← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 190

Sashe 127

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari bamuyi missing sallar assuba ba kaman jiya, Sultan ne ya fara tashi, sai da yayi alwala sannan ya tashe ni shi kuma ya fita masjid, ya jima bai dawo ba har nayi sallah na dan taba karatun al'qurani sannan nayi morning azkar dina, ji nayi duk na gaji da kwanciya, I want to do some work, na tashi na gyara dakin na wanke toilet, na dawo palo ina cikin gyarawa ya shigo, ya tsaya yana kallona "wato matar nan kin warke ko? Shine zaki kama aikin da assubar nan ko?" Nace "na gaji da kwanciya ne kawai, I want to do something" ya fara tahowa yana min murmushin mugunta yace "You want to do something? I have got something for you" na ajiye duster din hannuna na fara ja da baya ina jin tsoro har cikin raina dan na warke amma ban manta azabar da nasha ba. Nace "Sultan Allah ban gama warkewa ba, dan Allah kayi hakuri wallahi na daina aikin zan koma in kwanta" ya karaso in da nake yace "really baki warke ba? Can I see?" Nayi saurin girgiza kaina nace "you are not a doctor how will you know if a wound is healed or not?" Yace "am not a doctor but ni mijin doctor ne, dan haka believe me I will know" idonsa kawai na kalla nasan kona roke shi it will be to no avail, jikina har karkarwa yake yi saboda tsoro, me yasa nayi aure ne wai? A kunne na ya rada min "believe me, it will not hurt". And it didn't, at least not as I expected. Yana cikin bacci na zare jikina na tashi, a hankali na lallaba na saka kayana na fice, da sauri na karasa dakina ina shiga nayi locking kofar, finally nazo dakina after two days, da sauri sauri na gyara dakin duk da ba wani datti yayi ba, na shiga toilet na shiga shower ina wanka, at last zanyi wanka without sultan standing and watching. Na fito na zauna na shirya a tsanake cikin atamfa ruwan hoda, nayi 'yar kwalliya kadan na fesa turare na fito. Ina fita palo na tarar da wata tsohuwa a zaune a kan carpet da wadansu 'yammata su biyar daga can bakin kofa, ina fitowa duk suka mike tsaye kansu a kasa, 'yammatan kamar harda tsoro a fuskarsu, sai da na zauna sannan suka durkusa suka fara gaisheni daya bayan daya, na saki fuskata sosai na amsa musu. Babbar matar ce ta matso tace "ranki ya dade, Allah ya taya miki, Allah ya dora ki akan makiyanki duniya da lahira, Allah yaji kan magabata, Allah kuma yasa albarka a zuriya" nace "Ameen" ta cigaba da magana "ranki ya dade ai jiya ma munzo, muna nan har magriba bamu samu ganin ki ba. Dama mai babban daki (yaya) ce ta turo mu, tace tana gaishe ki sosai, kuma tace duk mu shidan nan mu dawo nan gurinki mu zauna muke yi miki hidima. Ni sunana Gaji, tun asalin kakanni na bayi ne a wannan gidan, anan aka haifeni anan na girma nayi aure na hayayyafa, 'ya'yana ma suka yi aure suka haihu duk acikin gidan nan, guda biyu daga cikin 'yammatan nan jikokina ne. Kamar yadda aka kawo 'yammatan nan gurinki yanzu haka aka kaini gurin mai babban daki sanda tana amarya, wannan shi yasa nake daga cikin amintattun bayinta, kuma wannan shi yasa ta zabe ni akan in zo in zauna a gurinki, saboda tasan zan rike mata amana. Suma wadannan duka yaran da kika gani zababbu ne dan ni ta saka in zabo mata masu tarbiyya da rikon amana kuma na zabo su. Insha Allah zamu rike ki da amana Allah kema ya baki ikon rike mu da amana." Kawai naji matar ta kwanta min araina, na tambayi yaran duk sunayensu suka fada min, naga duk sunki sakin jikinsu sai na fara yi musu wasa, ba'a jima ba suka fara dariya. Da kaina na tashi na kaisu har bq din mata na nuna musu komai sannan muka dawo tare. Nace "Ku dauke ni a matsayin yayar ku kunji, dama ni bani da kanne mata kunga shikenan na samu, duk abinda kuke so kuyi min magana in dai ina dashi zan baku, abinda bana so shine kazanta, ku kula da tsaftar gidan nan ku kuma kula da tsaftar jikin ku, ku kame kanku banda shiririta. Allah ya bamu ikon zama lafiya". Sunji dadin yadda na karbe su, kuma daga dukkan alamu sunji dadin bq din dai sai murna suke sunzo gurin 'yan gayu. Nan take baba Gaji ta raba mudu kowa aikinsa, jikokinta guda biyu su ta bawa part dina, sauran kuma sauran parts din gidan. Banda part din Sultan. A take suka tashi suka fara aikin su. Ina zaune sai ga abinci daga cikin gida, suka je suka ajiye a dining room sannan suka zo suka gaishe ni, wai hajiya tace ayi min sannu da jiki, na amsa musu, naga suna ta kallon 'yammatana da Baba Gaji da naga ta hade rai. Na tashi na koma part din Sultan na tarar ya tashi yana wanka, na zauna na jira shi ya fito, yana kallona yace "shine kika gudu ko?" Bance komai ba, ya tsaya yana goge jikinsa, ya juyo ya kalleni muka hada ido nayi sauri ya sunkuyar da kaina, yayi dariya yace "ana so ana kaiwa kasuwa. You are welcome to watch" nace "an kawo abinci, nan za'a kawo ko kuma zaka fito dining?" Yana kokarin shiga closet yace "bara kawai in fito, dama zan dan fita" har ya kai bakin kofa kuma ya tsaya ya juyo "bazaki zo ki tayani shiryawa ba?" Na rufe fuskata da hannuna, yayi dariya "wannan kunyar naga har yanzu da akwai saura, zanyi maganin ta ne" ina nan zaune inda ya bar ni har ya sake fitowa, kananan kaya ne a jikinsa yayi stocking rigar ya saka belt, da comb a hannunsa yana taje kansa, na tashi na karasa inda yake na karbi comb din na cigaba da taje masa, nace "ina zaka je?" Yace "orphanage. Yanzu zan dawo. Tunda aka fara bikin nan banje na gansu ba" na gama gyara masa gashin nace "let's go eat then". Sai bayan ya tafi sannan na dawo palo gurin baba gaji, ina zama tazo ta fara yi min tausa a kafa ta, naji dadin tausar saboda dama kafar ba dadin ta nake ji ba, cikin girmamawa ta fara yi min magana "ranki ya dade ni kam wadannan masu kawo abincin nan ina ma za'a ce musu su daina kawowa? Mu sai mu ringa yi anan" ban amsa mata ba na lumshe ido na inajin dadin tausar. Ta cigaba da magana "Ranki ya dade sai kinyi a hankali sosai da Hajiya. Mutanen da suke waje kullum suna maganar irin yadda take nuna wa karamin sarki soyayya amma mu da muke cikin gidan nan mun san ba haka abin yake ba" na bude ido na nace "waye karamin sarki?" Tace "maigidanki ranki ya dade, haka mai babban daki take ce masa muma kuma duk haka muke ce masa" na koma na kwanta na sake rufe idona, ta cigaba "bata sonsa ko kadan, kema kuma dole nasan kiyayyarsa zata shafe ki. Kar ki yarda da duk wata magana da zata gaya miki musamman akansa, mu mun san komai" maganar ta ta karshe ce ta saka na bude ido na, 'mu munsan komai' na tashi zaune ina kallonta nace "Baba Gaji, kin san mahaifiyar Sultan?" A hankali naga yanayin fuskarta yana komawa alamar tsoro, ta sunkuyar da kanta kasa, na sake magana "baba gaji kince anan gidan aka haife ki, kince kuma kina tare da Yaya tun tana amarya, haka yana nuffin kinsan mai martaba sarki tun haihuwarsa har girman sa har auren sa, hakan yana nufin kinsan haihuwar Sultan, abinda na tambayeki shine; kin san mahaifiyar sultan?" Gani nayi jikinta ya fara rawa, kanta har yanzu yana kasa ta kasa kallona, tace "ki yi min afuwa ranki ya dade, an hana mu yin magana akan ta, an hana mu ko da ambatar sunan tane" cikin mamaki nace "waye ya hanaku maganar ta? Kuma saboda me?" Ta dago ta kalleni tace "mai martaba sarki, marigayi, mahaifin wannan sarkin" wani mamakin na sake yi nace "kina nufin ba wannan sarkin ba, wancan" ta gyada kai, nace "to saboda me?" Ta girgiza kanta tace "Allah masani" nayi shiru ina tunani, Sultan ya taba ce min "no body talk about her, it is as if she didn't exist" na gyara zamana nace "amma baba gaji shi wanda kike magana akansa shekarar sa ashirin da rasuwa, in kin gaya min taya za'a yi yasan kin gaya min?" Ta girgiza kai, tace "ranki ya dade mu bayi ne, muna biyayya ga iyayen gidan mu koda kuwa bayan mutuwar su ne, bama cin amanarsu, bama ha'intarsu" na mike tsaye na fara zagaye a palon sannan na dawo na zauna nace "sanda wancan sarkin yana nan kina a matsayin baiwar sa, bayan ya mutu kika zama baiwar Yaya, yanzu kuma yaya ta bani ke, in dai har zaki yi masa biyayya har bayan ransa to hakan yana nufin zaki yi min biyayya nima. Ina umartarki daki bani labarin duk da kika sani dangane da mahaifin sultan da kuma mahaifiyarsa" ina kallon yadda duk ta rude, na dan dafa kafadarta nace "nayi miki alkawarin duk maganar da mukayi zata tsaya a tsakanin mu". Sai da ta nutsu ta daidaita numfashinta sannan ta fara magana " ina nan aka haifi mai martaba sarki na yanzu, ina nan kuma aka haifi dukkannin kannensa. Duk a cikin su shine yafi dauko halin mahaifinsa; zafin zuciya, taurin rai da kuma tausayi. Yadda kika ga karamin sarki haka yake, kuma shima kakansa haka yake. An gaya mana cewa wannan shine abinda yasa suke zama sarakuna, dan shi mulki sai mutum yana da karfin jiki dana zuciya, sai mutum yana da zafi kuma yana da sanyi. Sanda ya girma ya zama saurayi mu dai munsan yana kasar waje karatu, duk sanda yayi hutu yazo gidan nan haka zai cika gidan nan da abokanan sa har sai ya koma tukunna, wadansu abokan ma daga makarantar suke biyo shi su zo nan suyi hutun tare su koma. Rannan ya dawo gida tare da abokanan
Chapter 127 · 0% Book details