← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 190

Sashe 83

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda daddy ya fada haka ya aikata, washegari yaje fada akayi masa iso gaban mai martaba sarki, bai yi tsammanin zai gane shi ba amma sai yaga ya tare shi sosai da fara'a da wasa da dariya yace "Muhammad baka da kirki, ace kana garin nan da iyalinka amma ba ka zuwa mu gaisa? Kasan ni nauyi yayi min yawa bazan iya ziyarar abokanai ba" daddy yayi murmushi yace "Allah ya taimake ka ai ni ma ba zaman garin nake sosai ba, kuma in dai nazo to abubuwa sukan yi min yawa har sai na koma. Amma ayi min afuwa, in sha Allah zan ke lekowa lokaci zuwa lokaci" Har palon da yake barkar manyan bakin sa ya saka aka shiga da daddy, nan suka zauna gaba dayan su akan carpet suka fara hirar yaushe gamo da labarin karatun su da friends dinsu wadanda yanzu kowa ya kama gabansa. Daddy yayi mamaki sosai yadda yaga takawa ya zage sosai yana hira da dariya, saboda shi ya dauka maganar da zasuyi formally zasu yi ta maybe a gaban mutane ma, ashe dai Sadiq din is still the same person da ya sani kawai dai nauyi ne ya hau kansa yanzu. Anan suka zauna har aka kawo musu lunch sam daddy bai lura da yadda lokaci ya tura haka ba, he totally can't believe cewa wannan elegant mutumin shi yayi raising Sultan. Da kansa mai martaba yayi serving dinsu a plate daya suka ci, suna cikin ci Abbas ya shigo a nutse yazo ya gaishe su sosai sannan ya fada wa babansa sako cikin girmamawa ya fita. Daddy yayi noticing wani abu, Abbas totally baya kama da Sultan, ba zaka taba cewa 'yan uwa ne ba. Sai da suka gama sannan daddy ya gyara zama yace "Allah ya taimaki sarki magana ce ta kawo ni. Akan dan mu Sultan" daddy ya fada yana kallon fuskar takawa, abinda yayi tsammani kuwa shi ya tarar, just mentioning sunan sultan ya goge dukkan fara'ar dake fuskar takawa, komawa yayi kamar bai taba dariya ba. Yace "Wani abun yayi?" Daddy yace "babu abinda yayi ran sarki ya dade, ina neman alfarma ne in da hali ina so ya koma gida na da zama" Takawa yace "saboda me?" Daddy yace "ba wani abu kawai mun hadu da shine sai naga kusan sa'an yaron wajena ne walid shine sai naga ina sha'awar in hada su a gurina for sometimes, in ka amince of cause" Takawa yayi shiru yana shan lemon hannunsa, har daddy ya fitar da ran cewa ba zai yi magana ba sai kuma yace "you can do with him as you wish. Kawai dai ka tabbatar duk abinda ya aikata maka kai ka jawo mu babu hannun mu a ciki, kuma ka tabbatar duk abinda yayi kar ka danganta shi da mu" daga haka ya ajiye cup din hannunsa ya mike tsaye yace "in ka kammala da akwai servants a waje zasu raka ka motar ka. Na gode da ziyara Allah ya bar zumunci"
I
Da yamma Sultan yaji wayar Walid da sakon sarki ya masa maganar daddy, Sultan sam ya kasa tantance me yakeji a ransa, few things dinsa ya dauka ban da kayan sawa tunda daddy yace baya son irin su. To shi yanzu ina zai iya saka wata shadda ko yadi ne kam. Bashi ma da tailor. Yana zuwa gidan ya tarar da walid da Habeeb suna jiransa a compound, direct part dinsu suka wuce dashi fuskokinsu babu yabo babu fallasa dan sukam sam basa murna da wannan hukuncin na daddy. Four bedrooms ne dama a part din, sai palo mai hade da dining duk da dai ba mafani suke da dining din ba sai dai in bakon da ba za'a shiga dashi main palo ba. Walid ya bawa sultan key din daki daya da kuma spare key din palon. Sultan ya bude dakin ya shiga, ba laifi yana da girma, da gado da dan karamin closet sannan sai toilet. Yana gama duba dakin ya fita yana tambayar ina masu share share aka nuna masa su yace "dan Allah aron kayan cleaning nake so" da mamaki suke kallonsa, suka ce "ai mu zamu gyara maka" ya girgiza kai yace "thank you, zanyi, ba wani abu" Sultan sam bai yarda wani ya gyara masa dakin saba saboda gani yake ba za'a taba yi masa dai dai ba, tunda ya fara aiki bai gama ba har magrib, sannan ya shiga toilet yayi wanka ya chanza kaya ya fito da sauri, yana fitowa yaji dad yana cewa a kirashi su tafi masallaci, tare suka yi sallah suka dawo gida, suna zuwa suka zarce main palo, shi dai Sultan duk wani iri yake jin sa, yana zuwa masallaci wani lokacin amma bai taba zuwa tare da mahaifinsa ba ballantana ace wai harda siblings. A palon suka tarar an jera abinci a dining amma sam babu mommy, basu yi magana ba saboda kwana biyun nan haka take yi, kuma daddy ma baya son su hadu da Sultan har sai yayi mata magana da kansa. Suka zazzauna a dining din suna kallon kallo, can daddy yace "Sultan ai sai kayi representing Moon, kayi serving din mu" nan da nan sultan ya washe baki har kunne, ance yayi representing Moon, ya mike har da nade hannayen riga ya fara lafta musu abinci, walid yayi dariya yace "wannan uban abincin duk kana tunanin zamu cinye?" Sultan yace "why not?" Sai da kowa ya rage nasa abincin amma sultan ya chinye nasa tas. Daddy ne ya fara tashi ya koma palo, sultan ne na karshen gamawa, nan ya fara kokarin kwashe kaya, Habeeb yace masa "ka bar shi fa, za'a kwashe ai" shi Sultan ya saba da yiwa kansa komai, tunda aka kaishi america shi yake yiwa kansa komai, daya dawo Nigeria ma haka. Ya karaso palon, har zai zauna sai kuma yaji ajikinsa kamar zai shiga hurumin da ba nasa ba, sai ya mike zai fita, yana jin ba dadi a ransa, daddy ya kira shi ya dawo ya zauna yace "ina maganar kayan sawa da muka yi da kai?" Sultan ya dan bata rai yace "daddy ni ban taba dinki ba, ban masan inda ake saida yadikan ba ballantana wani tailor, amma in na samu zanyi" daddy ya kalli walid yace "gobe ka kai shi gurin tailor din mu ya auna shi, sai kuma ku shiga kasuwa kuyi siyayya" sai kuma ya juya gurin sultan yace "zaka iya ci gaba da saka kananan kayan ka a gida, amma duk sanda zamu fita ina so in ganka da manyan kaya da hula" sultan ya shafa kansa, lallai akwai rigima kenan, shi kam rabon da ya saka traditional hula tun kakansa yana da rai. Daddy ya juya kan su walid yace "ga Sultan nan, ina so ku rike shi tamkar shima dana ne da baya gurin mu amma yanzu yazo, kar inji kar in gani a tsakanin ku" duk suka amsa. Daddy ya sake cewa da Sultan "yi min bayani akan yadda kake gudanar da aikin ka" nan sultan yayi masa bayanin yadda yake yi, daddy yace "abinda za ayi yanzu shine, head office zaka bude, ka dauki ma'aikata sosai, ka saka wa gurin suna yadda zaka ke samun contract sosai. Na duba ayyukan ka naga suna da kyau sosai dan haka nima zan kara yi maka advertising dan kake samun contract a projects din government. Ina ganin hakan shi zai kara rage kama yawo, in ka samu abinyi zaka fi zama a guri daya" sosai sultan yaji dadi, babu wanda ya taba bashi shawara akan me zaiyi da rayuwarsa ko aikinsa. Ji yake yi wata soyayyar daddy tana shigarsa. Daga nan suka fara hirar su abin sha'awa, a tsokani wannan2, har mamaki sultan yake dama haka family yake? Dama haka uba yake a cikin 'ya'yansa?

Bayan sun tashi daga hirar sunyi sallah isha daddy ya hau saman su, dakin mommy ya shiga ya tura kofa, tana zaune tana aiki a computer, taji shigowarsa sarai amma bata dago ta kalleshi ba, a ransa yace 'wai ita menene problem dinta ne?' A bakin kofar ya tsaya yace "Fatima, ina so in sanar miki cewa Sultan ya dawo gidan nan da zama" zumbur ta mike har tana ball da system din gabanta ta karaso kua dashi da sauri tace "Sultan fa kace?" Sai kuma hawaye "haba dear, ya zaka dauko yaro kamarsa ka hada shi da yaran mu, so kake suma ya bata mana su kamar yadda ya so ya bata Moon? Dan Allah kayi hakuri idan purnishing dina kake dan na daukr Moon, wallahi zan dawo da ita, please ka kore shi daga gidan nan" daddy ya girgiza kansa yace "bazan taba korarsa ba sai dai in shine da kansa yace zai tafi, wanda bana jin zai ce haka, kuma badan kinyi min laifi bane yasa na kawo shi nan ba, a'a nayi haka ne dan naga wani chance ne na samun lada Allah ya dora akan cinyata, shi da na kowa ne, baka san wane ne zai ji kanka ba wata rana, kuma ita rayuwa duk abinda ka shuka shine zaka girba, ina so in shuka alkhairi yadda ko bayan raina zuri'ata zasu girbi alkhairi na. Ban gaya miki ba har sai da ya dawo saboda ina son kini zafin da naji nima sanda baki gayamin kin dauke moon ba har sai da kika aikata din. Yanzu bazan matsa miki cewa ki dawo da ita ba har sai na tabbatar da changes din da nake so in gani agurin sultan tukunna" daga haka ya juya yayi tafiyarsa. Mommy ji tayi gaba daya duniya tayi mata zafi, lallai daddy is even softer and weaker than she thought. Amma babu komai, ta tabbatar cewa Sultan will teach him a lesson. Ita kuma ba zata dawo da Moon ba har sai daddy ya yi learning lesson a gurin sultan tukunna.
Chapter 83 · 0% Book details