← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 190

Sashe 138

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nufin kina ganin zaki iya handling koma menene, amma ina so ki sani, as much as I like sultan I like you more, amma hakan ba wai yana nufin bana son sultan ba, ina sonsa sosai kuma ina alfahari da abinda kike yi a rayuwarsa, but be very careful my daughter, your picture with a gun almost give me a heart attack, idan kinga abin yana kokarin yafi karfin ki just give me a call, ko ina kasar nan ko bana kasar nan I will always be there for you. Idan wani abin ya same ki a dalilin auren nan I will never forgive myself, saboda ni na amince ba saka ki a ciki duk kuwa da sanin sarkakiyar da take ciki. Zan yi yawa da Sultan din shima zamuyi magana dashi." A hankali nace "to Daddy, nagode. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" yace "Ameen" na jima a zaune a gurin bayan mun gama wayar, kawai sai naji hawaye suna zubomin bansan dalilin su ba. A duniya mutum bazai taba samun mai sonsa ba sama da iyayensa, kuma babban dace a duniya bayan kasancewarka musulmi shine samun iyaye na gari. Iyaye na gari sune ginshikin samun rayuwa ta gari. Amina Tun ranar da tabar gidan Moon kullum sai ta kira number din Ibrahim sau ba adadi amma har yanzu bai dauka ba. Wani lokacin sai ta ji haushi ta jefar da wayar tace yayi wa kansa, amma kuma in ta huce sai ta kuma dauka ta kira shi, still no response, kuma karin jin haushinta shine number din tana shiga dauka ne ba'a yi. In tayi tunanin ta rabu dashi kawai sai kuma ta yi tunanin to ko bashi da lafiya ne, he might be dying on a hospital bed ko kuma alone a gida for all she knows. Ranar dai da akayi kwana biyar ta shirya da niyyar yau dai zata yi finding out ko ma menene ya same shi. Ta shirya tsaf ta hau sama dakin Mommy ta gaya mata zata fita tana son siyan wasu 'yan kaya, Mommy ta bata kudi tace kuma ta dauki driver amma kar ta dade. Tana shiga mota ta gayawa driver supermarket din Ibrahim, tasan dole zata samu labarin sa a gurin staff din gurin. Tana shiga ta danyi 'yar siyayyar ta kadan tazo gurin cashier ta biya sannan tace "please manager dinku kuwa yana nan? I am a friend of his ina son ganinsa" matar ta danyi jim tana tunanin me zatace sannan tace "eh yana nan ma'am, amma I don't know ko zai ganki, in kina da number dinsa ki kirashi mana in yace ki shiga kinga shikenan" Amina tace "ai number din nasa bata shiga ne, I would have call him, just ki je kice masa Amina tazo tana son magana dashi" matar tayi saurin girgiza kanta "am sorry ma'am, bana son inyi laifi" Amina tace "OK, just show me ina office din nasa yake sai inje ni kadai" nan matar tayi mata kwatance. Ta hau saman benen da aka nuna mata tana kallon kofar offices din da suke a jere, a kofa ta uku taga an rubuta "manager" sai data sauke ajjiyar zuciya sannan tayi knocking, babu response, ta sake yi sannan ta murda hannun kofar, ga mamakin ta sai ta ji kofar a bude, ta tura ta shiga da sallama. Yana zaune akan kujerar sa yana danna laptop din gabansa. Looking as handsome as ever. Ya dago idanunsa ya dora akanta, sanyin AC office din ya saka ta dan rungume hannayenta tana shakar daddadan kamshin sa. Bai ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanu. Ta dan kirkiro murmushi ta karaso gaban desk din sa, tace "Can I sit down?" Nan ma babu amsa, ta dan zauna tana kallon haduwar office din, ta na feeling nervous, damn you Moon da kika saka nayi miki wannan alkawarin. Kamar daga sama taji yace "What do you want?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa, babu dariya sam a fuskarsa, zuciyar ta taji ta fara tafasa, a ranta tace "what am I even doing here? In Moon tana son ta san halin da yake ciki she should come by herself" ta mike tsaye cikin zafin rai tace "am sorry I bother you" da sauri ta fice daga office din kamar zata tashi sama. Har ta fara sauka stairs din sai kuma tayi wani tunani, wannan mutumin kar fa ya dauka wai ta damu da shine ya saka take ta kiran sa a waya kuma har tazo office dinsa, da sauri ta koma saman, ba tare da sallama ba ta kuma bude kofar ta tsaya a bakin kofar tana kallonsa tace "ba wai dan na damu da kai nake kiranka a waya ba, ba kuma wai dan na damu da kai nazo office dinka ba har da zaka wulakanta ni. Moon ce ta roke ni inyi haka, har kasa ta durkusa akan guiwoyinta sannan na yarda zan yi, dan haka save your arrogance for her not me, ka tattara duk wani guntun wulakancin ka and shove it up your handsome face" tana gama fadin haka ta buga kofar da karfi ta juya ta tafi tana murmushin jin dadin ta rama wulakancin da yayi mata, sosai taga yadda expression din fuskarsa ya chanza sanda ta ambaci sunan Moon, ita wannan soyayyar mamaki take bata. Ji tayi ya bude kofar da sauri ya biyo ta, bata waiga ba taci gaba da sauka stairs din yace "Amina wait please" ta juyo tana kallonsa tace "saboda me? Saboda kaji nace sakon Moon ne zan gaya maka? Wait, ya akayi ma kasan sunana? Ka yiwa kanka ai, zan koma in gaya mata kace baka son jin komai daga gareta" ta juya ta cigaba da sauka, tana jin sa ya biyo bayan ta yana kiranta amma bata waiga ba, tana gama sauko wa tayi hanyar fita, sai da takai bakin kofa sannan ta juyo, bai biyo ta ba, the mighty manager ba zai zubar da ajinsa a gaban yaran sa ba. Ta fita ta shiga mota suka koma gida. Tana ta tunani a ranta, wannan wacce irin soyayyace haka, wanne irin so ne Ibrahim yake yiwa Moon, duk da cewa kiri kiri moon ta zabi Sultan, duk irin abinda ya faru ranar nan amma har yanzu mare ambaton sunan ta ya chanza masa lissafi. Ita kam bata jin zata iya yiwa wani irin wannan son. Ta fara tunanin abinda ya faru ranar da aka kai Moon, bata taba tsammanin wai maganar zata wuce shikenan kamar ba'a yi ba, amma Moon wai ko Daddy ta hana a gaya wa, wanne irin so ne haka itama Moon take yi wa Sultan?. Tana shiga gida ta dauko wayar ta, 6 missed calls from Ibrahim. Dariya tayi a bayyane, she got him right where she wants him, sai ta rama duk abinda yayi mata, sai ta ja ajinta san ranta. Kwanan su biyu a haka, ya turo messages sunfi a kirga, ya kira ta sau ba adadi amma bata kula shiba. Ranar kwana na ukun dai ya gaji, zuciyar sa tana ta yi masa sake saken menene sakon Moon din da Amina zata bashi? Is she OK? Kar dai ace wani abun ya faru da ita ranar nan bayan tafiyarsa. Yana tashi daga office ya biya ta restaurant ya ci abinci daga nan gidan su Moon ya wuce, direct ya doshi gate din gidan yayi horn, mai gadi ya leko ya ga motar bai bude gate din ba ya fito ya taho gurin sa, ya sauke glass din sa yana kallon mai gadin yace "Amina tana na kuwa" mai gadi yace "eh tana nan" ya cigaba da kallonsa, Ibrahim yace "zan iya shiga in ganta ko kuma in tsaya anan za'a kirawo min ita?" Da da sauri mai gadin yace "a'a bara a bude maka ka shiga ciki" still amma yana kallon Ibrahim, sai kuma ya dan yi gaba kamar zai tafi ya kuma juyowa ya kalli Ibrahim, sai ya dawo da baya, yace "ni kuwa bawan Allah kamar kaine ka taba zuwa nan a shekarun baya ka bani sako in bawa maimunatu" Ibrahim yaji yawun bakin sa ya bushe, yace "eh nine baba, ashe baka manta ni ba" baba habu ya washe baki yace "yauwa har naji dadi, ai bana manta fuska, in dai naga mutum ko mai tsahon shekaru ina iya gane shi" ya danyi shiru sannan yace "abinda yasa kaga na tambaye ka shine, bayan na bata sakon, lokacin zasu tafi England, ta bani wata katarda tace in baka. Tunda kuwa suka tafi kusan kullum sai ta kira ni ta tambaye ni kazo? Daga baya ni nace mata ta hakura ta daina kira, in kazo da kaina zan kira ta in baka ita kuyi magana" Ibrahim ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya runtse idonsa yana jin zafi a ransa, baba habu ya cigaba da cewa "ina fatan dai ba wajan ta kazo ba yanzu ba, saboda anyi auren ta satin daya wuce" Ibrahim ya bude idonsa yace "No, ba wajanta nazo ba, wajan Amina nazo, nasan anyi bikinta. Amma baba takardar da ta baka tana nan kuwa har yanzu?" Baba habu ya danyi tunani yace "ai shekarun ne da yawa, amma zan duba maka, inna ganta kafin ka tafi sai in baka" daga nan ya bude wa Ibrahim gate ya shiga sannan ya tafi kiran Amina. Tun da Ibrahim yayi packing idonsa yake rufe yana jin dachi a ransa. She trusted that he will come back shi yasa har ta bayar da letter tace a bashi idan yazo, amma bai zo din ba, he imagine her pain, calling day after day tana tambayar ko yazo? Amma kullum amsar shine bai zo ba. Tace masa five years tayi tana jiran sa, a cikin five years din nan bata taba yin ko da saurayi ba, shi take jira duk kuwa da tasan cewa shi yayi aure. Ya dafe kansa da yaji yana sara masa. Ya bude ido yana kallon gidan, wannan shine karo na biyu daya shigo gidan nan, ya tuna abubuwan da suka faru a zuwansa na farko, a karshe ya juya ya tafi ya bar hawaye yana zuba a idon maimunatu. Ji yayi duk ya tsani kansa. Ta madubi ya hango ta ta fito
Chapter 138 · 0% Book details