← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 190

Sashe 180

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

na tsallake tsarin addini nabi son raina, wannan shine ya jawo 'yar mu ta bijirewa umarnin mu tabi saurayi ta gudu daga kasar a wancan lokacin, tun a lokacin nasan cewa laifi nane amma pride ya hanani inyi admitting, sai muka tattara laifin duk muka dorawa shi yaron da yazo ya dauke mana yarinya, muka sha alwashin sai munga bayansa. Abin kunyar da nake gudu kar ace mun aura wa 'yar mu wanda ba balarabe ba sai ya zamanto gwara shima akan abin kunyar da muka fuskanta, cewa 'yar mu ta gudu ana gobe daurin aurenta ta shiga duniya. Wannan yasa muka kara kaimi gurin nemansu dan muga mun goge mugun suna a gurin mutane, kuma amma bamu same suba sai bayan shekara uku, sai a lokacin muka fahimci shima yaron dan babban gida ne, jinin sarauta ne, amma duk da haka maimakon mu zauna ayi maslaha sai muka dauki damarar sai mun nuna masa kuskurensa, muka je har gidan aurenta a gaban surukanta da mijinta muka dauko ta, muka raba ta da mijinta muka kuma rabata da dan jaririn danta. Amma Allah shine shaidar mu, bamu taba tsammanin raba sun da mukayi zai tabbata ba, mun raba su ne saboda mu hukuntasu a bisa abinda suka aikata, tunda har 'da ya shiga tsakanin munyi niyyar zamu hakura mu barsu. Amma sai yazo ya same mu ya bamu hakuri kuma ya nemi aurenta properly yadda kowa zai tabbatar cewa aurar da 'yar mu mukayi ba wai duniya ta shiga ba. Munce zamu hukunta shi idan yazo, amma mun san duk wanda yake da courage din shiga gidan mutane ya dauki 'yarsu ya gudu da ita to tabbas yana da courage din fuskantar hukunci a kanta. Amma kuma sai muka tarar da sabanin hakan, maimakon yazo din kamar yadda muka saka rai sai ya aiko mana da takardar sakin ta. Wannan shine abinda yafi komai kona mana rai, mu ana babban cin mutunci shine a auri 'yarka sannan kuma a sake ta. Ga kuma tashin hankalin da yarinyar ta shiga a dalilin sakin da akayi mata, da raba ta da danta da akayi. Tayi ta kokarin komawa amma muka hana ta saboda mu a gurin mu zubar da darajarta ne ace ta koma gurinsa duk kuwa da sakin ta da yayi, pride din mu ya saka muke ganin cewa shi ya kamata ya neme ta ba ita ba. Shi ya kamata yazo ya bata hakuri, ya bamu hakuri gaba daya. To Alhamdulillah yanzu gashi yazo, kuma ya bamu hakurin, kuma mun hakura, sauran magana kuma ta rage tsakanin sa da ita, in ta amince shi kenan ko a gobe sai a mayar musu da auren su". Tunda aka fara maganganun, khairat kanta yana kasa, tana wasa da 'yan yatsunta, ji take tamkar mafarki take yi amma kuma gashi kamar gaske. Bata dawo daga tunanin taba taji ana ta fita daga palon, zata tashi auntyn ta tace "ki zauna kuyi magana tukunna, zuwa gobe sai ku fadi shawarar da kuka yanke" ta koma ta zauna zuciyarta tana bugawa, tayi sauri tayi wa kanta fada "why are you behaving like a teenager? Ke da za'a haifawa jika very soon?" Nan take ta maida hankalinta guri guda ta juyo tana fuskantar Sadiq da abokin tafiyarsa, sai yanzu ta kalli abokin Sadiq din sosai, he looks familiar, and he also looks like maimumatu and Hafsat, shi ya fara gaisheta, ta sunkuyar da kanta kasa ta gaishe shi itama, ya amsa, sai kuma suka yi shiru, ya mike tsaye yace da Takawa zai jira a waje, har yakai bakin kofa tace "You are Maimumatu's Father, right?" Ya juyo yana murmushi yace mata "that's right" tayi dariya tace "Ina Fatima? Ya baku taho tare ba?" Yana murmushi yace "zata zo itama, maybe daukan amarya zata zo, tunda ni nazo daurin aure" sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta, shi kuma ya fita. Sun jima bayan ya fita babu wanda ya ce komai, sannan Takawa yace "so..., Fatima zata zo daukan amaryar a gaya mata ta shirya ko kuma ba zata zo ba a gaya mata tayi zamanta?" Ta dago suka hada ido, he looks just as she imagined he would, older, stronger and very confident, but then he is still the Sadiq she knows, the Sadiq she fall in love with, her husband, the father of her son, it feels like not a single day has passed. It feels like kamar dazu ne aka tashe su daga bacci aka ce su je ana kiransu a palon Takawa marigayi. Sati daya chif bayan nan aka mayar da auren Sadiq Abdallah da Khairat Faisal Abdallah. Daurin auren ya samu halartar kafatanin 'yan'uwa da abokan arziki daga barin khairat, a bangaren Sadiq kuwa jirgi guda aka chika da manyan mutane daga Nigeria suka je suka halarci daurin auren. Abin ya kayatar sosai. A take mujallu da jaridu na duniya suka yi ta watsa labarin auren saboda ana ganin wani karin kulla zumunci ne a tsakanin kasashen musulmai. Wannan tamkar wani ci gaba ne ga musulunci da musulmai baki daya. Ana gama daurin aure ango ya dauki amaryarsa suka tafi umra dan nuna godiyar su ga ubangiji akan dawo musu da rayuwarsu da yayi, da kuma neman taimakonsa akan dukkan abubuwan da zasu saka a gaba. Sai da sukayi sati biyu sannan suka dawo Riyadh, daga nan kuma amarya ta fara shirye shiryen biyo angonta Nigeria amma shi kam ango yace ba zai jira wannan fi'ilin sai amarya ta tare ba dan haka shi kawai sai ya tare a gidan amaryar. Ajjiyar da aka yi masa ta three full decades ya zage yake ta karba. It is like nothing has changed, jin su suke kamar sanda suna America farkon auren su. Duk abinda suke kuma hankalinsu yana kan sultan, suna keeping tabs on him. Sai da aka kammala gyaran gidan da Takawa ya saka ayi masa sannan amarya ta tare. Kamar yadda Daddy yayi alkawari, Mommy ya bawa private jet dinsa suka taho tare da Nani da wadansu zababbun mata daga fada suka dauko amarya daga Riyadh zuwa Nigeria. Wannan shi ya kara dankon zumunci tsakanin Ummee da Mommy.
Chapter 180 · 0% Book details