Sashe 183
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
gama ai. Babu dadi idan aka ce banzo ba, Amina babu abinda bata yi min a bikina ba. Ga su ya Walid suma ba zasu ji dadi ba" ya bata rai yace "da baki zo ba duk zasu fahimta, ai sunsan condition dinki" bance komai ba na rufe idona, dan maganar ma karamin ciwon kan take yi. Mommy tayi knocking ya tashi ya bude mata, ta shigo tana kallonsa tace "zaku tafi ne ko anan zaku zauna?" Yace "gwara mu tafi can din dai tunda yafi shiru zata fi hutawa sosai" tace "hakane, dan ana dawowa daga gurin dinner wanda bashi da high bp ma sai nashi ya tashi" ta jiyo tana kallona na dan yi mata murmushi nace "bye Mommy" tace "bye-bye, sai munyi waya" sai da muka ji tashin motar ta sannan sultan ya kama ni na mike tsaye muka fita, a hankali muke tafiya saboda jiri da nake ji, daga karshe ma dai dauka na yayi ya sakani a mota, ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana kallona, na kirkiri murmushi nayi masa shima ya mayar min, amma nasan nashi murmushin bai kai zuci ba. Ya kama hannuna daya ya rike a hannunsa daya, yayi intertwining fingers din mu ya dora akan gear sannan ya tura hannayen mu a tare muka saka gear muka fara tafiya a hankali, hankalinsa rabi akan titi rabi akaina, hannunsa daya akan stirring wheel daya a cikin nawa. Na kwantar da kaina a jikin kujera ina jin dadin kamshi da sanyin motar, amma maimakon inji bp dina yana sauka sai naji yana kara hawa, na kalli sultan na tina da ranar dana fara ganinsa, a hankali naga ya fara zama dishi dishi, this is my worst fear tun sanda na samu ciki, preeclampsia, a raina nace 'ko yanzu na tafi, at least nayi wani abu a rayuwata".