← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 190

Sashe 34

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rannan muna zaune a daki muna ta shirin kwanciya bacci, sai muka ji knocking a bakin kofa, Amina tace "waye?" Yaya Habeeb yace "ni ne, I am coming in" Hafsat tace "don't come in, we are naked" kawai ya bude kofar ya shigo yana dariya. Hafsat tayi sauri ta ja bargo ta rufe cinyoyinta, Ya habeeb yayi dariya yace "yanzu Hafsat ni kike wani rufe jiki dan na shigo daki? Da yaushe kika gama shan dummy?" Hafsat ta murguda masa baki tace "i was doing you a favor da nace kar ka shigo, now you are doom for life" yana kallonta yace "bangane ba" tace "yanzu ka shigo kaga tsiraicin mu, zaka fara tunanin duk mata irin mu ne, zaka yi ta searching ka kasa samun kamar mu at the end zaka kare da auri saki" duk muka saki baki muna kallon ta ya Habeeb cikin mamaki yace "Hafsat yanzu rashin kunyar ki dama har ta kai wannan stage din? Do you even think you are beautiful? No wonder har yau baki taba yin saurayi ba" Hafsat tace "Na dauka cewa kayi yaushe muka girma, kuma yanzu kana maganar har yanzu banyi saurayi ba, ashe mun girman kenan" rasa amsar da zai bata yayi, ya juya ya fice. Ni dai ina tsaye da towel a jiki na, Amina tace "Hafsat mai yasa kika yi masa rashin kunya" Hafsat tace "Na gaya masa kar ya shigo, specifically na gaya masa cewa we are naked amma ya shigo, nima banji dadi ba da nayi masa rashin kunya amma so nake yasan cewa we are matured enough yanzu, it is not right ya ke shigo mana daki anyhow" maganar Hafsat tayi zafi amma she is right. Ko 'yan biyu ne ku karewar brother and sister da akwai privacy da kowa acikin ku yake bukata. Samari bai dace su ke shiga dakin 'yammata ba, haka zalika suna 'yammata bai dace su ke shiga dakin samari ba, in dai har bada wani uziri ba.

Sai da muka gama second year din mu sannan na samu zuwa Nigeria. Kawai sai naji bana wani murnar zuwa saboda dama wanda nake saka ran zan gani a Nigeria yanzu na tabbatar is no longer mine. Da muka je Nigeria sai muka zama abin kallo a gurin mutane saboda yadda muka zama, ni kaina nasan a cikin wadannan shekaru biyun ba karamin chanji na samu ba, fata ta wani mugun laushi da santsi, nayi kyar kiba ta komai ya cika yayi bulbul, ga kuma uwa uba wayewa, dadin mu daya mommyn mu is very strict, bata son shigar banza, dan haka koda English wear mu ka saka to sai mun rufe jikin mu, bama taba fita waje da matsatstsun kaya. Samari kuwa tun a makaranta har a gida haka muke ta fama dasu, daga ni har Hafsat har Amina babu wacce take kula samari, dan ni a England zobe na saya na saka a ring finger dina, duk wanda yazo naga yana kokarin ya fara nuna min soyayya sai in nuna masa zoben in ce "am married" duk da dai wadansu suna fahimtar karya nake yi amma dole su hakura tinda babu yadda zasu yi dani. Muna zuwa Nigeria ma abinda ya faru da mu kenan, dan ma samarin nan suna dan jin tsoron tunkarar mu amma duk da haka da akwai masu courage, in sunzo nakan tsaya in basu hakuri ince anyi mana miji, Hafsat kuwa ko kwallon inda suke bata yi balle ta kulasu. Rannan Amina tace "ni kam Hafsat zan ga saurayin ki a duniyar nan" nace "gaskiya kam, duk wanda Hafsat ta bude baki tace tana so to ya kamata azo kallonsa" bata kulamu ba saboda in miskilancin Hafsat ya tashi mu din ma bamu ishe ta kallo ba.

Satin mu biyu a Abuja muka tafi 'yalleman. Murna a gurin su inna ba'a magana. Tana ganin mu tace "lah, England din ce haka? Anya ba za abar karatun nan ba kuwa? Kar kuzo wata rana mu kasa gane ku saboda kun zama irin 'yan can" na rungume ta nace "we miss you too innarmu, in mun tashi tafiya next time tare zamu tafi dake saboda kullum kike ganin mu dan karki manta mu" ta rungume ni itama tana cewa "na ki wayon, salon mu tafi da baffa ki kwace min shi da wannan kyan ka kike yi kullum bayan ni tsofewa nake yi" Amina tace "kai inna, ai kamar ku daya ke da Moon"

Naji dadin zuwan mu 'yalleman dan ba kara min missing din su nayi ba. Nan da nan fara bin 'yan'uwan mu gida gida ina gaishe su kuma kowa sai na kai masa kayan tsaraba, har kayan da na siyo musu suka kare na fara diban kayan mu ina rabarwa. Nan take samari kuwa su kace dawa Allah ya hada su ba da ni ba, babu shiri na koma daki kusa da Hafsat na zauna na daina fita, amma duk da haka ban tsira ba saboda har gida ake aiko wa wai ana sallama da maimuna, Hafsat tana ta yi min dariya wai wa ya aike ni futa yawo a garinnnan.

Rannan muna zaune a compound din gidan sai daddy ya shigo zai gaishe da mutan gidan kamar yadda ya saba. Inna ta aika ni na dauko masa carpet a cikin gida aka shimfida masa, duk ya gaishe su mu kuma muka gaishe shi. Sai Hajja tace "ni kuwa muhammadu ina son magana da kai, da Adama naso muyi magana da ita amma sai nayi tunanin kar ta ce bakin ciki nake yi wa jikokinta" ina jin haka nasan maganar mu zatayi masa. Daddy yace "to hajja ina jinki" tace "anya muhammadu yaran nan ba za kayi masu aure haka ba? Yanzu ka debi yara mata ka tafi dasu kasar waje wai da sunan karatu? Wanne karatu mace zatayi wanda ya wuce na dakin aure? Ni dai a shawara ta ka dawo dasu nan, ga 'yan'uwansu nan sai a hada su auren zumunci, ga nuraddeen nan shima in karatun ne ai yayi, ya gama degree dinsa a BUK, ga balarabe, ga manniru duk babu abinda suka rasa. Ni tsoro yaran nan suke bani musamman wannan tsagerar" ta fada tana nuna Hafsat, "yanzu ma tana mana kallon wulakanci ballantana nan gaba in tafi haka? Ai cewa zata yi bata taba ganin mu ba" daddy yayi ajiyar zuciya yace "to hajja, ni ban taba tunanin hana su aure ba, ko yau suka fito da miji aure zanyi musu" Hajja tayi sauri tace "yo ai indai wadannan ne ba zasu fito da miji ba, ai indai ana so ayi wa wadannan aure to sai dai a fito musu da miji" daddy ya sake cewa "shikenan Hajja, yanzu abinda za'ayi ki kira su samarin ki ce su zo suyi magana da su Hafsat din, indai sun fahimci juna a tsakanin su to na miki alkawarin baza mu bar garin nan ba sai da auren su aka".

Chapdi, lallai da rabon Hafsat zata saka wa garin wuta gaba daya. Lol.
I love you all. Thanks for following

Episode Thirty Two : Munnir

Daddy yana gama fadin haka ya mike yayi musu sallama ya fita. Gurin kowa yayi shiru banda Hajja dake ta sambatun ta ita kadai. "Yauwa, yanzu na ji magana, amma abar yara suna so sufi karfin mutane? Yanzu kuwa zan kira 'yan samarin nan duk abinda suke yi su bari su taho gida, azo ayi ta ta kare" tsam mommy ta mike ta shige dakin da muke sauka in munzo, Hafsat ta tashi ta bita a baya, nan Hajja ta sake daukan magana "zasu je suyi kulle kullen yadda za'a fasa, ai kuwa wannan maganar kamar anyi ta an gama ne, yo gida bai koshi ba a bawa jeji?" Duk abinda take yi inna bata tanka ta ba, aikin gabanta kawai take yi. Sai da na gama taya inna juye furar da ta dama a jug na kai kitchen na saka a fridge sannan na shiga dakin mu. Dariya naji tana neman kubucemin saboda ganin yadda akayi upside down da dakin, duk su biyun sun dage suna ta loda kayan mu a akwatinan mu, wadansu kayan ma ba'a ninke suke ba haka ake watsa su. Mommy idonta ya kada yayi jawur, Hafsat kuma fuskarta kamar an aiko mata da mutuwa. Bance musu komai ba suma haka, na samu guri na zauna na zuba wa sarautar Allah ido, nan da nan mommy ta bani aikin kwashe kayan kwalliyar mu da underwears din mu. Muna cikin aikin da bansan na menene ba sai ga inna ta shigo, da mamaki take bin mu da kallo "yanzu Bintou shine kika tisa 'ya'ya a gaba kuke hada kaya zaku gudu?" Maganar guduwar da inna tayi shi ya saka dariyar da nake kunshewa ta fito, Hafsat ta bini da uwar harara hamkar idanunta zasu fado. Mommy ta yar da rigar da take ninkewa ta zauna dabas a bakin gado tace "inna yanzu zama zanyi a yiwa yaran nan auren dole, dududu nawa suke? Girman jiki ne fa kawai dasu amma ba wani shekarun kirki ne dasu ba ballantana ace sunyi kwantai za'a raba wa 'yan'uwa, wai Nuraddeen, har da Mannirun da baya ganin kowa da gashi" inna tace "ke waya ce miki za'ayi musu auren dole? Ya kike abu ne kamar ba kisan halin mijin kiba? Ni dai abinda kunne na ya jiye min yace shine 'za'ayi auren in dai har yaran sun amince a junansu' to menene kuma abin tashin hankali a ciki. Ke kinsan waye Muhammadu, kinsan babu yadda za'ayi yayi wa 'ya'yansa auren dole, amma yanzu kina diban su kuka gudu cewa zai yi ba kya son 'yan'uwansa. Ki zauna kiyi musu addu'ar zabin alkhairi shi yafi miki" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.
Chapter 34 · 0% Book details