← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 190

Sashe 177

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Ninety Five : The Light Muka kalli juna ni da Sultan sannan muka kalleta, she was blushing, Sultan ya mike tsaye bacin rai a rubuce a fuskarsa yace "wait, what? Aure? Who did you marry? Kawai dan ki zo Nigeria sai kiyi aure?" Duk kallonsa muke yi daga ni har Ummee, ya fara zagaye palon yana magana "koma waye i will have nothing to do with him. Tunda kin aure shi ya kawo ki Nigeria shikenan mission accomplished, ya sake ki kawai ki dawo gidana ki zauna, in ma ba kya son zama a gidana sai in sai miki wani gidan ki zauna, but I don't want to see any man near you" ni kam dariya kamar zata kwace min ganin yadda ya hakikance yake fada, lallai kishi kumallon maza, lol, tabbas da ace Ummee tayi aure da anyi drama da sultan. Ummee tace "sultan you shouldn't judge people before you get to know them, give him a chance, yana da kirki sosai, you will like him" da sauri yace "I won't. Kuma ma nasan tunda da gaggawa akayi auren yanzu haka baki gama sanin halinsa ba, he may even be a 419 guy for all we know, ko kuma ma arm robber, Nigerians are not like Arabs, ba'a saurin trusting mutane anan Ummee" she was calm duk wannan fadan da yake yi, tace "Sultan I know him tun kafin musan zamu haife ka, zan iya cewa I knew him more than anyone a wancan lokacin, kuma har yanzu ma he hasn't change a bit" ya tsaya da zagayen da yake yana kallonta, sai a lokacin dariya ta kwace min, ya juyo yana kallona fuska a daure yace "menene abin dariya kuma?" Na tsaya da dariyar da nake nace "sultan, Ummee is trying to tell you cewa sun mayar da auren su ita da Takawa" ya dan jima yana kallona inayi masa murmushi, sai kuma ya juya ya kalli Ummee, ta gyada masa kai, a hankali kuma kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki sai ya dawo ya zauna a kusa da ita, ta saka hannu tana shafa gashin kansa, tace "you look so much kike your father when you are angry" yace "amma Ummee me ya faru? Ji nake fada kuke yi da Takawa" ta danyi dariya tace "dama can kullum fada muke yi dashi, he is so stubborn and hot headed like you" ya kwantar da kansa a kafadar ta yace "I love you, Ummee" na mike a hankali na koma cikin gida, ina jin dadin auren Takawa da Ummee a raina amma deeply kuma ina alhinin rashin Baffa. Washe gari da wuri Takawa yazo, da jiniya da hakimai da dogarai da komai yazo, Allah bai yi zasu gaisa da baffa ba. Kofar gidan baffa kuwa ya cika taf da mutane sunxo ganin sarkin abuja. Ya jima a gurin su Daddy sannan ya aiko aka kira ni, muka tafi tare da mata da yawa muka gaishe shi yayi mana gaisuwa sannan muka dawo cikin gida. Bayan azahar aka aiko su Ummee su fito zasu tafi, Ummee dama ta shirya amma muka nemi Huda muka rasa, gashi kuma ta bar handbag dinta da wayarta a ciki ballantana a kira ta, ni da Amina muka fita daki by daki muna nemanta amma shiru, gashi ana ta jiransu a waje, na zagaya bayan dakin hajja inda take 'yan shuke shuken ta kawai sai na hango hijab din huda a bayan katanga, na kara sauri sai na hango tare suke da wani namiji, gaba na ya fadi, na shiga ni maimunatu, kar dai munir ne ya ja 'yar mutane bayan gida zai lalata musu yarinya inzo inji kunya, ga mamaki na ina zuwa sai na ga Faruk, na tsaya ina kallonsu duk basu san ma nazo gurin ba, faruk ya karkace a jikin jini yana ta zuba mata tsari ita kuma ta sunkuyar da kai kasa tana ta murmushi, nayi gyaran murya, suka juyo a tare suna kallona, da sauri ta ja hijab dinta ta rufe fuskarta shi kuma ya juya baya yana shafa keya, nace "ki zo ana jiranki zaku tafi" sumi sumi tazo ta wuce ni, bance masa komai ba na juya zan tafi, ya biyo ni da sauri, "ammm...... dama wai bata san kayan lambu ba shine nake nuna mata" ba tare dana kalleshi ba nace "to" a raina nace 'maida karuwa 'yar iska' wai dan karamin faruk din nan nr har ya girma shima zai fara tsara 'yammata, sai kuma na tuno cewa yanzu fa service yake yi, dan haka ya girma kenan. Duniya kenan. Muka fita rakasu sultan yana ta bacin ran Takawa yace tare zasu koma, ni kuma sai anyi sadakar bakwai sai mu taho tare da su Mommy. Na san dan dai babu yadda zaiyi ne, gashi ko wata sallamar kirki bamu yi ba. Motar Takawa suka shiga, shi yana gaba kusa da driver, Takawa da Ummee suna baya a tare. Sai kawai na samu kaina da murmushin jin dadi. Suka shiga motocinsu suka tafi mu kuma muka koma gida. Ranar da Baffa yayi kwana biyar da rasuwa Amira tazo yi mana gaisuwa, ita da Mama da wata aunt din ta. Sun jima sosai sannan sukayi shirin tafiya, mun taho rakasu ni da Hafsat da Amina muna dan tafiya a hankali muka bar su mama suka yi gaba, ina ta studying Amira, she looks happy. Nace "how are you?" Tace "actually am great. Yanzu na fahimci family is everything, babu abinda yafi dadi irin ka ganka a cikin 'yan'uwanka, yanzu a kano duk inda na kalla hagu da dama duk 'yan'uwana ne, kuma rashin zama a cikin su tun farko shi ya saka nake ganin kamar basa sona ashe abin ba haka yake ba" nace "ya angon naki kuma yazo?" Nan take naga wani murmushi ya shi kadai ya isa amsar sauran tambayoyin nawa, tace "yazo, bai jima ba ya koma, da yake karatunsa yazo karshe ne abubuwa sundan shige masa gaba" nace "and" tace "he is OK. A bit different though, mamansa shuwa ce, kuma kamar duk ita yayo, so technically za'a iya ce masa shuwa. He is really nice, a doctor, kuma naji dadin yadda ya karbe ni" na tsaya ina kallonta wani tunani yana zuwa min raina, nace "wait, ya sunan sa?" Tana kallona da mamaki tace "Mahdi" sai kuma ta rufe baki tace "oh my God, kin san shi ashe, Oxford yake yi kuma medicine" nace excitedly "Mahdi was my best friend a Oxford. Congratulations Amira. Mahdi is the best husband that you can ever wish for" nan muka rabu da alkawarin next time idan muka hadu zan bata labarin rayuwar makarantar mu da mahdi. Bayan sun tafi na zauna ina tunanin hukuncin ubangiji. Tayi ba dai dai ba a rayuwa amma kuma tayi nadama, mun yafe mata mu da ta bata wa, Allah ma sai ya yafe mata, sannan kuma tazo ta farantawa mahaifiyarta rai ta hanyar bata zabin mijin da zata aura, sai ubangiji yayi mata zabin alkairi ya bata Mahdi, wanda ni a ganina yafi Amir din da da na dauka zasuyi aure, ya kuma fi Abbas din da naso hada ta dashi. Allah kenan. Ranar sadakar bakwai Ibrahim yazo yi mana gaisuwa, dama Amina tace min yazo dashi akayi jana'iza. Muka fita gaba daya dasu Hafsat yayi mana gaisuwa, sam babu wani special treatment daya bani, idonsa suna kan Aminan sa. A ranar muka taho gaba daya har Daddy, Amina kadai muka bari acan saboda 'yan shirye shirye da zata yi saboda bikin su yanzu saura sati uku. Su inna sun so a daga bukukuwan amma mazan gidan suka ce babu wani abu, sai dai an yanke shawarar Abuja za'a tafi ayi bikin gaba daya a can. Muna zuwa Abuja gida muka wuce, Sultan yayi ta nacin in taho gida amma naki, saboda ba karamin gajiya nayi ba kuma nasan ina komawa gida sai ya karamin wata gajiyar. Da kyar na samu na lallabashi ya hakura ya barni na kwana a gida. Tunda muka sauka a gida daga ni har Hafsat muka baje cikkuna a gado muka yi ta bacci. Washegari bayan sultan ya taso daga office ya biyo muka tafi. Naga duk ya chanja a kwana biyar din da ban ganshi ba, he looks so calm and happy, loneliness din da nake gani kullum a idonsa is now totally gone, a raina nace lallai duk duniya babu abinda yafi iyaye dadi, komai girman mutum, komai arzikinsa, komai yawan matansa da 'ya'yansa, soyayyar iyaye daban ce, ballantana ga sultan wanda da bai san taba, dan haka yanzu kara'i ake masa. Ina shiga motar ya matso ya jawo fuskata ya fara kissing dina, na barshi yayi dan kansa ya hakura, yace "damn it baby girl, I missed you" nace "ina kayi missing dina bayan nasan kana can Ummee tana goya ka da zani" yayi dariya yace "da ace zan tsaya da sai ta goya nin ai" na taya shi dariyar nace "how is she?" Yace "tana can tana shan amarci" na dungure masa kai nace "Ummeen kake gaya wa tana amarci ko?" Yace "in munje zaki gane wa idonki ai". Muna shiga naga gidan gaba ki daya ya chanza min, gaba daya an chanza masa traditional setting din sa an mayar da shi modern. Part din Takawa in ka shiga ba zaka dauka a Nigeria kake ba saboda haduwarsa, anan kuma ummee take, basu wani raba dakuna ba. Komai wayewar ka in ka shiga gurin sai kayi kallo. Da sauri Ummee tazo ta rungume ni tana min sannu da zuwa, ta sunkuya kusa da cikina tace " Hello dear, welcome back home" daki daki sai da ta shiga dani ta nuna min, master bedroom ne naki shiga, ina suruka ina ganin makwancin surukai?, lol. Part din Hajiya yana nan yadda yake, tana nan kuma har yanzu a ciki, amma kuma a kusa da gurin anyi wa su saratu sababbin dakuna suma, an kawata musu gurin gwanin ban sha'awa. Sultan yana ta tabani wai in tashi mu tafi amma Ummee tana ta zuba min hira, tana tsara min yadda aka tsara bikin Amir wanda za'ayi next week. Ban tambayeta labarin yadda aka mayar da auren su da Takawa ba ita ma kuma bata gayamin ba. Muna ta
Chapter 177 · 0% Book details