Sashe 102
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
you and let you know cewa I came back like I promised. Ina komawa ibadan na yiwa baba karya nace na samu Daddy yace yanzu kina karatu in bari sai kin gama tukunna. Mama tana gurin ashe ta gane karya nake yi. Rashin lafiyar ce dai bata barni ba dan tunda na koma ina kwance. Ban san ya akayi mama ta bincike kayana taga IV din da Amira ta bani ba. Bata ce min komai ba har na samu sauki na koma lagos. Ashe bayan na tafi ta nuna wa baba IVn ta gaya masa cewa yarinyar da nake so anyi mata aure, kuma wannan shine sanadin duk wannan ciwowwukan da nake. Ba tare da baba ya sake bi ta kaina ba ya yanke shawarar daura min aure da efi, a cewarsa macece kadai zata saka in manta da ke. Sam babu wanda ya gaya min labarin za'a yi min aure har aka daura ban sani ba, sai da uncle dina na Lagos ya je daurin auren ya dawo sannan ya kira ni ya gaya min, ranar naga tashin hankali, na gaya masa sunyi mistake, ni bana son efi ba zan iya zaman aure da ita ba dan a matsayin kanwa na dauke ta. Ya gaya min lallai in shirya in tafi ibadan inje ayi biki in taho da amaryata. A dole na shirya amma maimakon in tafi ibadan sai na zarto Abuja, direct gidan ku naje, wannan karon na tarar gidan da alamar mutane a cikin sa, ban shiga ba wannan karon a waje na tsaya sai da wani yaron gidan ya fito sannan na tambayeshi ko kina nan? Sai ya ce min ke baki zo ba, amma sauran mutan gidan sunzo, abinda na fahimta a lokacin shine mutan gidan sunzo daga England ke kuma baki zo ba tunda kina 'yalleman. Wannan shi ya goge min duk wani sauran doubts akan auren ki. Na tafi gidan su Amira, wannan karon a gida na same ta. Na gaya mata yadda mukayi da yaron gidan ku tace min eh ke kina 'yalleman, 'yan gidan ku ma sunzo suna ne saboda haihuwar da kika yi, har ta nuna min hoton babyn a wayarta. Ta gaya min cewa kunyi magana da ke kince mata in na sake zuwa ta ce min I should move on, ke kinyi moving on nima I should do the same thing. Zancen haihuwarki ba kara min tayar min da hankali ya kuma yi ba dan ina zuwa ibadan na zube wa mama a tsakar daki, mama hannu ta dora aka tana rusa kukan ta shiga uku danta zai mutu. Babane ya saka ni a gaba da nasiha da addu'a da fada har na dan samu na saki raina. Nan aka fara shirye shiryen biki. Sosai baba da mama suka kashe kudi a bikin nan a niyyarsu ta son suga sun faranta min rai. 'Yan uwana duk sun zo daga side din babana, side din baba da kuma side din mama, kowa was there to make me happy. Bana so in nuna musu kamar wahalar banza suke ji dan haka na ware sosai tamkar na karbi auren har aka yi biki aka gama. Bayan an gama biki ne mama tace mu tafi Lagos tare da efi sai nayi mata bayanin cewa bani da gida a lagos nima a gidan uncle dina nake, amma tunda a lokacin kudi suna shigo min sosai, inna koma Lagos zan sayi gida sai inzo in dauke ta, a haka muka rabu dasu na tafi Lagos. Na sayi gidan kamar yadda nace amma fir naki dauko efi. Nace ni bana son in ci zalinta kuma ni bazan iya zaman aure da ita ba. Sai da Efi ta shekara guda da aure akan ta amma tana zaman gida. Kwata kwata ma na daina zuwa ibadan saboda kar ayi min maganar tafiya da ita. Gashi arzikina kullum karuwa yake yi. Rannan kawai akayi min waya cewa baba babu lafiya, ba shiri na tafi ibadan, kwana na daya da zuwa Allah yayi masa rasuwa. A lokacin nasan mutuwar uba tunda sanda mahaifina ya mutu bani da wayo. Bayan komai ya lafa nace zan tafi, mama ta saka ni a gaba har da kukan ta akan lallai in tafi da matata, yanzu bata da kowa, ba uwa ba uba, ga mijin da dashi da babu duk daya, duk ta lalace ta fita daga haiyacinta. Kukan da mama tayi min ne ya saka na tafi lagos da efi". Muna zuwa lagos na kaita gidan uncle dina na kama gaba na, ban kuma komawa ta kanta ba. Muna yawan yin waya da Amira, nakan kira ta inji ya kike da su Hafsat, kullum tana ce min lafiya lau kuke, tace hankalinki a kwance yake yanzu baki da wani problem. Kullum tana min maganar ya kamata in ajiye maganar ki a gefe in san me nake ciki a rayuwa amma sam na kasa. Ina waya da ita ne saboda she was the closest thing i have to you. Rana daya kawai sai ga mama tazo Lagos, nan naga bacin rai a gurinta data fahimci abinda na aikata. Efi cewa tayi ta hakura da auren, ita a raba auren kawai duk son da take yi min ta hakura. Mama kuma tace ban isa ba tunda bani na haifi kaina ba. Dole efi ta dawo gidana ta tare. Mama ma anan ta zauna tare da mu ta saka mu a gaba" yayi shiru for the first time tunda ya fara magana. Na kalleshi naga yana kallon can gefe. Ya cigaba da cewa "a duk zaman da muka yi da efi bazan iya tuna ranar da na ganta cikin farin ciki a dalili na ba, ta samu gangar jiki na, amma zuciya ta da ruhina ni kaina basa tare da ni ballantana in bata. I kept blaming iyayen mu da suka hada auren duk da cewa sun san bana sonta. Ba kowanne namiji ne zai iya rayuwar aute da matar da baya so ba. Bamu dade tare ba ta samu ciki, cikin yana girma mama ta dauko ta suka dawo ibadan ni kuma nayi zamana a lagos. A ibadan ta haihu, anan kuma Allah ya karbi ranta a gurin haihuwa. Allah yaso zamuyi sallama nazo kawo musu kayan da mama tace in siya, ina xuwa ta fara labour na kaita asibiti, tana haihuwa jini ya balle mata wanda shine sanadin ta. Inda Allah ya taimake ni na nemi gafarar ta kafin ta mutu da nasan alhakin ta bazai taba barina ba. Bayan na koma lagos naji duk zaman garin ya ishe ni, da kadan na fara sayar da business dina ina dawowa nan garin, a hankali na gina wannan gurin na sayi gida sannan na dawo garin nan da zama. Bayan dawowa ta garin nan na fahimci cewa Amira still have something for me sai na yanke alakar dake tsakanin mu saboda ban taba jin son ta a raina ba, ban taba jin son kowacce mace a raina ba bayan ke. Ina yawan bin hanyar gidan ku with hope wai ko wata rana zan ganki koda kuwa daga nesa ne. Rannan kawai naje unguwar sai naga gate din gidan a bude, kamar ana biki a gidan. Nayi packing daga dan nesa ina jin dadin maybe zan ganki. Na kira Amira a waya nace mata nazo gidanku na tarar ana biki, sai tace min bikin Hafsat akeyi. Ta fito ta same ni tace ta gaya miki nazo kince please in tafi kar mijinki ya ganni, tace kince you are happy with your life and I should leave you alone" ya sake yin shiru yana kallona, fuskarsa tana nuna irin bacin ransa. Ya cigaba da cewa "tun daga ranar ban sake zuwa gidan ku ba. Nayi concentrating akan business dina. Amira tasan ina garin nan amma bata san me nake yi ba, she had no idea nan guri nane, dan haka da kuka zo bata taba tsammanin zata ganni anan ba" Tun da ya fara maganar nake hawaye har ya kammala, ya tashi ya je gurin water despenser ya debo ruwa a cup ya dawo ya miko min na karba na shanye ina jin dadin yadda sanyin ruwan yake sanyaya zuciyata. Maimakon ya zauna a kujerar daya tashi sai ya hau kan table din gabana ya zauna, exactly yadda yake yi sanda muna makaranta. Na dago kai na kalle shi, he was grinning from ear to ear. It is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Involuntarily na kai hannuna kan zoben Sultan na fara wasa dashi. A hankali Ibrahim yace "it is alright now, we are together now" a hankali na far girgiza kaina hawayen fuskata yana karuwa, ya saka hannu zai dago fuskata na matsa baya. Nace "married or not married, ba dai dai bane kake taba ni ba, ka sani kuma" yayi dropping hannunsa a sides dinsa, yace "bani naki labarin inji, what have you been doing all these years" a hankali na fara magana nace "I waited for you, for five years, I waited" yace "six, almost seven" nace "I met someone after five years of waiting for you" nayi shiru ina kallon yadda yanayin fuskarsa ya fara chanzawa, yace "what? Who?" Nace "it doesn't matter who" ya sauko daga kan table din ya koma wajan ruwa, this time kansa ya zuba wa yasha, sannan ya tari wani ruwan ya zuba a kansa, ya juyo yana kallona da wani yanayin da bazan iya fassarawa ba, nayi sauri na dauke kaina dan ba zan iya juran kallonsa a haka ba. Yana daga tsayen yace "do you mean to tell me that you are in love with someone else?" Na yi shiru ina jinjina kalmar love, in nace love sai inga kamar na rage darajar what I feel for Sultan, it is more than love, na gyada kaina a hankali nace "yes" da sauri ya karaso gaba na ya durkusa "maimunatu please, please don't say that, zuciya ta zata iya bugawa please" na runtse idona ina jin zafi a raina, I hate to hurt him like this amma dole in gaya masa gaskiya, nace "I loved you, but not anymore" ya mike da sauri ya fara safa da marwa a office din yana cewa "you don't mean that, dan dai bana nan ne,