← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 190

Sashe 141

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

than sarauta, and now I don't want it, har cikin zuciyata" tun daya fara maganar nake kallonsa kuma na fahimci har cikin zuciyarsa abinda yake fada haka ne. Nace "tunda haka kake so then that's exactly abinda zaka yi. Amma ni ina ganin no matter how much kake so kayi ditching sarauta it is in your blood. In kana ganin zaka iya why not kake zuwa once a week, kamar on Fridays, just ka gaishe shi da sauran mutanen gurin ka fito, Amir zai iya kula da companyn ka a lokacin. At least kaga galadima ba zai ga kamar ka ki daukan shawarar sa ba" ya danyi murmushi yace "in dai hakan shine abinda my Queen tace to hakan zanyi. But not Amir, sai dai in sami wani, Amir hasn't been himself lately" naji babu dadi nace "why? Me ya faru dashi?" Yace "akan wata yarinya ne da yake nema. Sunanta Aisha, 'yar maiduguri ce, tazo bikin cousin dinta garin nan suka hadu suka fara soyayya, bayan ta koma gida har maiduguri yake zuwa gurinta, wajan shekarar su daya kenan tare. To yanzu sai iyayenta suka ce ta fito da miji ita kuma tace shi take so, aka aiko wa aunty din ta tanan garin akan ta bincika waye shi, the first thing da tayi finding out shine babu wanda yasan iyayensa, a kofar orphanage aka tsince shi ko cibiyarsa ba'a yanke ba. Suna jin haka suka aiko masa cewa kar ya sake zuwa gurin 'yarsu, su ba zasu bada 'yarsu ga wanda bashi da asali ba. And that break him down, bai taba nuna damuwarsa ga rashin iyayensa ba sai yanzu, lokuta da yawa yana mayar da maganar kamar wasa amma yanzu he is devastated, it hurts me that there is nothing I can do for him" naji kamar zanyi kuka, naji tausayin Amir sosai, how can some parents be so cruel, ki haifi da da kanki sannan ki je ki jefar dashi? Shi yaron menene laifinsa? Shi yace ki haife shi? Ana samu kuma har da masu kashewa, wadansu su jefa a toilet, ni dai a ganina wannan shine extreme of cruelty. Allah ya shirya mu baki daya. Nace "but da na dauka yana son Amira ne ai, har na fara tunanin idan abin yazo zan yiwa Daddy magana ya shigar masa tunda akwai sanayya abin zai zo da sauki" Sultan yace "gaskiya bai taba yi min maganar Amira ba, kullum ina tsokanarsa akanta saboda inji ta bakinsa amma bai taba cewa komai ba, wannan Aishan dai ita ce a gabansa" nace "Allah sarki Amir, Allah ya kawo masa mafita" yace "Ameen". Tun daga lokacin Sultan ya fara zuwa fada duk ranar Fridays, ranar farko da zai je haka na zauna nayi ta addu'ar Allah ya dora shi akan mahaifinsa kar ya wulakanta shi a cikin mutane, dan nasan zuciyar Sultan, in dai Takawa ya kore shi to kuwa ba zai sake zuwa ba, tunda yanzun ma ba wai a son ransa yaje ba. Cikin ikon Allah kuwa babu abinda ya faru, sai dai kamar kullum da ya gaishe shi bai amsa ba, Sultan bai nuna ya damu ba ya gaishe da sauran mutane ya dan zauna for one hour sannan ya tashi yayi tafiyar sa. Kiri kiri ya hango bacin rai a fuskar Abbas amma bai kula shi ba, sai ya nuna kamar bai san yana yi ba. Ranar ina zaune ina jiran sultan ya dawo daga office sai ga sako daga Abbas, alkyabba da rawani, wai a bawa sultan inji shi a ce masa in dai yana son zaman fada he should dress like dan fada, nasan tsokanar fada ne, dan haka na nuna wa dan aiken kamar Sultan yana dakin sa, na shiga na fito na dawo masa da kayan nace sultan yace a gaya wa Abbas ya gode sosai, amma ya riga yayo order nasa kayan daga saudiyya, idan sun iso ma har shi zai aikowa, tunda dai hakkin yaya ne ya jagoranci gida ya kuma kula da kannensa. Ni nasan na kunna wuta a zuciyar Abbas ranar nan, Sultan yana zuwa na bashi labarin abinda ya faru, muka yi ta dariya tare dashi na kuma cigaba da rokon sa akan dan Allah duk abinda Abbas zai yi masa kar ya kula shi, dariya kawai sultan yayi bai ce komai ba. A kwana a tashi na fahimci shigar ciki a jikina, sam babu laulayi dan ko sau daya ban taba amai ba ko zazzabi, lokacin period dina yana zuwa naga bata zo ba dan haka na tabbatar da zargina, Sultan kam da yaga babu period shi murnar sa ta daban yake yi dan kwata kwata banga alamar yayi linking abin da ciki ba. Babu laulayi a ciki na sai dan karen kwadayi, kullum ina kitchen, in soya wancan inci, in gasa wannan inci, in tafasa wannan inci. Tunda sultan baya wuni a gida dan haka sam bai san me nake yi ba, da daddare kuwa yawo nake masa in gudu daga dakinsa in tafi kitchen in ci abinda zanci in dawo. Ina ta tunanin yadda zan yi in gaya masa, duk da bamu taba yin zancen haihuwa dashi ba amma nasan yadda yake son 'ya'yansa na orphanage dan haka nasan Allah ne kadai yasan irin son da zai yiwa nasa dan ko 'yar. Ranar wata Wednesday tun da safe nake son chocolate, sauran wadda nake da ita a gida na shanye amma kamar tayar min da kwadayi ta kuma yi, sultan yana dawo wa daga office na saka shi a gaba sai ya kaini mall na sayo chocolate, da kyar na barshi yayi wanka ya dan huta, ana yin sallar magrib na dauko bakar after dress na dora akan riga da zanin jikina, nayi rolling viel na dauki key din mota na tsaya ina kallon Sultan, ya langwabe kai yace "please Love, ki bari muci abinci mana" na girgiza kai nace "in mun dawo ma ci, yanzu fa zamu je mu dawo, ko 30 minutes ba za muyi ba. Yayi ajjiyar zuciya ya mike yace " amma ki sani, ina binki bashi, in mun dawo zan karba" a raina nace 'oho dai, ko ka kaini ko baka kaini ba dama nasan sai ka karba din'. Muna fita nace "sahad zamu je" ya dan bata rai yace "why? Kin san bana son zuwa sahad, it is too crowded" nace "naga yafi kusa ne ai, kuma ba wani special abu zan saya ba kawai chocolate ne" ya daga kafada yace "OK, bara muje can din". Ibrahim Tun da safe yace da Amina zai zo gurinta da yamma, dan haka yana tashi daga office gida ya tafi yayi wanka ya shirya, yana yin sallar magrib ya fito ya dau hanyar gidan su, yana shan kwanar gidan ya hango ta tana tahowa bakin titi, bakar after dress ce a jikin ta, tayi rolling mayafin rigar, kamar kullum duk sanda ya ganta sai gabansa ya fadi saboda gani yake kamar Moon ce sai ta matso kusa sai yaga ba ita bace. Yayi slowing down ya barta ta karaso inda yake sannan ya sauke glass dinsa yace "ina zuwa ne haka?" Ta dan tsorata kadan, yayi dariya ita kuma ta bata rai "tun dazu kace min zaka zo ina ta jiranka shiru" ya hada hannuwansa biyu yace "am very sorry, ban tashi da wuri bane ba kuma naga it is already late, shine na tsaya na jira bayan magrib sannan na taho. But ina zaki je kuma?" Ta dan kara bata rai tace "Mommy ce ta aike ni sahad, kuma drivers din duk basa nan" yace "to ga wani drivern yazo, common in" ba musu ta zagaya ta shiga suka tafi. A hanya yace mata "but why sahad? Ba zaki zo gurina kiyi siyayyar ba?" Tayi dariya tace "are you jealous?" Yace "of cause I am" tace "let me tell you why. Shi sahad tsohon guri ne, akwai wasu specific abubuwan da ba'a samu a wani gurin, misali sababbin guri irin naka, sai acan. Dan haka Mommy ta fada min exactly abinda take so bata son substitute, dan haka gwara inje can din direct nasan zan samu" yace "OK, zan kaiki sahad ne kawai saboda inyi proving cewa you are wrong, babu abinda suka fi mu dashi, sai abubuwan da muka fi su dashi ma" tace "OK, we will see". Suna shiga cikin sahad motar su Moon tayi packing suma suka fito duka shiga, amma kowa da side din daya nufa. Ya dauko mata basket suka fara zagaye tare tana duna list din Mommy, ya karbi list din ya duba yayi tsaki yace "babu abinda bani dashi anan wallahi" ta karbi basket din tace "ka ga in kasan zaka dame ni da mita yi tafiyar ka wani gurin, in na gama sai in neme ka" da kamar ba zai tafi ba kuma sai ya tuna cewa a matsayinsa na dan kasuwa ya shigo gurin abokin competition dinsa gwara yayi using chance din ya zagaya yaga abinda suke dashi wanda shi bashi dashi, dan haka ya sakar mata basket din yace "OK, call me when you are done". Ya tafi yana zagaya gurin, har ya fama zagayensa bata kira shi ba, yayi tsaki, su dai mata in suka shiga kasuwa sai ka rasa me sukeyi, shi kuma bai ga abinda wannan gurin yafi nasa ba. Ya juya ya koma ya fara neman ta, ko bata gama bama fita zasuyi, ko me take so suje gurin sa ta dauka. Moon Muna shiga direct gurin sweets na tafi, na dauki basket na mika wa sultan ya rike min, na fara chocolate verities iri daban daban ina zubawa a basket din, Sultan kawai kallona yake yi da mamaki yace "wai yaushe kika zama shazumamu ne ban sani ba? Duk wannan chocolate din me zaki yi da ita? A matsayin ki na doctor ai kinsan illar zaki ga lafiyar ki ko?" Na juyo na murguda masa baki na juya na cigaba da abinda nake yi, yace "ni ko? Zaki yi bayani ne in mun koma gida?" Mun jima ina ta diban alawa, in dau wannan in ajiye in koma baya in dauko wata, Sultan ya gaji, kuma ina sane nake kara delaying din mu, a raina ina cewa 'bani kadai zan sha wahalar cikin nan
Chapter 141 · 0% Book details