← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 190

Sashe 93

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Da safe yawa ta tana kashe dan haka bamu yi wayar da muka saba yi da safe ba kafin ya fita, bayan munyi breakfast na kira shi naji switched off, har aka zo lunch ban samu wayarsa ba, kuma bai zo cin abinci ba, daddy ya tambayi walid sai walid yace masa sunyi waya yace yau aiki yayi masa yawa ba zai zo ba. Muna gama cin abinci naje na hada masa basket guda na abinci na bawa driver nace ya kai masa office dinsa. Ga mamaki na sai ga drivern ya dawo yace wai ance yau baije office ba, suma nemansa suke yi. To ni maimunatu ina sultan ya tafi. Babu irin tunanin da banyi ba. Har akayi la'asar shiru. Ina kitchen ina zaune ina kallon su asma'u suna ta aiki, yau ko surutun ma bana musu, sai ga maryam ta shigo da sauri tace "kai kuxo ku gani yau baki akayi a gidan nan har da masu rawani da dogarai" da sauri na mike nabi bayansu muka leka ta tagar kitchen amma bama hangowa sosai, na dai hango jama'ar gidan mu sunyi chirko2 a gefe, muna cikin leke Mommy ta shigo kitchen din da sauri tace min "zo ki fita ki tafi daki" da sauri na fice ina jinta tana bada order abinda za'ayi. Dakin hafsat na shiga na tarar tana sana'ar tata ta bacci, na daga labulen window dinta na leka waje, jibga jibgan motoci na gani har guda biyu sai kuma mota mai kalar kayan dogarai, yaya Walid na gani da sauri yaje gurin motar farko ya bude kofar ya durkusa ya gaishe da wanda yake ciki sannan ya matsa ya badu guri suka fito, manyan mutane ne sun sha kayan alfarma na sarauta, duk ban san suba, naga sun tafi palon da Daddy yake saukar manyan bakin sa. Aka matsar da motar gefe aka matso da dayar, matane suka fiyo su biyu, daga ganin su kaga manyan mata, dogarai suka zagaye su har suka shigo kofar palo. Nayi sauri na koma bakin kofa nayi kneeling ina leke ta keyhole, Mommy da mutanen ta suna ta kai kawo a gurin bakin amma bana hango su sosai kuma bana jin me suke cewa. Na zauna anan na jingina da jikin kofar, na kara kiran wayar sultan switched off. Dazan kama matar nan mai cewa switched off a waya da Allah kadai zai raba ni da ita. Ina nan zaune naji kiran Mommy ya shigo, na dauka tace "kina ina ne?" Nace "ina dakin Hafsat" sai a lokacin Hafsat ta tashi ta ganni nayi tsuru2 ta tambaye ni menene na daga mata kafada. Mommy ta shigo tana kallona sannan tace "ki zo ki gaishe su" da sauri na bude kayan Hafsat ina neman kayan sakawa, Mommy tace "NO, kayan ki are OK, kawai ki dan gyara fuskarki sai ki samu babban mayafi ki saka" na shiga toilet da sauri na wanke fuskata, jikina sai rawa yake, inna kama sultan ni kadai nasan me zan yi masa, in less than five minutes na shirya Hafsat ma ta dan gyara muka fita. Tunda muka fita kaina yana kasa amma inajin idonsu a kaina, muka zauna daga can nesa muka gaishe su suka amsa mana da fara'ar su. Daya ta fara magana "Sultan bai kyauta mana ba wallahi, sam bai gaya mana maganar nan ba sai yau. Yanzu gashi ya saka munji kunya bamu kawo mata wani abin kirki ba" wata kuma tace "marar kunyar ba, ni yaushe rabon da in saka shi a idona, kawai sai gashi da sassafe yaje min kamar an koro shi, ni na dauka ma baya kasar" sai kuma ta dawo kaina "Maimunatu kalle ni kinji, ni ba surukar ki bace ba, ni kakar ki ce, Nani sunana, wannan kuma Yaya" ta nuna ta kusa da ita, "wannan ita ce surukarki, matar galadima ce" na kara sunkuyar da kaina ina murmushi, yaya tace "mu kadai muka zo yanzu saboda bai bamu lokaci ba, yace lallai sai munzo yau, mu zuwa muka yi mu ganki mu saka miki albarka sauran kuma magana ta maza ce" Matar galadima ita ma tayi mana addu'ah aka ce mu tashi mu koma. Ina shiga daki na zube a kan gado, gaba ki daya jikina rawa yake yi. Hafsat tace "wai kina nufin bai gaya miki zasu zo ba?" Na girgiza mata kai. Muna nan zaune har suka tafi sannan muka fito palo, kaya muka tarar a gaban Mommy akwati biyu, kayan kwalliya ne kawai dana gyaran jiki. Ina ta jiran inji anyi min wata magana shiru babu wanda yace min komai, har muka yi dinner da Daddy shima bai yi min magana ba. Sultan bai zo ba kuma babu wanda yayi maganar sa. Na gaji da zama na tashi na ce musu sai da safe na hau sama. Na kwanta amma sai juyi nake yi na kasa bacci, me hakan yake nufi? Babu abinda zuciya ta bata ayyana min ba kuma duk marasa dadi. A haka har bacci barawo ya dauke ni.
Chapter 93 · 0% Book details