← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 190

Sashe 16

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na jima ina karanta takardar hannuna ina maimaitawa. Amma Ibrahim baka yi min adalci ba, yanzu me kake so ince maka? Yes or No? Ni dai nasan koda wasa bazan tunkari Hafsat da sunan neman shawara ba. Na saka karanta takardar kamar me saka ran ganin ganin chanji a rubutun. Tabbas handwriting dinsa ne, kuma kamshin turarensa ne. Na kai ido na kan number daya rubuta a kasan takardar lokaci daya na haddace ta. Na ninke takardar na mayar cikin littafin, a lokacin Hafsat ta shigo tana hamma, ta kalleni tace " kasa, a gidan ma sai kinyi baccin wuri" nayi dariya ban bata amsa ba saboda I am not in the mood. Ina kallonta tana shirin wanka na dauko littafin Ibrahim na fara karantawa saboda nasan sa idon Hafsa, tana shiga wanka na rufe littafin na saka a kasan filona na kwanta akai. Har ta fito ta shirya ta kwanta banyi bacci ba ina ta sakawa da warwarewa. What should I do? Ni nasan ina son Ibrahim har cikin rai na, wannan bani da tantama akai, amma nasan abu ne mai wahala kasancewar mu tare. Bani da problem da daddy sai mommy nake ji, kallo daya idan tayi min sai na gwammace ban taba ganin Ibrahim ba, Inna da baffa da kawunnai na na 'yalleman zasu iya haka rami su binne ni akan su barni in auri Ibrahim. Ina son family na fiye da komai dan haka maganar inbijire musu ma bata taso ba. A daya side din kuma inna cewa Ibrahim no nasan ba wasa yake yi ba akan maganar barin school din mu, kuma bazan sake ganin saba har abada sai dai wani ikon Allah. Anya zuciya ta zata iya daukan haka kuwa? Anya zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba kuwa? What should I do? A haka bacci barawo ya dauke ni. Cikin bacci nayi mafarki wai gashi muna tafiya da family na a mota a nata hira ana dariya sai naga Ibrahim yana tafiya a kasa shi kadai, sai yayi mun murmushi nima nayi masa, mun wuce shi kenan sai ya fara bin mu da gudu yana kirana a haka har muka yi nisa na daina ganinsa. Na farka a firgice ina addu'ah. Na jima a zaune ina ta maimaitawa a raina cewa 'it is only a dream, you will see him again". Ina tashi na daga pillow na na dauko letter dinsa na je na bude locker din textbooks din mu na saka ta acikin wani biology textbook na mayar na rufe.

Hutun sam banji dadinsa ba, kona saki raina da na tuno da takardar da take cikin locker dina sai inji gaba na ya fadi. Rannan na fito daga wanka ina shirya wa kawai na kalli mudubi sai na fara wondering what happenned to me? Yaushe har nayi girman da zan fara tunanin soyayya? Yaushe daada ta daina goyani? Ni ba shekaru ba ni ba girman jiki ba amma na dora wa kaina wahala? Na tuno daddy da yadda zai zama disappointed in yaji labarin abinda yake faruwa. Da wannan tunanin na saka kayana direct na tafi part din daada, luckily na tarar tana bacci, banyi wata wata ba na dau wayarta na saka number din Ibrahim. Sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka yace "hello" da muryar bacci. Dif duka nepar jikina ta dauke na tsaya sororo da waya a kunnena na kasa magana. Ya sake cewa "hello, who is there?" Still na kasa magana kuma na kasa kashe wayar. Ina jinsa yayi tsaki yana kunkuni kasa kasa ya kashe wayar. Na durkushe a kasa ina jin haushin kaina. What has Ibrahim done to me? I can't even say no to him.

Tun daga ranar ban sake gwada kiransaba kuma har hutun mu ya kare banyi making decision ba. Ranar da zamu koma haka kawai naji ni kamar marar lafiya, mommy duk ta dauka bana son komawa ne har tana yi min fada. Kamar tasan abinda yake raina tace "Moon zaku cigaba da lessons din da wannan copper din?" Na kalleta truthfully nace "I don't know mommy" tace "ok in zaku cigaba ki tabbatar kuna zuwa tare da Hafsat, I don't want you staying alone with him" na sunkuyar da kaina kasa nace "ok mommy". Da haka mukayi sallama muka tafi.
Motar mu tana packing na hangoshi a jikin staff room, ya jingina da jikin katanga ya rungume hannayensa a kirjinsa, idonsa akan inda motoci suke ajiye students. Muna fitowa Hafsat ta matso kusa dani tace "wow, he can't wait to see you Moon, can he?" Nayi banza na rabu da ita ina fito da bags din mu, na sake matsowa tace "au ba zaki bani answer ba? Ko saina fada da karfi ya Habeeb yaji? Maybe they can even be friends" na ajiye jakar hannuna nace mata "what exactly do you want to know?" Ta tsare ni da ido tace "is it going to be a Yes or a No?" Nan take naji daci a bakina, so Hafsat ta karanta letter din Ibrahim kenan, amma ban taba ganin mutum mai sa ido a rayuwata irin Hafsat ba. Na tsaya kawai ina kallonta ita kuma tana yi min murmushin mugunta. Ya Habeeb ya zagayo yace "Hey, zaku fara fadan tun kafin in tafi ko?" Hafsat tace "No, yaya Habeeb ba fada muke ba, we are just catching up akan harkar makaranta" Ya Habeeb ya kalleni yace "is she maltreating you, I know Hafsat can be bossy at times" na kalle shi kawai sai naji kwalla tazo min, na rungume shi sai kuka, nayi kuka na mai isata sannan na sake shi, sai a lokacin na lura ashe fada ya ke yiwa Hafsat ita kuma sai rantse rantse take yi cewa sharri nake yi mata babu abinda tayi min. Su duk basu san me yake damuna ba. Ina gama share hawayena na dauki handbag dina na wuce hostel. Ina zuwa hostel ko gado na ban gyara ba na dauko wani pink handkerchief dina mai ratsin purple, na duba locker dina da dauko permanent marker na zauna nayi rubutu a jikin handkerchief din na barshi ya bushe sannan na ninke na fita daga hostel din da sauri. Hanyar staff room na nufa ina tafiya ina share kwalla a ido na, a hanya muka hadu da Hafsat ta fara yi min bala'in na taho na barta da daukan kaya, ban kula ta ba na wuce na bini da kallo. Ina shiga staff room na ganshi yana arranging desk dinsa ya dago da sauri yana kallona, ya taho kamar zaiyi min magana na wuce shi na ajiye handkerchief din hannuna a kan desk dinsa na juya na fita. Ina kallonsa yayi sauri ya dauki handkerchief din sai naga murmushi ya baiyana a fuskarsa. Abinda na rubuta masa shine "I DON'T KNOW WHAT THE FUTURE HOLDS, BUT I WANT TO FIND OUT WITH YOU" na juya na koma hostel.
Washe gari muna shiga class naga students a tsaye a gaban board suna karanta wani abu, na buda su na shiga, rubutun Ibrahim ne akan board "THEN I WILL BE THE HAPPIEST MAN ON EARTH" na juya naje nayi zamana a seat dina. Ina zama sai ga Hafsat ta zo ta tsaya a gaba na tace "then it is a yes" na kalleta cikin ido nace "yes, it is"

Wow, then the battle has begun.

Episode eighteen: what's Next?

Hafsat ta tsaya saroro tana kallona. Sannan ta sunkuyo saitin fuskata tace "yanzu ke Moon kina ganin har kinyi girman da zaki fara soyayya? Har kina ganin kin isa ki yanke wa kanki hukunci? Har kina ganin kin san menene dai dai menene ba dai dai ba?" I was ready for her dan haka ko gezau banyi ba nace "7 years ago, sanda nace inna girma ina so in zama neorosurgeon murna kuka yi ta tayani kuna cewa nayi making right decision, ta yaya kuma yanzu zaki ce min ban isa in making decisions ba? I know what I am doing I just need u to support me please" Tayi min wani kallon wulakanci tace "lallai yau na tabbatar baki da hankali Moon" tayi tafiyar ta ta zauna. Nayi shiru ina tunani, lallai Hafsat bata gama sanina ba har yau.
Mutane da yawa suna cewa I am a genius, amma ni ban yarda ba, na san dai ina da brains kuma I am going to use it here. Tabbas nasan ina son Ibrahim amma hakan bazai sa in barshi yayi meddling with my life ba. Dole zanyi mana katanga tsakani na dashi. I said yes to him saboda bana son ya bar makarantar kamar yadda yayi threatening amma hakan ba yana nufin I will let him romance me ba. In dai har yana sona zai jira ni har in gama sec sch sannan we will see what will happen.

Na gama tsara komai yadda nake so ya kasance. Abu na farko shine; ba zan ke bari muna kebewa ni da shi ba alone. Dan haka ana yin break na tashi a class nayi announcing cewa ina gayyatar duk wanda yake da ra'ayi zamu ke karatu tare. Kusan rabin class din suka ce suna so, nan muka zauna muka tsara timetable ta karatu, kullum da akwai subject din da zamukeyi, za muke fara wa 3pm mu gama 6pm. Nayi inviting duk class din ne saboda nasan kullum dole wani zai zo, baza mu kasance daga ni sai Ibrahim ba.
Abu na biyu da nayi shine na fito da duk textbooks dina na jefa akan desk dina yadda babu yadda za'ayi mutun ya zauna akai, no more sitting on the desk tactic. Iyakacin sa sai dai ya tsaya a gaban board ya gama abinsa ya fita. The next thing da nayi shine ana tashi a school na tafi gurin HOD na Islamic studies na kai masa complain cewa ina so a raba mana class din islamiyya ni da Hafsat, ina so a mayar dani B class. Da kyar na samu ya amince shima saboda muna mutunci dashi sosai tun jss1. Nasan in Ibrahim ya fahimci abinda nayi he will be mad but I am ready for him.
Chapter 16 · 0% Book details