← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 190

Sashe 150

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ya koma kiyayya. Zai zamanto kamar mun raba da da ubansa ne Allah ya taimake ka, ina tausayin yaron tunda kaga yanzu babu uwa kuma azo ace uba yana tsanarsa ai abin zaiyi masa yawa, tarbiyyar sa nake tunani" Sarki Abdallah ya daga kansa sama yana tunani. Tabbas in aka raba Sadiq da Khairat an shiga rayuwar Sultan. Amma kuma in ba'a raba su bafa? Ya lissafa abubuwan da suke at stake, na farko rayuwar Sadiq din gabadayanta, Sadiq shine sarki yake sa ran zai gaje shi, shine yake sa ran ko bayan ransa zai rike gidan, zai rike sarautar kuma zai rike al'ummar da suke karkashi sa baki daya, ba rayuwar Sadiq ce at stake ba, family name dinsu da family future dinsu gabadaya is at stake, ba family dinsu kadai ba, hatta martabar musulmin Nigeria gabadaya is at stake, ba musulmin Nigeria kadai ba, ita kanta Nigeria martabar ta sai ta ragu a idanun sauran kasashe. Dan in dai suka ka.a Sadiq sai sunyi publishing a international papers cewa ga abinda Nigerian Prince yayi. Sarki ya sauke ajjiyar zuciya ya sunkuyo da kansa yana kallon malamin yace "a yi. Ni kuma nayi alkawarin zan zamarwa Sultan uwa kuma zan zamar masa uba. Zan bashi duk kannin wani gata da ya kamata iyaye su bashi. Insha Allah sultan ba zai yi maraici ba. Ina rokon Allah kuma ya dubi uzurina, ya dubi dalilin da yasa nayi haka, ya yafe min". Kaico, mai martaba sarki babu wanda yasan gawar fari sai Allah.
Chapter 150 · 0% Book details