← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 190

Sashe 72

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gari ya waye ina kwance a gado naji an bude kofar dakin, nayi sauri na mike zaune, mommy ce ta shigo sai mai aiki a bayanta, a ajiye tray da abinci a ciki ta fita, na ce "mommy good morning" ba tare data kalleni ba tace "ki tashi ki ci abinci" daga haka ta fice tare da rufe kofar. Tunda nazo duniya yauce rana ta farko da na gaida mommy bata amsa ba, It feels really bad, wato haka Sultan yake ji kenan tunda yazo duniya. Ban kalli in da abincin yake ba na cigaba da kwanciyata har zuhr tayi. Ina zaune a kan sallaya aka sake bude kafar, wannn karon Asma'u ce, tajiye trayn hannunta ta kalli na safen da ko taba wa banyi ba. Tace "mai sunan daada ki ci abinci mana? Ya za'ayi mutun ya zauna babu abinci?, murmushi kawai nayi mata na cigaba da jan charbi na. Bata dade da fita ba aka sake bude kofar, wannan karon mommy ce ita kadai. Ta zauna akan bedside drower sannan tace "tashi kici abinci" banyi mata musu ba na dauko trayn ba bude na zuba abincin na fara ci, sam ji nake abincin babu taste amma haka nake hadiyewa da kyar, ina gama cin abincin ta dauke trayn ta fita ta rufe kofa. Sai da akayi la'asar sannan ta dawo, yanzu ma ina kan sallaya ta zauna akan bedside tace "zo nan" na mike naje gabanta na tsugunna, tace "tashi ki zauna a kan gado, ba musu na tashi na zauna ina kallon kasa tace "Maimoon ina so ki gaya min gaskiya, in kika yi min karya abinda zanyi miki sai yafi wanda nayi niyya" a hankali nace "to mommy" tace "tun yaushe kuke tare da Sultan?" Nace "tun bikin Hafsat" tace "shekara daya kenan?" Nace "eh" ta gyada kai tace "good, yaushe ne kuma ya fara koya miki shaye shaye?" Da sauri na dago kaina ina kallonta "mommy nice fa, Moon ce fa mommy" ta dauke kanta tace "I don't know you anymore, Moon din dana sani ba zata bi saurayi gidan giya ba, Moon din dana haifa na raina ba ita ce wannan a gaba na ba. Just answer the question" sai yanzu sannan hawaye suka zo idona, na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ta sake cewa "just answer the question, tun yaushe yake kaiki bar?" Nace "wallahi mommy ban tana shan komai ba. In baki yarda ba kisa ayi min drug test" tace "OK, ina son ki gaya min komai and I mean everything da ya faru tsakanin ku" nan na fara bata labarin tun haduwar mu dashi a abuja har komawar mu England shima ya bi mu, sannan na bata labarin bina da yayi America da duk abinda ya mu kayi a can amma na cire labarin abinda ya faru ranar da zan dawo, oh no I can never tell her that, sannan na bata labarin dawowar mu Nigeria da plans din mu na kai maganar gaban iyayen mu, na gaya mata kuma abinda ya faru tsakanin su da yaya Habeeb da kuma bin Amir da nayi zuwa gurin sultan. Na kara da cewa "mother, he is not a bad person, he is a good person. Dan Allah ku tsaya ku fahimce shi" ta yi ajjiyar zuciya tace "you are not as smart as we all thought you are, moon he is playing you. Mutane irinsa abinda suke yi kenan, su samu yarinya kamarki su yaudare ta su bata mata rayuwa suyi dumping dinta. Tunanin ki bai taba baki cewa duk wadanda suke zuwa suke baki labari akansa shi ya ke turo su ba?" Na girgiza kaina nace "mother this is for real, wallahi da gaske ne, I trust him" ta mike tsaye tare da ajjiyar zuciya tace "Maimoon, you are no longer allowed to see or talk to Sultan in dai na isa dake" na fado daga kan gadon na rike kafafuwanta, ina kuka nace "Mommy kiyi min rai, mommy wallahi in kika raba ni dashi mutuwa zanyi, purnish me duk yadda kike so dan Allah karki raba mu" ta kwace kafarta taje bakin kofa tace "you really have no idea about your situation. Already munir yayi waya 'yalleman ya gaya musu abinda ya gani jiya, it is just a matter of time kafin baffa ya turo a bincika masa, so you really understand why I want you as far away from sultan as possible? He is who he is and you are who you are" ta bude kofa ta fita ta barni a durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha. I can only imagine yadda Hajja zatayi ta yawo da maganar nan. Allah ne kadai yasan irin karyar da munir ya kara akan abinda ya gani din. Na dafe kaina daya fara sara min.

Washe gari da assuba mommy ta shigo da breakfast a hannunta ta saka ni a gaba na ci, sannan tace in tashi inyi wanka, naje naji na fito na tarar ta ajiye min kaya har da underwears akan gado tace in saka, a raina nace ina zamu je kuma da sassafen nan? Ni dai na shirya na zauna ina kallonta, ta kalleni cikin ido tace "you are going on a journey, ke da daada, ba za ku dawo ba har sai kin manta da Sultan" na durkushe a gabanta nan da nan na fara kuka ina rokonta, ko saurare na bata yi ba, tace it's for my own good, a karshe dai nace mata "mommy, ina son magana da daddy" tace "mun riga munyi maganar dashi, shine ma ya bada wannan shawarar" mommy is a bad liar, in dai tayi karya sai an gane, ina kallon fuskarta nasan daddy bai san maganar tafiyar nan ba. Zata tura ni wani gurin da Allah ne kadai yasan inane, ba tare da sanin daddy ba ballantana wani dan haka Allah ne kadai yasan ranar dawowata. Allah gani gare ka.

When everything seems lost, always have hope. Have faith that God is planning something for you. Believe that God's plan is the best.

Episode Fifty Two : The Journey

Munir, ni mai nayi wa Munir a rayuwa? Kawai dan nace bana son sa? Ai ba yaudarar sa nayi ba, tun farko na gaya masa bana sonsa kuma ni ban saka shi lallai sai ya jirani ba shi yaga dama. Na gane mugun nufinsa so yake yayi ruining reputation dina yadda lallai koda na dage bana donsa sai iyayen mu sun tilasta min na aure shi. Ni kam ban masan me zanyi ba in aka aura min Munir. Ina nan a durkushe a gurin ina hawaye har ta dawo, daga bakin kofa ta tsaya tace "let's go" na kuma rike kafarta "mommy dan girman Allah ki bani wayata, wallahi ba sultan zan kira ba, mommy dan Allah ko Hafsat ki barni inyi magana da ita" ta hade rai tace "am not stupid Moon, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba, in dai har zan baki waya menene amfanin kaiki wani gurin. Tunda har kika san ki fita daga gidan nan ki tafi gurin saurayi ai zaki iya komai moon. Moon daga bar fa aka dauko min ke kina warin giya. Moon kece fa har da daukar saurayi ku tafi wani kasar. Duk abinda nayi miki har kina da bakin rokona mercy. In dai har ni na haife kiba zaki kara ganin yaron nan ba har abada. Kuma in dai har ni lawyer ce sai na tabbatar yaron nan yayi jail time saboda ya zama darasi a gare shi da sauran masu hali irin nasa" sautin kukana na kara, tashin hankali na shine jin tace sai ta rufe sultan, sanin halin mommy i know she is not bragging. "Mommy kiyi min rai dan Allah karki taba Sultan, dan Allah ni kiyi min komai, laifi nane, ni naje gurinsa bashi yazo gurina ba, he needs help mommy not more suffering. He will loose himself completely idan ya rasa ni kuma aka rufe shi" ta karaso inda nake tana kallona, ni kuma na sunkuyar da idona kasa tace "did you have sex with him?" Na dora hannayena aka na rusa wani sabon kukan tace "answer me, did you? How many times?" Kuka kawai nake na kasa bata amsa, mommy ta riga tayi nisa duk abinda zance mata ba zata saurare ni ba. Tace "ba zaki amsamin ba sai na kira Walid ya nakasa min ke tukunna? Did you?" Na girgiza kaina da sauri "no mommy, never" ta jima tana kallona kafin tayi deciding gaskiya nake fada, tace "tashi mu tafi" nace "ban dau kaya ba ai" tace "no need, na hada miki already" na juyo na kare wa dakina kallo, sannan na fita ta biyo ni a baya. Babu kowa a palo, haka ta tisa keyata muka fita waje, daada na gani a tsaye gaban motar mommy, baya mommy ta saka na ta rufe kofar ta zagaya zata shiga drivers seat. Yaya Habeeb na hango ya fito daga part dinsu da gajeran wando da singlet, daga dukkan alama jogging zai fita, tsayawa yayi da sakakken baki yana kallon mu muna shiga mota, wannan shi ya tabbatar min da cewa suma basu san da wannan tafiyar ba, da sauri ya karaso "Moon ina zaku je" bani da amsar da zan bashi sai kawai na daga masa hannu alamar 'oho' ya karasa gurin mommy tun kafin ya karasa ta watsa masa harara, ya juyo ya sake kallo na sai kuma ya juya da sairi yana kwalla wa ya Walid kira, tun kafin ya shiga part din nasu mommy ta ja motar dan haka ya tsaya kawai yana kallon mu, munje gate na juyo naga ya Walid ya fito shima ya tsaya yana kallon mu fuskarsa dauke da mamaki.
Chapter 72 · 0% Book details