← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 190

Sashe 131

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

min lessons din musabaka lokacin soyayyarsa ta kara karuwa a zuciya ta, I guess na kasa boyewa ne har na nuna masa, abinda yace min shine ya daina yi min lesson din sai dai in zamu ke zuwa tare dake, I was so pissed up nace na fasa musabakar ma gaba daya, yaje ya gaya wa pc ta kira ni nace eh na fasa, maimakon ya lallasheni ya bani hakuri sai cewa yayi da pc ai kema zaki iya, a rabu dani a saka ki kiyi kawai. Ranar ne na fara gaya miki maganganu kuma daga baya sai naji babu dadi, it is not your fault that you get everything I wanted. It was not your fault that he loves you not me. Kuma shima banga laifinsa ba, dan babu wanda zai samu someone like you ya ajiye ya dauki someone like me. It was my fault that I couldn't control my heart. Bayan nan yazo har cikin class ya fada a gaban kowa cewa baya so na, duk da dai 'yan ajin basu san dawa yake ba. Na fahimci cewa ya gaya miki abinda ya faru tsakanin mu, amma ga mamaki na sai naga hakan bai sa kin chanza min komai ba, saboda ke din ta daban ce. Daga lokacin har adduah na ringa yi ina rokon Allah ya cire min shi daga raina. Bayan munyi graduation ne rannan kika gaya min cewa he left you sai nan gaba zai dawo, a raina nayi adduar Allah yasa ba zai dawo ba saboda bana son abinda zai bata kawancen mu dake. I never thought nima zan sake ganinsa. Kawai rannan bayan kun tafi England sai gashi a kofar gidan mu, na dawo daga makaranta kawai na ganshi a tsaye yana jirana. He looks so happy to see me, and my stupid heart thought cewa guri na yazo, it was very stupid of me to even think that. I was so happy. So excited. Sai bayan da na shigar dashi gida muka gaisa sosai sannan ya gaya min cewa ke yake nema. It hurt me so much then. I don't even know ma yaushe na kirkiri karyar cewa kinyi aure na gaya masa. Sai da naga expression din fuskarsa sannan na fahimci me nayi. It was already too late to gi back, maganar ta riga ta fito babu yadda zan yi in mayar da ita" ta fara kuka sosai "nasan cewa abinda nake ba dai dai bane ba amma na kasa dawowa baya in warware karyar da nayi. Na saka akayi min fake IV na kai masa. I kept telling myself cewa it will be better in na raba ku din yadda ba zan ke ganin sa ba ballantana har in bata friendship din mu dake. I kept telling myself cewa you will soon forget about him. Wani lokacin kuma in gayawa kaina cewa ko na bar ku ma ba lallai bane daddy ya yarda ya aura miki shi. Ita karya in ka yi ta sau daya to ka ringa karawa kenan kullum saboda kayi covering waccan da kayi. Haka na ringa yi masa karya akan ki. At first na yi masa karya ne saboda I was angry cewa baya so na, daga baya kuma na cigaba dayi masa karya saboda in boye waccan karyar da nayi dan inye saving friendship din mu. Abinda nake so ki fahimta shine, ban raba ki da Ibrahim saboda ni ina so in same shi ba, a'a na raba ku ne saboda ina gudun in yi asarar kawancen mu" na goge hawayen da yake ido na. Yana daga cikin ginshikin imani mutum ya zama mai yarda da kaddara, mai kyau ko marar kyau. Amira have always been a good friend to me. Ina jinta a raina kamar 'yar'uwata. Na mika mata hannu nace ta tashi ta zauna akan kujera. Ta zauna tana ci gaba da kuka. Nace "it's OK. Komai ya wuce in sha Allah" Amir ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna yace "To kuma kukan na menene, ba tace ta yafe miki ba? Sai kinje ki sa wa kanki wani ciwon kuma". Muna nan tare dasu Sultan ya shigo, ya rike kugu yana kallon su "shikenan kuma mutum bashi da damar ya dan fita waje sai an zo an cika masa gida. Dole ma muzo mu bar kasar nan wallahi". Sam sultan bai nuna wa Amira yasan wata magana a tsakanin mu ba, ya zauna ya saka su a gaba ita da Amir da tsokana nima ina tayashi. Muna tare dasu har aka kawo lunch aka kai dining na yi musu bismillah, Sultan ne na farkon tashi wai dama yunwa yake ji, a raina nace 'acici'. Muna shiga na dauko plates da spoons, sultan na fara serving, na duba naga farar shinkafa ce da miyar kaji, sai brown macaroni. Na zuba masa shinkafar ina cikin zuba masa miyar naji yace " khulsum bata tafi ba kenan" na tsaya da abinda nake ina kallonsa naga bani yake kallo ba abincin yake kallo, na bata rai nace "me kace?" Still bai kalleni ba yace "khulsum nace bata tafi ba kenan, this is her cooking" na ajiye serving spoon din hannuna na rike kugu ina kallonsa nace "ya akayi ka san cewa this is her cooking?" ya jawo warmer din ya nuna grated carrot din da aka barbada akan shinkafar yace "this is her signature, in dai tayi abinci tana barbada carrot akai as her signature" sai a lokacin ya dago kai yaga yadda na rike kugu na hade rai ina kallonsa yayi dariya yace "common, da ina yawan cin abincinta, she is a chef, the carrot is just her signature kamr yadda mai zane yake signing a kasan zanen sa dan ya nuna cewa shi yayi" na kara hade rai ganin yayi comparing ita as a chef da shi as an architecture, ya gane abinda nake nufi yayi sauri ya gyara yace "ko kuma yadda likita yake signing a kasan prescription dinsa dan asan shi ya rubuta" a zuciye na jawo plate din abincin da na zuba masa na juye a cikin warmer din na kwallawa Hassana, daya daga cikin yarana kira, tana shigowa nace duk ta kwashe abincin ta tafi dashi gurin su su cinye. Na juya na kalli Amir da Amira da suka saki baki suna kallona kowa da cokali a hannu, sultan mamaki ne ya hana shi magana, sai daga baya yace "common Love, yunwa fa muke ji, yanzu kin bayar da abincin me zamu ci kenan?" Nayi hanyar kitchen ina cewa "I will cook you something" ya taso ya biyo ni, yace "yaushe kika iya girkin?" Nace "I will learn today" ina shiga kitchen na jawo apron na saka na kunna gas na dora tukunya da ruwa. Sultan ya karaso kitchen din ya rungume ni ta baya yace "relax, am sorry, dan nace na gane girkin ta doesn't mean anything, nasan ta iya girkin amma ban taba son taba, nasan baki iya girkin ba amma am head over heal in love with you. Ki bari Amir ya fita ya sami mana abinda zamu ci" Amira ce ta shigo kitchen din ya dan sake ni kadan ta karaso tace min "me za'a dafa?" Sultan yace "no ku bar shi kawai bara mu fita mu siyo" tace "ai kafin ku fita ku dawo ma yaci ace mun gama koma menene, yadda gidan nan yake da nisa zuwa gate ma aiki ne" ya dan tsaya yana kallona, na daga kafada yace "OK, cook us something simple" yana fita Amira ta bude freezer, ina kallonta tana fitowa da abubuwan da take bukata, ta miko min nama tace "wanke wannan" ina tabawa naji shi duk kankara nace "yayi sanyi da yawa ba zan iya tabawa ba" ta tsaya tana kallona kawai, sannan ta dauki naman ta zuba masa ruwa ta koma tana gyara kayan miya. Na dauko waya ta na kira Mommy, tana dauka na shagwabe murya kamar zanyi kuka nace "Mommy ban iya girki ba" tace "au ke da baki san baki iya girkin ba sai yanzu? Babu yadda banyi dake ba akan koyon girki ki ka ki, dama nasan wannan ranar tana nan zuwa. Yanzu me kike so inyi miki?" Nace cikin sanyin murya kamar abin tausayi "Mommy Asma'u zaki bani" tace "ita ma'un an gaya miki toy ce da zance kawai na baki ita? Besides nima ina bukatar ta tunda office aiki yayi mana yawa ba zama nake a gida sosai ba. Cooking classes zaki shiga ki koya ki ringa yi da kanki. Su yaran da aka baki duk basu iya girkin ba suma?" Nace "Mommy ni ba zan iya cin abincin su ba, Sultan ma haka. Professional cook muke nema. Kuma Mommy wallahi sultan ba zai barni in shiga cooking class ba" tace "to ai kuwa kwa kare da siyan abinci" nace "Mommy please" ta dan jima sannan tace "zan tambayi ma'un inji ko zata zo, amma da sharadi, in tazo zama zaki ke yi kuna girkin tare da ita kina koya, yaran naki suma duk su ringa koya, duk lokacin dana bukace ta zan aiko ta dawo gida in baki koya ba kafin nan matsalarku ce" cikin murna na fara yi mata godiya, bata saurareni ba ta kashe wayar. Zuciya ta naji tayi min fari tas, duk wani takaicin khulsum da girkin ta na manta dashi. Nima zan koyi abincin nan dai in huta.
Chapter 131 · 0% Book details