Sashe 148
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2 A hankali Takawa ya fara dawowa haiyacinsa, ya bude idonsa da sauri yana kokarin ya dai dai ta tunanin sa, ya ilahi wannan wanne irin mugun mafarki yayi haka? A mafarkinsa wai an raba shi da khairat, a mafarkin sa kuma wai baya son Little Love, a mafarkinsa little love shine abinda yafi tsana fiye da komai, kuma wai har anyi shekaru da yawa har Little Love ya girma yayi aure. Oh wannan wanne irin mugun mafarki ne haka? Ya yinkura ya tashi zaune yana duba gefensa dan ya tashi khairat ya bata labarin mafarkin da yayi, amma sai me? Babu khairat a gurin, kuma wannan gadon ba nasa bane ba, ya kalli dakin shima, wannan dakin shima ba dakin sa bane ba, yayi kama da executive dakin asibiti, amma kuma haduwar dakin babu abinda ya raba shi da dakin gida sai drip daya gani a hannunsa. A karshen mafarkinsa an yi forcing dinsa ya je asibiti duba little love daga nan kuma bai san me ya faru ba sai ya farka daga mafarkin, to ko dai still har yanzu mafarki yake yi ne? Ya matsa ledar drip din yaji zafin shigar ruwan, mutum ai baya jin zafi a mafarki. Ya tashi zaune sosai ya cire drip din ya mike tsaye, gaban taga yaje ya daga labulen tagar, tabbas nan asibiti ne. Ya ilahi what is happening? Kofar toilet ya bufe ya shiga dan ya wanke fuskarsa maybe ko zai dawo haiyacinsa sosai, abinda ya gani a cikin madubi shine ya saka ya daskare a bakin kofa, he looks exactly like yadda yake a cikin mafarkinsa, older, thirty years older, ya karasa gaban madubin yana taba fuskarsa, shi din ne dai kuma tabbas wannan ba mafarki bane ba. Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu duk abinda ya faru da gaske ya faru kenan? Yanzu shekararsa talatin rabonsa da khairat? Tana ina yanzu, shin tana da rai ko akasin haka? And Little Love, my poor innocent Little Love. A toilet din ya durkushe yana rusar kukan dashi kansa bai san ya iya irinsa ba. 30 years back Tabbas Prince Sadiq Abdallah yayi soyayya da Khairat Faisal Abdallah a Oxford, England. Khairat full blood balarabiya ce kuma she too is of royal blood, born and raised in Riyadh, Saudi Arabia. Soyayya suka yi mai tsanani wadda har suke ganin cewa kamar they share the same soul but different bodies. Amma duk wannan soyayyar da suke yi iyayensu basu da masaniya a cikin al'amarin, wannan kuma ya faru ne kasancewar khairat balarabiya dan larabawa da wahala su dauki 'yar su su bada ita aure ga bakar fata, bahaushe. Khairat bata taba ganin anyi haka a familyn su ba, in fact a familyn su ma mostly auren dangi ake musu, dan already ma ita da akwai wanda aka riga aka ajiye mata zata aura in ta gama makaranta. Wannan shi yasa duk nacin da Sadiq yake yi mata akan ta barshi yaje gidansu taki yarda. Lalube kawai suke yi a cikin duhu. Sadiq yasan da irin kalubalen da yake gabansu amma shi bashi da tsoro sam, kuma ya riga ya saka a ransa cewa khairat tasa ce ko da kuwa sama da kasa zata hadu babu wanda ya isa ya raba shi da ita. A haka har suka gama makaranta, iyayen Khairat suka zo suka dauke ta suka mayar da ita gida. Wannan ba karamin tayar da hankalin Sadiq yayi ba dan ya san da maganar wancan hadin da ake so ayi mata a gida. Babu shiri shima ya tattaro ya dawo Nigeria gurin sarki Abdallah, ya shigar da maganar yana son sarki Abdullah yaje can Riyadh ya nemo masa auren Khairat. Sarki Abdallah yasan abinda dan nasa yake nema is close to impossible, ba zasu bashi auren khairat ba, musammam tunda an riga an yi mata miji, ba zasu karya alkawari ba, hakan yasa yayi kokarin tausar zuciyar dan nasa akan ya hakura da auren ya dawo gida ya nemi auren ko wacece a Nigeria zai nema masa aurenta, amma Sadiq was as hard as stone, dan haka ya tubure shi lallai ita yake so kuma ita zai aura. Da Sadiq ya fahimci cewa baban nasa bashi da niyyar honoring wish dinsa ga kuma time yana kurewa dan yasan a koda yaushe za'a iya daura wa khairat aure, dan a halin yanzu ma tayo masa waya tana kuka cewa maganar auren ta tashi kuma ta fadawa babanta cewa ita bata son wanda za'a aura mata kuma shi sadiq din take so, tana fadar haka baban ta ya saka aka kaita daki aka rufeta yace ko palo kar a barta ta ta kuma fitowa. Wannan ba karamin tayar da hankalin sadiq yayi ba, dan a lokacin ji yake yi da ace ya rasa khairat gwara ya rasa ransa, sai ya hada kayansa bada sanin iyayensa ba ya gudu daga gida. Riyadh ya tafi ya kama hotel ya zauna yana plan din abinyi, ba'a karbe wayar khairat ba dan haka suna waya da ita, ita take kara encouraging din sa ma akan yazo din, suka shirya plan dinsu sosai, plan A da plan B. Plan A shine zaizo gidan su ya nemi aurenta a gurin uncle dinta. Plan B kuma shine idan plan A yayi failing an hana shi auren nata zai salallabo cikin dare ya sace ta su gudu. Sadiq yasan cewa Saudi Arabia ba Nigeria ba ce ba, suna da tsatstsauran doka, idan aka kama shi zai iya rasa ransa, babu wanda zai kalle shi ya matsayin Prince tunda su a gurinsu he is not a Prince, amma soyayya ta rufe masa ido. Ya shirya tsaf yaje ya aiwatar da plan A, amma ko kyakykyawan kallo bai samu daga uncle din Khairat ba, in fact warning ma ya buga masa kuma yace ya bashi two days yabar kasar in ba haka ba zai turo masa askarawa suyi out dashi. Sadiq zuciya kamar zai mutu dan bakin ciki, wai yanzu saboda tribe dinsa da kalar fatar sa shi yasa za'a hana shi auren wacce yake so? Menene aibun sa? Yana da asali, yana da addini, yana da ilimi, yana da dukiya kuma shi cikakken namiji ne bashi da tawaya ko kadan amma saboda shi bakar fata ne an hana shi aure duk kuwa da cewa yarinyar shi take so. Nan take ya kira khairat ya gaya mata plan A failed, initiating plan B. Khairat ce ta tsara masa duk yadda tsarin gidan nasu yake shi kuma ya zana, tayiasa bayanin dakin da take da komai. Tayi wa mahaifiyar ta dabara ta saci spare key din kofar gidan ta jefa ta window, ta kira sadiq ta gaya masa shi kuma yazo ya dauka, ta kuma gaya masa exactly a inda ake ajiye keys din gidan. Ana gobe daurin auren khairat Sadiq yazo, bai samu matsala ba saboda su a Saudi Arabia babu burglary dan haka ba wani security. Tunda kowa yasan hukunci babu wanda yake shiga gidan wani. Yana zuwa ya bude kofa da key ya shiga ciki, duk gidan suna bacci banda khairat da take yi masa magana ta waya tana kara yi masa bayanin inda zai bi, a haka har yaje har dakin mamanta ya dauko key din dakinta. Ya fito ya tafi dakinta ya bude, already a shirye take dama dan haka ko magana basu yi ba ta biyo shi da sauri suka fita daga gidan suka shiga motar daya zo da ita, a dakinsa na hotel suka karasa kwana, da sassafe dama yayi musu booking plight suka tafi airport, around 7, jirginsu ya tashi zuwa America. Sun zabi America ne saboda it's a free country, babu wanda ya damu da wani, kuma sun san za'ayi wahalar samun su a can saboda girman ta. Plus England shine guri na farko da za'a fara zuwa neman su. Sadiq bai san ya debo da zafi ba, a saudiyya, ka shiga har gida, kuma gidan masu sarauta, ka sace musu yarinyar da za'ayi bikinta gobe, ka gudu da ita ku bar kasar gaba daya. Chafdi. Kwanan su daya a America, saboda suna gudun sabawa ubangijin su, suka nemi wani imam suka bukaci a daura musu aure, liman ya nemi waliyyanta khairat tace ita marainiya ce bata da kowa a america, daga ita sai iyayenta kuma iyayen yanzu sun mutu kuma bata taba zuwa garin suba ballantana ta san danginta, sadiq ne duk ya tsara mata wannan yace in sunxo ta fada. Imam din ne ya zauna a matsayin waliyyinta, yace duk wani problem da ya tafu da auren ta zo gurinsa, ya zama shine babanta, Sadiq kuma shi ya tsaya a waliyyin kansa, aka daura aure Sadiq ya bada sadaki, mutanen da suke masallacin sune shaidu. Daga nan sukayi signing marriage certificate sun zama islamically and legally married. Daga gurin daurin auren direct airport suka nufa suka shiga jirgi sai Nigeria. Shi sadiq a tunanin sa uban yaki yadda da auren ne saboda yana jin tsoron zuwa neman auren, dan haka yake ganin yanzu tunda yaje ya aikata abinda ya aikata ai shikenan komai ya wuce. Yana zuwa gida da khairat tun kafin yayi wa sarki Abdallah bayani sarkin ya fahimci abinda ya faru, sato khairat sadiq yayi. Sosai hankalin sarki da Yaya ya tashi dan su sunsan menene zai je yazo. Sadiq ya gaya musu cewa ya riga ya auri khairat dan haka iyayenta babu yadda zasuyi dashi, amma sarki ya san cewa auren nata da yayi shi zai kara mayar da case din worst, saboda zasuyi charging dinsa da forced marriage wanda babban laifi ne a saudiyya, sarki Abdallah ya nuna wa Sadiq cewa lallai ya dauki yarinyar mutane ya mayar da ita gidansu, jin haka Sadiq ko amsa bai bashi ba ya kamo hannun khairat suka fice daga palace din. Shi a tunaninsa yama za'a ce ya sake ta ya mayar da ita gida duk uwar wahalar da yasha kafin ya same ta? A gidan wani abokinsa anan Abuja suka kwana, da safe suka kuma hawa jirgi sula koma America. Sun yanke shawarar gwara suyi zamansu su kadai tunda iyayensu sun kasa fahimtar irin son da suke yiwa junan su. Shikenan kuma suna zuwa america aka shiga honeymoon. Rayuwarsu kawai suke