar za'a kai mana har gida abuja. Tun da ya dawo yace min yau zai kai ni wani special guri muyi last dinner tunda gobe da safe zamu bar kasar. Muna sallar magrib muka shirya, ni kaina nasan munyi kyau, dama gashi na kara fari, in ka ganni ma ba zakace na taba shiga rana ba, ga kuma kibar ciki data kara min cika da budewa sosai, hips dina kamar wanda aka dauko aka dora min. Na saka riga da skirt bakake masu adon red, nayi rolling red veil wanda ya kara fito da hasken fata ta, kayan kuma tunda masu girma ne sai suka boye girman cikina. Sultan kuma suit ya saka ash, ya saka red shirt a ciki, ya taje kansa ya kwantar da gashinsa sai kyalli yake yi. Na zauna kawai ina kallonsa saboda kyan da yayi min. Golden brown skin dinsa tana reflecting duk fitilar data haska shi. Duk wanda ya kalle mu sai ya kara. Wani restaurant mukaje mai suna Ithaa, a karkashinin ruwa restaurant din yake, lifter zaka shiga tayi kasa da kai sannan sai kadan yi tafiya kadan a cikin wani glass corridor zuwa cikin restaurant din. Dan karami ne kuma shima duk da glass aka yi shi dan haka ji zaka yi kamar a tsakiyar ruwa kake, ni dai ji nayi kamar glass din zai fashe ruwa a shigo ya cinye mu. Gurin mutane 14 kawai yake dauka, amma fa abincinsu number one ne gurin dadi. Muna ci muna zuba soyayyar mu, dan gurin babu wanda ya damu da abinda wani yake yi. Bamu muka dawo dakin mu ba sai after ten. Muna zuwa muka kammala harhada sauran kayanmu mukayi sallah muka kwanta. Washe gari da sassafe jirgin mu ya tashi, na leka ta window ina kallon islands din nace a hankali "Adiós Maldives, sai mun dawo" sultan yana kusa dani yace "we will come back for sure". Jirgin mu yana gama settling a sama na cire seatbelt dina na tashi na dawo kan cinyar sultan na kwanta, ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, sama sama naji sultan yana cewa plight attendant ta kawo mana bargo, ya dan kwantar da kujerar sa ya lullube mu da bargo. Gaba dayan mu bacci mukayi, dan sai da jirgi zai sauka a malam Aminu kano international airport sannan aka tashe mu. Muna fita reception muka tarar da Mahmud abokin sultan na kano wanda sultan ya kira ya gaya masa zamu zo yana jiran mu. Na kalli agogo naga 9:30am. Ikon Allah, banbancin lokuta a tsakanin garuruwa kadai ya ishi mutum abin mamaki. Mun baro Maldives 8:30, munyi tafiyar at least five hours amma kuma munzo Nigeria at 9:30am, to ina four hours din suka tafi?. Sai da muka tsaya muka danyi takeaway din abinci kuma sultan ya chanza kaya zuwa manyan kaya da hula sannan muka dauki hanyar 'yalleman. Sai a lokacin baji mutuwar tana sake dawomin a raina, muna zuwa kofar gidan naga cikar mutane a gurin, dan gabaki daya garin ma kusan a cike yake da mutane tunda yau ne sadakar uku. Kafin muyi packing na kira Amina nace tazo mu shiga tare saboda bana son shiga ni kadai. Ina shiga naga kowa ido shabe shabe da hawaye ai nan take na fara nawa nima, sai kuma kowa ya dora daga inda ya tsaya, naje na fada jikin Inna muna yi tare. Uncle Aliyu ne ya shigo da fadan sa, yace "dama tunda na jiyo sabon kuka nasan sarauniyar kuka ce tazo, menene haka maimunatu? Ana kokarin ayi masa adduoi ke kina kokarin ki tayar mana da sabon kuka ko?" Nan take na hadiye kuka na, na dau charbi ina ja amma ban san me nake cewa ba, hawaye ne kawai yake bin fuskata ina kallon irin jama'ar da Baffa ya bari, ga dakinsa nan kamar zai fito daga ciki. Sai yamma sannan jama'a suka dan ragu, sai a lokacin na samu naga Hafsat wacce itama nata cikin ya fito ba laifi, Daddy kuwa sai da daddare sannan na samu nayi masa gaisuwa. Washegari wajan 12:00 na safe duk kusan jikoki mata muna palon hajja a zazzaune sai ga aike wai inzo dakin inna nayi baki daga abuja sun zo min gaisuwa. A raina nace 'lallai Yaya da kokari, wannan tafiyar aita yi mata nisa da yawa, tunda munyi waya ba shikenan ba?' Na kama hannun Zainab amaryar yaya Walid muka tafi tare. Amma ga mamaki na ina shiga palon sai ganin Ummee nayi a zaune akan kujera tana kallona, na saka hannu na na mitstsike idona wai ko ba dai dai na gani ba amma still ita dince, da nani, da matar galadima da kuma Saratu da Huda. Na karasa gurinta da sauri na fada jikinta, ta rungume nu tana cewa "careful, kar kiji ciwo kuma" na fara kuka tana rarrashina, da hannu ta saka take goge min hawayena, duk mutanen gurin kallin mu suke da sakakken baki, nace "Ummee how comes you are in Nigeria? When did you come? Did Sultan know you are here?" Ta share min hawaye tace "I will tell you all about it later. Now let's pray for the dead" ta ringa jero adduoi muna amsawa. Na aika Zainab ta kira Hafsat, sai gasu tare da Amina, suka zo suka gaishe su. Haka mutane suka ringa shigowa suma gaishe da Ummee, wasu ma tsegumi ne yake kawo su. Hajja ta fara mita "idan nace sayar da yaran nan akayi sai ace min ba haka bane ba, in uta Hafsat ance balarabe ta aura to ita kuma maimuna fa? Ita data auri bahaushe menene hadin ta da larabawa?" Daga Mommy har Inna babu wanda ya tanka mata, ni dai ina nannade a jikin ummee ina lussafin ya akayi ta baro saudiyya ta taho Nigeria har tazo 'yalleman. Sai bayan sun ci abinci sun huta sannan na dauki waya ta na zagaya baya na kira sultan, yana dauka nace "kasan da zuwan Ummee kuwa?" Yace "wacce Ummee kike magana akai" nace "Ummee dai tamu, gata nan a dakin Inna" dariya yayi kadan yace "Moon rasuwa fa akayi, why are you making jokes" na koma na leka dakin ta taga na ganta akan sallaya tana addu'ah nace masa "wallahi va tsokanar ka nake ba Ummee ce suka zo da su Nani daga Abuja" ya kashe wayar, na koma dakin still ina kallonta, tayi min murmushi ta nuna min kusa ta ita alamar inzo in zauna. Da la'asar su Nani suka koma, amma banda Ummee da Huda, Ummee tace "sai gobe daddyn sultan zai zo sai mu tafi tare" ni dai kawai kallonta nake da mamaki. Sai bayan mun raka su mun dawo sannan nace mata "Ummee sultan fa bai san kinzo ba" tace "eh, bai sani ba" nace "dan Allah in kira shi ya ganki?" Ta dan dungure min kai tace "wai ke nan mai miji ko?" Na langwabe kai ina rokonta, tace "Ok, da daddare sai yazo mu gaisa, yana ina?" Nayi mata bayanin yana gidan nuraddeen, a can ya sauka. Sai daga baya mutane suka gane Ummee surukata ce, sai kuma aka koma gulmar yadda muke da ita babu alamar sutukuta. Mommy sosai ta karbi Ummee suna ta hirar su, daga dukkan alama tasu tazo daya, ballantana nasan Mommy da son 'ya'yanta, soyayyar da taga Ummee tana nuna min ma kadai ya isa itama ta so ta. Da daddare bayan an watse sai few mutane, na kai Ummee palon waje, na kira sultan. Yana shigowa tsayawa yayi yana kallonta ya kasa magana, ta tashi ta rungume shi da sauri "my little love, how was the honeymoon?" Muka kalli juna ni da sultan, tace "do you guys enjoy Maldives?" Tayi dariya ganin yadda mukayi da fuskokin mu ta zauna muma muka zauna muka saka ta a tsakiya tace "kun dauka wai bamu san inda kuka tafi ba? Maldives kukaje, kuka sauka a hotel din soneva jani, cabin no 12" sultan ya bata rai "saka wa kikayi aka bi mu?" Tayi dariya tace "bani na saka ba, babanka ne, tun sanda kace masa zaku tafi ya aika wani a can Riyadh ya tsaya a airport yaga wanne plight kuka hau ya gaya masa, sannan ya kira Maldives din ma ya saka wani ya jira ku a airport yaga saukar ku kuma ya biku har hotel din da kuka sauka sannan ya gaya masa" sultan ya mike tsaye ya fara zagaye dakin "shikenan yanxu mutum bashi da private life kenan" ina dariya a raina ina cewa "sultan har yanzu America bata barka ba". Ya dawo ya zauna yana kallonta yace "to ya akayi kika taho Nigeria kuma keda akayi banning from leaving Saudi" Tace "They can't stop me from coming to Nigeria if am married to Nigerian". Lol, we have new amarya in town.