← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 190

Sashe 96

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Akan kujera ya zauna nima na karasa na zauna a kusa dashi, ya juyo yana kallo na nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa ina murmushi, dariya yayi sosai yace "wai ni kike jin kunya kuma? Tsafdi, lallai kin hadu da aiki" ni dai bance komai ba, ya kamo hannayena duk biyun yana kallon su, sannan a hankali ya shafa zoben sa da har yanzu yake makale a danyatsa na. Sannan yace "wata biyu suka ce, what if something happens a cikin watanni biyun? Na kalle shi naga ya sunkuyar da kansa yana kallon hannayen mu a hade, nace " Sultan, babu abinda zai faru kaji? Kullum muna addu'ar zabin alkhairi, tinda har Allah yasa suka ambaci wata biyu to sune mafi alkhairi a gare mu. What if da ace baffa cewa yayi NO? Ya zakayi kenan?" Ya dago da sauri yana kallon idona yace "then I will definitely be your patient, dan kwakwalwata zata iya bugawa" na same hannu na daga nasa na tallafo fuskarsa dasu ina kallon idonsa nace "babu abinda zai same ka, shi Allah baya taba dorawa bawansa abinda yasan ba zai iya ba" ya katse ni yace "then Allah ba zai raba mu bama, saboda yasan ba zan iya dauka ba" idonsa gaba daya ya chanza kala, nayi saurin chanza maganar nace "Askin ka yayi kyau" Hannu biyu ya saka ya rufe kan sa yace "ash, ya akayi na bari kika gani" nace "really yayi kyau, I like it" ba duk gashin aka aske ba, an rage masa tsaho dai, sai ya fi dacewa da sajen sa, fuskarsa kuma ta kara fitowa sosai. Ya shafa kan yace "thank You" sannan ya cigaba da magana "tom yanzu cikin two months din nan me za muyi?" Nace "kamar me fa?" Yace "to kill the time" nace "as usual, kai already ma ai aiki yayi maka yawa, ga office ga harkar gini, ni kuma I will just be here, waiting" yace "driving lessons din mu fa?" Nace "bayan ba wani abin kirki kake koya min ba, for over one month amma ace har yanzu ban iya driving ba" muna cikin haka muka ji muryar Amir "to in kun gama soyewa sai kuzo muyi sallama mu zamu tafi gida" na tashi ina dan jin kunya, muka fito muka tarar har sun dauko mota mukayi sallama suka tafi, Amir kuma ya dauko motar sultan guda daya, yana zuwa gurin mu nace "Amir dan Allah ga Amira nan ka kaita gida, kaga dare yayi sosai" a tare suke ce "what?" Ni da sultan sai dariya, sultan ya bata rai yace "gaskiya Amira in ba zaki shiga motar Amir ba to sai dai ki hau taxi, dan ni na gaji ba zan kai ki gida ba" Amir yace "to ni an gaya maka ban gaji bane? Ballantana wannan unguwar tasu mai shegen nisa, kuma ni ba ma nason a ganni da ita a mota a daukar ko budurwata ce, ai sai aji na ya zube" nan Amira ta hayayyako "Allah ya kiyaye min shiga motar ka, ni da in shiga motar ka ba gwara na tafi a kafa ba" yace "ai kuwa zaki tafi a kafar" har yaja mota sai kuma yayi reverse, yace "get in" kawai sai muka ga Amira ta zagaya ta bude ta shiga sun tafi, daga ni har sultan duk sakin baki muka yi muna kallon su, Sultan yace "munafukai, a hankali sai asirin ku ya tonu"

Rayuwa ta koma normal, abubuwa suna tafiyar mana yadda muke so, sultan ya dukufa haikan akan aikin gininsa duk da kusan tare muke aikin dan dai ni bana fita field dinne amma komai tare muke tsara shi, komai za'a saka a gidan sai ya kawo min samples na zaba tukunna, ba karamin kudi yake narkar wa a aikin ba dan ni har mamakin inda Sultan yake samun kudi nake yi, gani nake kamar aikin sa ba zai shigo masa da wadannan uban kudaden ba. Rannan mun fita koyon mota sai yace min yana so zamu je wani guri. Hanyar barin gari naga mun dauka amma ban tambaye shi ina jamuje ba. Gani nayi yayi packing, na fito ina kallon gurin da muka zo, orphanage, a kafa muka shiga cikin building din. Babban guri ne sosai, ga dakunan yara, maza daban mata daban, ga gurin wasa, ga kitchen sannan ga offices din staff. Muna shiga ma'aikatan gurin suka fara gaishe mu da girmamawa sosai kamar zasu kwanta a kasa, ni har mamaki nake yi, idonsu kawai zaka kalla kaga tsantsar soyayyar sultan da kuma respect dinsa, ya fara tambaya "where are my kids?" Da sauri wata tace "suna playground suna wasa" muka tafi gurin, ina ta kallonsa naga wani excitement a fuskarsa, real love, ai kuwa muna shiga gurin wasan gaba daya rayan suka taho a guje wasu har suna faduwa suka rungume shi, sai da suka kai shi har kasa yana ta kyalkyala dariya, in ba tare da ni ba ban taba ganin sultan cikin wannan fara'ar ba, da kyar ya samu suka daga shi, ya zauna a zaune suka zagaye shi kowa yana kokarin bashi labari, ga mamakina duk yasan sunan kowa kuma yasan me yake ciki, ni sam bana fahimtar me suke cewa saboda yadda suke magana gaba dayan su a tare. Sai da suka dan numfasa sannan ya tashi ya kamo hannuna yace "na kawo muku bakuwa yau, Mommy zaku ke ce mata, she is going to be my wife" masu wayon cikin su suka kama murna marasa wayo kuma kawai suka tsaya suna kallona, har cikin dakunan su ya shiga dani na gani, ko wanne yaro da gadonsa sai 'yan kanana ne ake musu shimfida a kasa saboda kar su fado, gurin tsaf tsaf babu kazanta, ko wanne yaro da locker din kayansa, ga kuma inda suke cin abinci shima a tsaftace, muka shiga kitchen masu aikin girki suna ta gaishe mu, suka bashi list din abubuwan da suke bukata nan take ya bada kudin yace a saya, muka shiga dan karamin clinic dinsu shima ya nuna min sannan yace yana son ya dan yi musu 'yar karamar makaranta amma sai nan gaba tukunna, yanzu dai van ya saya musu ake kaisu kamaranta kullum ake dawo dasu. Har zamu tafi wani yaro yazo da gudu yana bata fuska yace "Daddy kace in ka dawo zaka kawo min bindiga kuma gashi ka dawo baka kawo min ba" Sultan ya sunkuya har kasa yana shafa kan yaron yace "sorry Halifa, na manta, amma gobe insha Allah zan bawa uncle Amir ya kawo maka" yayi masa kiss a goshi, yaron ya tafi yana ta murna. Ji nayi kwalla ta taru a idona, yanzu na fahimci inda sultan yake samun kudi, as long as kana kyautatawa mutane da dukiyarka, musamman marayu, to Allah zai yi ta ninka maka kofofin arzikin ka, abinda ka bayar sai Allah ya biya ka da dubun sa, mutum kamar sultan ba zai taba talauci ba. Muna shiga mota ya kama hannuna daya ya rike yake tuki da dayan hannun, babu wanda yace komai, can nace masa "da ka gayamin nan zamu zo at least ai da na taho musu da wani abu ko?" Yace "you are welcome, duk sanda kike son zuwa zan kawo ki" na sake yin shiru a raina ina mamakin mutum irin sultan.

Tafiya muke a hankali kamar ba ma son zuwa gida, kowa da tunanin da yake yi, har yanzu kuma yana rike da hannuna, sai da muka yi nisa nace "Sultan ya kamata kaje gurin Takawa kuyi maganar bikin nan dashi" ba tare da ya kalleni ba yace "naje ai" da sauri na kalleshi ina mamakin ya akayi bai gaya min ba, packing yayi sannan yace "Abbas ne ya kira ni a waya ina office yace min inje Takawa yana kirana, da naje gurinsa na gaishe shi bai amsa ba, kin san me yace min?" Na girgiza kaina, yace "check book ya jeho min duk yayi signing pages din yace 'ka dauki duk adadin kudin da kake so kayi duk abinda kake so dashi, amma ina son ka fasa auren yarinyar nan, she doesn't deserve someone like you" yayi shiru fuskarsa tana nuna bacin ransa, a hankali na tambayeshi, "me kace masa kuma" ya daga kafada yace "na ajiye masa check book dinsa na ce masa bana bukatar kudinsa, abinda da nake nema daga gare shi ma yanxu bana bukatar sa" ya juyo yana kallona yace "all I wanted before is love, yanzu na samu daga gare ki, kowa ma yaje ya rike nasa, your love is enough for me" hawaye naji yana fitowa daga idona (is it possible to love someone so much that it makes you cry?) Ya saka hannu yana goge min hawayena yace "just promise me that you will never leave me

Episode Sixty Two : The Manager
Chapter 96 · 0% Book details