Sashe 135
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
wa baban ta alkawarin kula da ita ne, duk da cewa na gaya masa cewa duk abinda kayi mata shi ya saya da kudinsa. Amma har kana buda baki kana gayamin cewa kai ka bata bindiga da hannunta ka saka ta ta harbi mutum. What kind of a husband are you?" Ya juyo kaina yace "ki sani, zan kira Muhammad in gaya masa halin da kike ciki, Idan kuma shi ba zai dauki mataki ba ni zan dauka, saboda a matsayina na shugaba bazan tsaya ina kallo yarinya kamarki with good potential in life ta rusa rayuwarta saboda yaro kamarsa ba" ya karashe maganar yana nuna sultan. Sultan ya sake kama hannuna ya rike yace a hankali "we will leave, we will leave the palace, we will leave the town in ma kasar kake so mu bar maka zamu bar maka, you will never hear from us again..." Ya katse shi yace "you will leave the town dai, amma babu inda zaka tafi musu da yarinya, in kaga dama ka tafi karshen duniya ma babu wanda ya damu, but she will remain here" da sauri sultan yace "she is my wife" Takawa yace "and yet, nace babu inda zaka je da ita, in kuma baka yarda ba try me kaga abinda zai faru" tunda suka fara maganar nake kallon fuskar Takawa ina tattaro dukkan ilimi na na psychology ina so in karanci mind dinsa amma na kasa, kamar wani blanket ne a idonsa daya rufe emotions dinsa. Sultan ya mike da sauri ya jani, ina jin Hajiya tana cewa "amarya ki shiga ciki mana in na shigo sai mu gaisa sosai" kafin in samu bata amsa Sultan ya jani da sauri muka bar gurin, ni dai kawai binsa nake yi a baya dan ji nake yi kamar zai tashi sama dani, muna zuwa ya bude mota ya jefa ni ciki ya rufe ya zagayo ya shiga ya tayar, yana yin reverse ya daki lamp post amma bai tsaya ba ya figi motar mukayi hanyar gurin mu. Har mukaje bai ce min komai ba nima ban ce masa ba, yana yin packing ya fito da sauri nima na biyo shi a baya harda dan gudu na dan in kamo shi, ta kofar part dinsa ya shiga na bishi a baya, yana shiga ya dauki coffee table dinsa ya buga shi a jikin bango ya tarwatse, na saka hannuna na toshe kunne na ina ambaton sunan Allah, ban taba ganin bacin ran sultan ba irin na yau, idonsa yayi duhu hancinsa yana budewa alamar yana shakar numfashi da sauri, nayi kokarin in rike shi kar ya taka glass din ya yanke amma ya kwace ya jawo wani frame ya doka a jikin glass din window duk suka hadu suka tarwatse. Na kira sunan sa da karfi "Sultan, look at me, me kake yi ne haka?" Ya juyo yana kallona sai kuma ya kwabe fuska kamar zaiyi kuka amma kuma babu hawayen, yace "He is going to take you away, I should have known dama ba zai taba bari na cikin farin ciki ba. What did I ever do to him" na karasa na rungume shi ina jin bugun zuciyarsa tamkar a kirjina, a hankali nace "babu mai rabaka dani mijina, am yours, forever and ever" ya zagayo hannayensa a jikina yana sauke ajjiyar zuciya sanna ya sake cewa "what did I ever do to him?"